"Ba Ɗan Kunar Bakin Wake ba ne," Ministan Tinubu Ya Faɗi Mutumin da Ya Tashi 'Bam' a Abuja

"Ba Ɗan Kunar Bakin Wake ba ne," Ministan Tinubu Ya Faɗi Mutumin da Ya Tashi 'Bam' a Abuja

  • Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya musanta rahoton cewa ɗan ƙunar bakin wake ne ya tashi bam a kusa da barikin sojojin Mogadishu
  • Wike ya ce hukumomin tsaro sun tabbatar da cewa abin da ya faru ba harin kunar bakin wake ba ne, wani mutumi ne ya jefa rayuwarsa a haɗari
  • Tsohon gwamnan Ribas ya ce rahoton da hukumar NEMA ta fitar ba gaskiya ba ne, yana mai cewa ya kamata a rika yin taka tsan-tsan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya musanta bayanin da Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta fitar kan bam din da ya tashi a Abuja.

Hukumar NEMA dai ta ce wani ɗan ƙunar bakin wake ne ya tashi kansa a kusa da barikin sojojin Najeriya da ke Mogadishu a babban birnin Najeriya.

Kara karanta wannan

Wike ya kasa hakura da kalaman Sule Lamido, ya yi martani mai zafi

Nyesom Wike.
Wike ya saɓawa bayanin da NEMA ta yi kan bam ɗin da ya fashe a Abuja Hoto: @GovWike
Source: Facebook

Ministan Abuja ya saɓawa bayanan NEMA

Sai dai ministan harkokin Abuja, Wike ya bayyana cewa tashin bam ɗin ba shi da alaƙa da harin kunar bakin wake kamar yadda NEMA ta yi ikirari, Vanguard ta rahoto.

Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas ya bayyana haka ne da yake zantawa da manema labarai yayin da ya fita rangadin duba wasu ayyukan tituna a Abuja.

Ministan na ƙoƙarin ganin an kammala ayyukan domin a kaddamar da su a bikin cikar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu shekaru biyu a kan mulki.

Da yake jawabi ga ƴan jarida, Mista Wike ya ce rahotannin da ya samu daga hukumomin tsaro sun sabawa bayanin da hukumar NEMA ta yi.

Wane mutumi ne ya tashi bam a Abuja?

Ministan ya ce:

“Babu wata hukuma ta tsaro da ta ce wannan abu da ya faru harin ƙunar baƙin wake ne, don haka bai kamata a kirkiri labarin da zai haifar da tsoro ga jama’a ba. NEMA ba hukumar tsaro ba ce, hukumomin tsaro na nan na aikinsu.

Kara karanta wannan

NEMA: Yadda ɗan ƙunar baƙin wake ya kusa tada bam a barikin sojoji a Abuja

“Abin da ya faru shi ne, wani mutumi ne ya je wurin da ake fasa duwatsu, ya ɗauko nakiya ya sa a aljihunsa, da alama bai san illa ko haɗarin hakan ba, sai abin ya tashi da shi.
"Kun ga wannan ba ɗan kunar baƙin wake ba ne, ya kamata mu yi taka tsan-tsan kan labaran da za nu yaɗa, ka da mu wuce gona da iri ta yadda za mu firgita al'umma."
Wike.
Wike ya ce mutum da bam ya tashi da shi bai san illar abin da ya ɗauko ba Hoto: Nyesom Wike
Source: Facebook

Jaridai Daily Trust ta ruwaito cewa fashewar ta auku ne a kusa da wani shingen bincike a gaban barikin sojojin Mogadishu da ke babban birnin tarayya, inda aka ce mutum guda ya mutu.

Duk da cewa NEMA ta fitar da rahoto kan abin da ta gano, rundunar sojoji da ‘yan sanda ba su fitar da cikakken bayani kan musabbabin lamarin ba, sun ce suna kam bincike.

Yadda bam ya tashi a kusa da barikin sojoji

A wani rahoton, kun ji cewa wani bam ya tarwashe a tashar mota da ke gaban barikin sojojin Najeriya na Mogadishu a Abuja.

Shaidu sun bayyana cewa ana zargin wani ne ya yi yunkurin kai harin kunar bakin wake amma ya rasa ransa a lokacin da bam din ya fashe.

Rundunar sojoji ta tabbatar da faruwar lamarin ranar Litinin da ta gabata, amma ta ce babu wani abin fargaba domin an shawo kan lamarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262