NEMA: Yadda Ɗan Ƙunar Baƙin Wake Ya Kusa Tada Bam a Barikin Sojoji a Abuja
- Hukumar NEMA ta tabbatar da fashewar bam din da ya auku a gaban barikin sojoji na Mogadishu, Abuja, a ranar Litinin da rana
- Wani ɗan kunar bakin wake ya rasa ransa lokacin da bam ɗin da ke jikinsa ya tashi yayin yunƙurin shiga cikin barikin Mogadishu
- An rahoto cewa jami’an tsaro daga sojoji, 'yan sanda, DSS, FRSC da kuma NEMA sun killace wajen da abin ya faru tare da yin bincike
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta bayyana cikakken bayani kan fashewar bam da ta auku a ranar Litinin, a babban birnin tarayya, Abuja.
Legit Hausa ta ruwaito cewa fashewar bam din ta auku ne a gaban shahararren barikin sojoji na Mogadishu da ke kan hanyar Abuja-Nyanya.

Source: Twitter
Bam ya tashi a kusa da sojoji a Abuja
Wasu ganau sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa ana zargin wani ɗan kunar bakin wake da rasa ransa a lokacin da bam ɗin ya tashi.
Lamarin ya jefa jama’ar da ke wucewa a lokacin cikin firgici, inda mutane da dama suka watse domin neman tsira daga fashewar.
Rundunar ƴan sanda ta bayyana cewa sun fara gudanar da cikakken bincike, ciki har da tantance abubuwan fashewar ta hanyar binciken forensics.
A wata sanarwa da NEMA ta fitar ranar Talata, a shafinta na X, ta bayyana cewa fashewar ta auku ne yayin da wani ɗan ƙunar baƙin wake ya yi yunƙurin shiga cikin barikin sojojin Mogadishu.
NEMA ta ba da agaji bayan fashewar bam
Bam ɗin ya fashe a jikin mutumin yayin da yake ƙoƙarin shiga, wanda hakan ya yi sanadin mutuwarsa a wurin nan take, yayin da wani mai wucewa kusa da wurin ya jikkata.
NEMA ta ce ta samu kiran gaggawa kan fashewar da misalin ƙarfe 1:47 na ranar Litinin, inda ta aika da tawagarta domin haɗa kai da jami’an tsaro wajen bada agaji.
Sanarwar ta ce:
"Da misalin ƙarfe 1:47 na ranar Litinin 26 ga Mayu, 2025, NEMA AOO ta samu kiran gaggawa game da fashewar bam a gaban barikin Abacha da ke kan titin Abuja-Keffi.
"Tawagar AYA ERAB ta shiga aiki nan da nan domin bada taimako, kuma ta iske har jami’an tsaro sun rufe wurin da abin ya faru domin ba da tsaro."

Source: UGC
'Dan ƙunar baƙin wake ya mutu nan take
Sanarwar ta ci gaba da cewa:
“Bayanan da aka tattara sun bayyana cewa wani ɗan kunar bakin wake ya yi yunkurin kutsawa cikin barikin sojojin, amma bam ɗin da ke jikinsa ya fashe.
"Fashewar ta yi sanadin mutuwar ɗan ƙunar baƙin waken nan take, yayin da wani da ke wucewa a wajen ya samu raunuka.
"Rundunar EOD ta ƴan sanda ta kai wanda ya jikkata asibitin kasa, sannan ta karɓi ikon gudanarwar wurin domin ci gaba da bincike. An kuma kammala aikin da misalin ƙarfe 5:29 na yamma."
Sanarwar ta ce jami’an da suka halarci wurin da bam din ya tashi sun haɗa da NEMA, sojoji, 'yan sanda, DSS da kuma FRSC.
Ana zargin bam ya tashi a Abuja
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu mazauna babban birnin tarayya, Abuja, sun shiga fargaba bayan wani abin fashewa da ake zargin bam ne ya tashi.
Shaidu sun bayyana cewa fashewar ta auku ne a ɗakin wasu maza biyu, inda aka fara zargin tukunyar gas ce ta fashe, amma babu tabbaci a kai.
Majiyoyi sun ce an sanar da ofishin ‘yan sanda faruwar lamarin, inda suka bukaci a kira ƙwararrun jami’an kwance bama-bamai domin tantance gaskiyar lamarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


