Yadda Aka Samu 'dan Sandan da aka Kashe a Kano da Hannu a Kisan 'Barayin Kaji' Tun 2021
- An yi waiwaye a kan babban jami'in dan sanda da wasu matasa suka hallaka a Kano bisa zargin azabtar da dan uwansu har lahira
- Baturen 'yan sanda, SP Baba Ali ya gamu da ajalinsa shekaru hudu bayan kotu ta kama shi da zama sanadin rasuwar matasa a Bauchi
- Matasan da aka tabbatar da mutuwarsu bayan ya azabtar da su, sun shiga hannu ne a bisa zargin satar kajin wani bawan Allah a Bauchi
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Bauchi – An gano yadda kotu ta hukunta runduar yan sandan kasar nan saboda yadda dan sandan da aka kashe a Kano, SP Baba Ali ya jawo asarar rayukan wasu matasa a 2020..
A lokacin, wata Babbar Kotun Tarayya da ke Bauchi ta umarci rundunar ‘Yan Sandan Najeriya da ta biya N210m a matsayin diyya ga iyalan matasan da aka azabtar har lahira.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta wallafa, wadanda aka azabtar har suka mutu sun hada da Ibrahim Babangida da Ibrahim Samaila, yayin da aka ji wa Abdulwahab Bello rauni a ranar 21 ga watan Yuli, 2020.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kama matasan ne bisa zargin satar kaji daga wani gonar kaji mallakin wani tsohon dan sanda.
Kotu ta yi hukunci a kan yan sanda
Channels TV ta ruwaito cewa a zaman kotun da aka yi, Mai shari’a Hassan Dikko, ya yanke hukunci daban-daban guda uku inda ya bayyana cewa abin da ‘yan sandan suka aikata ya ci karo da dokar kasa.
Mai shari’a Dikko ya ce azabtar da mutanen da ake zargi ya sabawa hakkokinsu na dan Adam da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka yiwa kwaskwarima.
A hukuncin da ya yanke, mai shari’a ya umarci a biya Naira miliyan 100 ga Hafsatu Babangida da Hajara Samaila, iyayen haihuwa na Ibrahim Babangida da Ibrahim Samaila.
Wannan hukunci na nufin cewa rundunar ‘yan sanda za ta biya jimillar Naira miliyan 210 a matsayin diyya kan wannan danyen aiki da jami’inta ya aikata.
A karshe an kashe dan sandan Kano
Babban jami'in dan sandan kasar nan, DPO Baba Ali ya gamu da ajalinsa a Kano bayan matasan karamar hukumar Rano sun zarge shi da kashe wani matashi.
A tattaunawa da Legit a ranar Litinin da lamarin ya afku, wani mazaunin garin ya bayyana cewa:
"Ya kashe kusan mutane 10 a nan, da an kai masa yaran mu, sai ya hau su da duka da kulki."
Elder Karofi ya bayyana cewa ya san marigayin a lokacin da yake garin Bauchi, kuma ya ce a iyakar saninsa, mutumin kirki ne.
Ganin videon kisan da akayi wa DPOn Rano ya tayar min da hankali. Se da naga hoton sa naga ashe CSP Baba Ali ne. Na san shi mun saba Lokacin da ya rike DPO na Central Market Division a Bauchi.
Duk Juma’a yana tura min da gaisuwar Juma’a. Mutumin kirki ne a sanin da na masa. Tsakani na da shi akwai mutuntawa da girmamawa sosai. Allah ubangiji ya masa rahama.
- Elder Karofi
Da yake cigaba da tofa albarkacin bakinsa a shafin Facebook, matashin ya ba da shawarar a rika bincik kuma a guji daukar doka a hannu.

Source: Facebook
Labaran da aka samu daga baya sun bayyana cewa an kai wani matashi hannun DPO Baba Ali bisa zargin tseren babur ba bisa ka'ida, inda aka yi masa dukan kawo wuka.
Daga baya, an tabbatar da rasuwar matashin, lamarin da ya harzuka jama'ar gari har suka dauki hukunci a hannunsu.
'Yan sanda sun kama wani matashi a Kano
A baya, kun ji rundunar ƴan sandan Kano ta sanar da cafke wani mutum da ake zargi da hannu a kisan gilla da aka yi wa wata matar aure a unguwar Tsamiyar Duhuwa a jihar.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ya ce sai da aka yi bincike mai zurfi kafin a kai ga gano mutumin.
Wanda ake zargi da kisan, Shu’aibu Abdulkadir, mai shekaru 35 daga unguwar Madatai, ya amsa cewa shi ne ya kutsa cikin gidan Rumaisa da daddare, inda ya shake ta da dankwalinta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


