Malamin Addini Ya Fito Karara Ya Gayawa Tinubu abin da Zai Hana Shi Tazarce a 2027

Malamin Addini Ya Fito Karara Ya Gayawa Tinubu abin da Zai Hana Shi Tazarce a 2027

  • Babban malamin addinin Kirista, Cardinal John Onaiyekan ya nuna rashin gamsuwarsa da inda akalar gwamnatin Bola Tinubu ta nufa
  • Malamin ya koka kan yadda rayuwar ƴan Najeriya ta taɓarɓare a cikin shekaru biyu da Tinubu ya kwashe yana mulki
  • Ya bayyana cewa idan aka ci gaba da tafiya a haka, shugaban kasa Tinubu ba zai iya lashe sahihin zaɓe ba a 2027

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Babban malamin addinin Kirista, Emeritus Archbishop na Abuja, Cardinal John Onaiyekan, ya yi magana kan kamun ludayin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Malamin addinin ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ba zai iya yin nasara ba idan aka yi zaɓe na gaskiya da adalci, saboda irin wahalar da jama’a ke ciki a halin yanzu.

Cardinal John Onaiyekan, Bola Tinubu
Onaiyekan ya ce Tinubu ba zai iya lashe zabe ba a 2027 Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce ya bayyana haka ne a ranar Laraba a birnin Abuja, yayin wani taron cocin Katolika na shekarar 2025, da kuma bayar da lambar yabo ta mutunta marigayi ɗan jarida, High Chief Raymond Dokpesi.

Kara karanta wannan

"Kuɗin kamfe," Ɗan Atiku ya tayar da ƙura, ya jero abubuwa 3 da Tinubu zai yi da bashin N40trn

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

John Onaiyekan ya ƙalubalanci Bola Tinubu

John Onaiyekan ya ƙalubalanci gwamnatin Tinubu da ta gaggauta ɗaukaka rayuwar ƴan Najeriya, ta hanyar inganta ta.

Ya buƙaci Tinubu ya fuskanci haƙiƙanin wahalhalun da mutane ke fuskanta, maimakon dogaro da yabo daga hadimansa, idan ba haka ba zai fuskanci rashin nasara a zaɓen 2027.

Ya jaddada buƙatar shugaban ƙasa ya nemo hanyoyi da dabarun rage wahalar da jama'a ke ciki, yana mai gargaɗin cewa kada ya dogara ga hadiman da ke yawan yabonsa kawai, rahoton TheCable ya tabbatar.

"Ba ina cewa ya je ya zauna a Mpape, Abuja na kwana biyu bane, duk da cewa hakan ba zai zama laifi ba, amma ya kamata ya san yadda mutane a Mpape ke rayuwa. Ya kuma san yadda iyalai ke rayuwa da albashin N30,000 a wata."
"Ba mu yi rashin adalci ga gwamnati ba idan muka ce cikin shekaru biyu da suka wuce, rayuwar talakawa ta taɓarɓare ƙwarai. Aikin gwamnati ne ta tabbatar da cewa aƙalla, rayuwar mutane ba ta tabarbarewa, ko ta inganta idan zai yiwu."

Kara karanta wannan

Tinubu ya ƙara ƙarfi, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya haƙura da neman mulki a 2027

“Idan ya ci gaba da irin wannan salon har zuwa ƙarshen mulkinsa, idan aka gudanar da zaɓe na gaskiya da adalci, ba zai ci ba. Domin yaya za a ce mutane za su sake zaɓensa alhali ba su jin daɗi?"

- Cardinal John Onaiyekan

Onaiyekan ya ba Tinubu shawara

Malamin addinin ya kuma amince da hukuncin Kotun Koli da ya tabbatar da nasarar Tinubu a zaɓen 2023.

Cardinal John Onaiyekan
Onaiyekan ya bukaci Tinubu ya kyautata rayuwar 'yan Najeriya Hoto: Cardinal John Onaiyekan
Source: Facebook

Ya nuna cewa batun zaɓe ya riga da ya wuce, yanzu lokaci ne da ya kamata a tsaya a yi wa jama'a aiki.

"Zaɓe ya wuce tun shekaru biyu da suka wuce. Yanzu ya kamata ya yi mulki yadda ya kamata, ya sa rayuwar ƴan Najeriya ta inganta, ya magance matsalolin tsaro a ko'ina, ya farfaɗo da tattalin arziki, kuma ya yaƙi cin hanci da rashawa."
"Waɗannan ne abubuwan da wanda ya gabace shi, Buhari, ya ce zai yi, amma bai yi ba har bayan shekaru takwas. Yanzu muna sa ran wannan zai yi wani abu.”

- Cardinal John Onaiyekan

Buhari ya taya Shugaba Tinubu murna

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya aika saƙo ga Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

2027: Sanatan APC ya fadi dalilin da ya sa Tinubu ke samun goyon baya

Buhari ya taya Tinubu murnar cika shekara biyu a kan karagar mulkin Najeriya bayan rantsar da shi a shekarar 2023.

Tsohon shugaban ƙasan ya nuna cewa gyaran da Tinubu ke ƙoƙarin yi a ƙasar nan, abu ne wanda ba zai faru a dare ɗaya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng