Gwamna Radda Ya Yi Karatun Ta Natsu, Ya Fadi Abin da Zai Hana Magance 'Yan Bindiga
- Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya taɓo batun matsalar rashin tsaro da ake fama da ita na tsawon lokaci
- Dikko Radda ya bayyana cewa mafi yawan mutanen da ke haddasa rashin tsaro, suna rayuwa ne a cikin al'umma
- Gwamnan ya bayyana cewa dole sai an magance masu ba ƴan bindiga bayanai kafin a shawo kan matsalar rashin tsaro
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya bayyana cewa kaso 70 zuwa 80 cikin 100 na waɗanda ke haddasa rashin tsaro a jihar ba zaune suke a cikin daji ba.
Gwamna Radda ya nuna cewa suna cikin al'umma suna aiki a matsayin masu bayar da bayanai ga ƴan bindiga.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce Gwamna Radda ya bayyana hakan ne yayin da yake magana ranar Alhamis a wajen taron addu’a ta musamman domin cika shekaru biyu a kan mulki.
Dikko Radda ya taɓo batun rashin tsaro
Gwamna Radda ya jaddada muhimmancin ɗaukar matakai na gaggawa, yana mai cewa ba za a iya samun nasara a yaƙi da ƴan bindiga ba sai an magance barazanar masu ba su bayanai, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
"Ba mu zo nan domin murnar mulki ba, sai domin mu godewa Allah da kuma tunatar da kanmu cewa shugabanci amana ce, ba kyauta ba ce."
"Kuɗin da muke sarrafawa ba namu ba ne, na jama’a ne. Mu dai masu kula da su ne kawai."
- Gwamna Dikko Umaru Radda
'Masu haddasa rashin tsaro na cikin al'umma' - Radda
Gwamna Radda ya bayyana cewa masu haddasa rashin tsaro ba daga cikin daji kawai suke ba, inda ya ce waɗanda ke cikin daji kaɗan ne idan aka kwatanta da masu aikata laifi da ke cikin al’umma.

Source: Facebook
"Ba batun daji kaɗai ba ne yanzu. Ba za mu ci gaba da yin shiru ba, matsalar rashin tsaro tana cikin al’ummominmu yanzu. A nan ne muryoyinku ke da matuƙar muhimmanci.”

Kara karanta wannan
Musulmi sun yi babban rashi, Sarki mai martaba a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya
“Har yanzu ina kira ga malamai da kowa da kowa game da matsalar rashin tsaro da ta addabi jiharmu. Mun yi taron tsaro jiya kuma a cikin bincikenmu, mun gano cewa kashi 20 zuwa 30 ne kawai daga cikin masu laifin ke cikin daji, yayin da kashi 70 zuwa 80 ke cikin al’umma.”
“Waɗanda ke cikin daji su ne ke karɓar bayanai daga cikin garuruwa. Su ne ke saya musu miyagun ƙwayoyi, mai domin tafiya kai hare-hare, su ke kai musu magunguna, har ma da kuɗin fansa a daji."
"Dole na ce idan ba mu magance waɗannan masu bayar da bayanai da ke cikinmu ba, ba za mu yi nasara ba a wannan yaƙi da rashin tsaro. Dole mu ɗauki alhakin bayyana su."
Gwamna Dikko Umaru Radda
Masu ba da bayanai bala'i ne
Kabir Usman ya shaidawa Legir Hausa cewa tabbas masu ba ƴan bindiga bayanai babbar masufa ce a cikin al'umma.
"Matsalar rashin tsaro tana ƙara ruruwa ne saboda ayyukan waɗannan ɓata garin. Su ne suke kitsa duk wata tsiya da ake ƙullawa."
"Ƴan bindigan da ke daji ba su san wanene mai kuɗi ko talaka ba, su ne suke gaya musu inda ya kamata su kai hari don su yi ɓarna."
"Kuma sun yi yawa a cikin mutane saboda ɗan abin da suke samu daga wajen ƴan bindigan."
- Kabir Usman
Gwamna Radda ya sha alwashi kan rashin tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya ƙudiri aniyar magance matsalar rashin tsaro.
Dikko Radda ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta ɗauki matakan da suka dace domin kawo ƙarshen ƴan bindiga.
Gwamna Radda ya sha alwashin ne yayin da ya je ziyarar jaje kan wani hari da ƴan bindiga suka kai a ƙaramar hukumar Dutsinma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

