'Yan Bindiga Sun Farmaki Kauyuka a Neja, an Tafka Gagarumar Barna
- Hankula sun tashi a jihar Neja bayan da wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai suka kai harin ta'addanci kan bayin Allah
- Ƴan bindigan waɗanda aka ƙiyasta cewa adadinsu ya fi mutum 100 sun kai hatin ne a wasu ƙauyuka guda uku na ƙaramar hukumar Munya
- Miyagun ƴan bindigan sun riƙa bi ƙauye bayan ƙauye suna cin karensu babu babbaka a yayin harin wanda suka kai a ranar Talata
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Neja - Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai wani ƙazamin hari a jihar Neja.
Ƴan bindigan waɗanda aka ƙiyasta yawansu ya haura 100 sun kai farmakin ne aƙalla ƙauyuka uku da ke ƙaramar hukumar Munya.

Source: Twitter
Jaridar Tribune ta rahoto cewa a yayin harin, ƴan bindigan sun kashe wasu mazauna ƙauyukan da dama tare da yin fashin fiye da shanu 200.
Ƴan bindiga sun yi ɓarna a Neja
Kauyukan da aka kai wa harin sun haɗa da Zagzaga, Chibani, da Kuchi da ke ƙaramar hukumar Munya.
Rahotanni sun bayyana cewa an kashe mutane da dama, ciki har da mata, yayin da ƴan bindigan suka riƙa kai farmaki daga ƙauye zuwa ƙauye.
Ƴan bindigan sun ƙona gidaje, sace kayan abinci yayin da suka ci karensu ba babbaka daga ƙarfe 4:00 na yamma zuwa 7:00 na dare.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa an kashe ɗaya daga cikin ƴan bindigan a ƙauyen Kuchi, amma ba a tabbatar da dalilin mutuwarsa ba.
A cikin ƙauyen Kuchi, ƴan bindigan sun ƙona sansanin jami’an tsaro na haɗin gwiwa. Rahotanni sun ce jami’an tsaron sun tsere daga sansanin ne bayan sun ga gawan ƴan bindigan da suka kawo harin.
Wasu majiyoyi sun nuna cewa ƴan bindigan sun taru ne a ƙauyen Kusasu da ke ƙaramar hukumar Shiroro, wacce ke iyaka da Munya, kafin su ƙaddamar da harin.
Me hukumomi suka ce kan harin?
Ƙoƙarin da aka yi don jin ta bakin Shugaban ƙaramar hukumar Munya, Hon. Aminu Najume, ya ci tura domin layukansa duk a kashe suke.
Sai dai kwamishinan tsaro na cikin gida, Birgediya Janar Mohammed Bello Abdullahi (mai ritaya), ya tabbatar da samun hare-haren ƴan bindiga a yankin, kodayake ya ce bai karɓi cikakken rahoto dangane da wannan harin ba tukuna.

Source: Original
Karanta wasu labaran kan hare-haren ƴan bindiga
- 'Yan bindiga sun farmaki jami'an tsaro a Katsina, an samu asarar rayuka
- Zamfara: Ƴan bindiga sun shammaci masu sallah a masallaci, sun kwashe al'umma
- 'Yan bindiga sun kai sabon hari Kogi, sun sace babban jami'in soja da ya yi ritaya
Ƴan bindiga sun kai hari a Abuja
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai hari a ɗaya daga cikin unguwannin birnin tarayya Abuja.
Ƴan bindigan sun mamaye unguwar 'Grow Homes' da ke a Chikakore, wani yanki da ke Kubwa a birnin Abuja.
Miyagun ƴan bindigan sun yi garkuwa da wasu mutanen unguwar bayan sun kai harin da misalin ƙarfe 12:00 zuwa 1:00 na dare.
Asali: Legit.ng

