WAEC: Ɗakin Zana Jarabawa Ya Rufta kan Ɗaruruwan Ɗalibai, Jama'a Sun kai Ɗauki

WAEC: Ɗakin Zana Jarabawa Ya Rufta kan Ɗaruruwan Ɗalibai, Jama'a Sun kai Ɗauki

  • Ɗaruruwan ɗalibai sun sha da kyar yayin da ɗakin jarabawa ya rufta kansu a makarantar sakandiren gwamnati da ke garin Namne a jihar Taraba
  • Mazauna yankin ne suka yi kokarin ceto ɗalibai da malaman da ke kula da su yayin rubuta jarabawar ranar Laraba da ta gabata
  • Ɗakin rubuta jarabawar ya rufta ne sakamakon ruwan sama mai karfi da guguwa da aka yi a wannan rana, babu wanda ya rasa ransa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Taraba - Babban ɗakin zana jarabawa a makarantar sakandiren gwamnati da ke garin Namne a karamar hukumar Gassol ta jihar Taraba sun rufta kan ɗalibai.

Rahoto ya nuna cewa ɗaruruwan yara ne suka sha da kyar yayin da ajin da ɗalibai suke rubuta jarabawar kammala sakandire (SSCE) watau WAEC ya rufta kansu a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Mutane 2 sun rasu da suka ɗauko ragunan layya da Babbar Sallah a Najeriya

Taraba.
Dakin zana jarabawa ya rufta wa dalibai a jihar Taraba Hoto: Legit.ng
Source: Original

Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne daidai lokacin da ruwan sama mai karfi da iska ya ɓarke a garin, wanda ya haifar da ruftawar azuzuwan makarantar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda jama'a suka kai wa ɗalibai ɗauki

Dalibai da masu kula da su sun makale a cikin azuzuwan da suka rufta na tsawon sa'o'i kafin daga bisani wasu mazauna yankin su kai masi ɗauki, su ceto su.

Wani mazaunin yankin, Alhaji Dan-Azumi Lauris, ya shaida wa jaridar Vanguard cewa wannan ne karo na biyu da daliban ke fuskantar irin wannan hadari.

Mutumin ya bayyana cewa rukunin farko da suka gama jarabawarsu sun riga sun bar makarantar kafin ibtila'in ruftawar azuzuwan ya faru ranar Laraba

Ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:00 na yamma a ranar Laraba da ta gabata, 28 ga watan Mayu, 2025.

Ɗalibai da ƴan NYSC na kwance a asibiti

Dan-Azumi ya bayyana cewa daliban da suka jikkata tare da malamai da ‘yan bautar kasa (NYSC) an garzaya da su zuwa cibiyar kula da lafiya a matakin farko (PHC) da ke dab da makarantar don kula da lafiyarsu

Kara karanta wannan

Jiran shekara 3: Za a fara hukunta daliban Najeriya da aka kama da satar amsa

Ya kara da cewa ba makarantar kadai abin ya shafa ba, domin guguwar ta lalata gidaje da dama a garin yayin ruwan saman da aka yi.

Makaranta.
Dalibai sun sha da kyar ama tsaka da rubuta jarabawar WAEC a Taraba Hoto: Waqqas Ahmad
Source: Facebook

Ɗalibai sun kusa kwana a makaranta a Jalingo

A garin Jalingo kuwa, dalibai da dama ba su samu damar komawa gida ba sai bayan karfe 1:00 na dare, sakamakon ruwan sama mai tsanani da ya fara sauka yayin da suke tsaka da rubuta jarabawa.

Rahotanni sun nuna cewa ruwan saman ya dauke ne bayan lokaci mai tsawo yana sauka, wanda ya hana su komawa gida a kan lokaci.

Gwamnan Taraba zai gyara makarantun gwamnati

A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Agbu Kefas ya jaddada kudirinsa na inganta makarantun gwamnati domin samar da ilimi mai inganci a Taraba.

Gwamnan Kefas ya bayyana hakan ne a wurin bikin yaye dalibai da ya halarta a Kwalejin Ilimi ta Zing wanda aka gudanar a ranar Asabar.

Ya ce ilimi shi ne tushen ci gaban kowace al'umma, wanda ya sa gwamnatinsa ta ayyana ilimi kyauta da tilasta shi a matakin firamare da sakandare a fadin jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262