Tsaro: 'Dan Majalisa Ya Yiwa Ministan Buhari Fata Fata kan Sukar Gwamnatin Tinubu
- Donald Ojogo ya soki tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami SAN, bayan ya caccaki gwamnatin Bola Ahmed Tinubu
- Hon Ojogo, ya kara da zargin Malami da hana yaki da rashin tsaro a Kudu maso Yamma a lokacin gwamnatin da ta gabata
- 'Dan majalisar ya yi watsi da kalaman Malami kan Tinubu, yana cewa bai kamata ya soki tsarin mulki da ‘yan sanda na jihohi ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Ɗan majalisa mai wakiltar Ilaje/Ese-Odo a Majalisar Tarayya ta Tarayya, Hon. Donald Kimikanboh Ojogo, ya caccaki tsohon Ministan Muhammadu Buhari, Abubakar Malami.
Ya ce tsohon Ministan Shari’a na Najeriya, Abubakar Malami, babban cikas ne ga yaki da matsalar tsaro a kasar, musamman a yankin Kudu maso Yamma.

Source: Facebook
Nigerian Tribune, ta wallafa cewa Hon. Ojogo ya kara da bayyana rashin dacewar kalaman Malami dangane da amincewar APC na Shugaba Bola Tinubu ya nemi wa’adin mulki na biyu.
Ya bayyana cewa furucin Malami bai dace da wanda ke kishin dimokuraɗiyya da ci gaban kasa ba, saboda ba shi da bakin.
'Dan majalisa ya soki furucin Malami kan Tinubu
The Guardian ta ruwaito cewa Ojogo ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda Malami ke nuna ƙyama ga shirin kafa 'yan sandan jihohi
Ya bayyana cewa hakan hujja ce da ke nuna cewa Malami ba ya goyon bayan ingantaccen tsarin tarayya mai aiki a zahiri.
Ojogo ya ce:
“Ni dan Majalisar Tarayya ne. Ba na magana da yawun fadar shugaban kasa, kuma ba na kokarin karɓar aikin kakakin jam’iyya. Sai dai na ga wajibi ne in maida martani ga tsohon babban lauya, Malami wanda na sha gwagwarmaya da shi a lokacin gwamnatin Buhari.”
'Dan majalisa: 'Malami ya kawo cikas a Najeriya'
Ojogo ya bayyana Malami a matsayin wanda ya jawo cikas ga duk wani yunkuri da gwamnoni na Kudu maso Yamma suka yi domin shawo kan matsalar tsaro a yankin su.

Source: Facebook
Ya ce:
“Ni da kaina na shaida yadda Malami ke kokarin hana duk wani shiri da gwamnoni karkashin jagorancin Akeredolu suka tsara domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.”
“Ko lokacin da shirin kafa rundunar Amotekun ke tasowa, Malami na cikin wadanda suka fi kokarin hana shi, duk da goyon bayan jama’a daga sassa daban-daban na yankin.”
Ojogo ya yaba da jaruntakar marigayi Gwamna Rotimi Akeredolu da sauran gwamnoni na yankin Kudu maso Yamma.
An ji shi yana mai cewa bajintarsu ce ta rage matsalolin garkuwa da mutane da kashe-kashe a yankin.
Malami ya yiwa gwamnatin Tinubu kaca-kaca
A wani labarin, mun wallafa cewa tsohon Ministan Shari’a na Najeriya, Abubakar Malami (SAN), ya nuna damuwa kan yadda jam’iyyar APC mai mulki ke fifita siyasa a kan matsalolin tsaro.
Malami ya zargi jam’iyyar APC da gazawa wajen gudanar da mulki, yana mai cewa jam’iyyar ta fi mai da hankali kan shirye-shiryen siyasa da zabukan 2027, maimakon magance matsalolin kasa.
Ya caccaki amincewar jam’iyyar da Shugaba Bola Tinubu a matsayin ɗan takara na shugaban ƙasa a 2027, yana mai cewa hakan alama ce da ke nuna cewa APC ba ta damu da jama'a ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


