An Kama Boka Yana Kokarin Arcewa daga Najeriya bayan Samun Kabari a Gidansa
- Hukumar Shige da Fice ta Najeriya ta kama wani boka da ake nema ruwa a jallo bisa zargin garkuwa da mutane da kisan gilla
- Mutumin, wanda aka bayyana sunansa da Obi Levi Obieze, ana zargin sa da hannu wajen sace wata yarinya mai shekaru 13 a jihar Enugu
- Rahotanni sun nuna cewa an kama shi ne a kan babur yana kokarin tserewa daga Najeriya ta hanyar iyakar Badagry-Seme a jihar Legas
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Lagos - Hukumar Shige da Fice ta Najeriya ta sanar da kama wani fitaccen mai sihiri da ake nema bisa zargin aikata laifin garkuwa da mutane da kisan gilla.
An kama mutumin ne a wani shingen binciken abubuwan hawa da ke hanyar Badagry-Seme, jihar Legas.

Kara karanta wannan
Ambaliya: Ana tsoron rayuka sama da 50 sun salwanta bayan gano gawarwaki 15 a Neja

Source: Twitter
Hukumar shige da ficen Najeriya ta wallafa a X cewa ta yi nasarar kama Obi Levi Obieze ne a kan babur.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Obi Levi Obieze da aka fi sani da Levi Obu Onyeka, yana daga cikin wadanda rundunar ‘yan sanda ke nema tun bayan sace wata yarinya a Umuojor, jihar Enugu, a ranar 27 ga Mayu, 2025.
Rahoton hukumar ya bayyana cewa kama wanda ake zargin ya biyo bayan bayanan sirri da suka fito daga rundunar ‘yan sanda, tare da hadin gwiwar jami’an tsaron iyaka na jihar Legas.
An kama boka yana kokarin arcewa
Jami’an tsaron iyaka sun cafke wanda ake zargi ne a kan babur yana kokarin tsallakawa iyaka zuwa wata kasar makwabta, kamar yadda rahoton hukumar NIS ya bayyana.
A lokacin da aka cafke shi, an same shi da takardar rajistar shaidar zama dan kasa (NIMC), wanda hakan ya tabbatar da shaidarsa.
A yayin tambayoyi na farko, wanda ake zargin ya amsa cewa shi ne wanda ake nema kuma ya yarda da laifin.
Boka ya ce yana da hannu a sace yarinya
A cewar hukumar, an sace yarinyar ce lokacin da take hanyarta zuwa gona tare da mahaifinta, inda daga bisani aka kai ta wani wurin bori da ake zargin wanda aka kama yana amfani da shi.
Rahoton jaridar Punch ya bayyana cewa an kubutar da yarinyar ne a wani samame da ‘yan sanda suka kai, inda suka gano wasu gawa biyu a cikin rami da aka rufe da siminti.
Za a mika boka ga ‘yan sanda don bincike
Hukumar Shige da Fice ta ce tana aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda domin mika wanda ake zargi ga hukuma domin ci gaba da bincike.
Hukumar ta tabbatar da aniyar ta na kare iyakokin kasar daga masu aikata laifuffuka da ke kokarin tserewa bayan aikata laifi a cikin kasa.
Matashi ya nemi a kashe shi bayan kisan kai
A wani rahoton, kun ji cewa an kama wani matashi da ya amsa cewa yana da hannu a kashe wata matar aurea jihar Kano.
Matashin ya tabbatar wa 'yan sanda cewa shi kadai ya kashe matar auren yayin da ya shiga gidanta da dare.
Ya bayyana cewa babu abin da ya fi bukata kamar a yanke masa hukuncin kisa domin laifin da ya aikata ya dame shi matuka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

