Martanin 'Yan Najeriya yayin da Mahajjaciya daga Zamfara Ta Haihu a Madina
- Wata mahajjaciya daga jihar Zamfara ta samu ƙaruwa bayan ta haihu a birnin Madina na ƙasar Saudiyya
- Mahajjaciyar wacce ba a bayyana sunan ta ba dai ta haihu ne yayin da ake gudanar da aikin Hajjin bana na shekarar 2025
- Ƴan Najeriya da dama sun yi martani inda suka nuna mamaki kan yadda aka bari ta tafi zuwa ƙasa mai tsarki alhalin tana ɗauke da juna biyu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Saudiyya - Wata Mahajjaciya daga jihar Zamfara ta haihu a birnin Madina, Saudiyya, yayin gudanar da aikin Hajjin bana.
Wannan lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta kan yadda aka bari ta yi tafiyar tana cikin watan haihuwa.

Source: Facebook
Mahajjaciya ta haihu a kasar Saudiyya
Labarin ya fito ne daga Independent Hajj Reporters of Nigeria, inda suka wallafa hoton mahajjaciyar da abin da ta haifa a shafinsu na Facebook a ranar Talata.
Tun daga lokacin, labarin ya karaɗe shafukan sada zumunta, inda ƴan Najeriya da dama ke bayyana mamaki tare da tambayar yadda hukumomin Hajji na Najeriya da na Saudiyya suka yi sakaci.
Jaridar Leadership ta ce hukumomi ba sa bada dama ga mata masu ciki, musamman masu ciki da ke a watanni uku na ƙarshe, su halarci aikin Hajji, saboda wahalhalun da ke tattare da ibadar.
A mafi yawan lokuta, irin waɗannan mata ba a ba su damar tafiya idan aka gano suna da ciki a lokacin gwajin lafiya.
Wane martani ƴan Najeriya suka yi?
Aminu Abdullahi:
"Idan aka zo kan Najeriya, komai yana iya yiwuwa, cikakkiyar mace mai ciki. Ta yaya za ta iya gudanar da aikin Hajji tana ɗauke da cikin wata tara? Ko da ya ke, muna taya ta murna."
Hassan Ubali:
"Ta yaya ta tsallake ka'idoji har ta isa Madina da ciki?"
Muhammad Ariko:
"Alhamdulillah, amma me ya sa aka bari mace mai ciki ta fara wannan tafiya tun da farko?"

Source: Facebook
Usman Shehu Karofi:
"Tambayar da na fara tunani kenan.....ta yaya ta tsallake irin waɗannan tsauraran bincike tana da cikon wata kusan tara?? Wannan yana nuna cewa babu abin da ke tafiya daidai a Najeriya! Ko da ya ke, muna taya ta murna !!"
Muhammad Suraj:
"Mai galihu ce dai ko? Domin mace mai ciki ba a yarda ta je aikin hajji ba."
Sakina Attahir:
"Muhammad Suraj, toh yanzu dan Allah yaya za ta yi aikin hajji ba tare da tsarki ba. Me ya sa mutanenmu suke kama da jakkai haka?"
Nasiru Abubakar Danjibga:
"Masha Allah, Alhamdulillah. Allah Ya raya Ya shirya mana kuma Ya bada abun yi musu hidima."
Muttaka M. Haruna:
"Najeriya 🇳🇬 🇳🇬 Allah ya kyauta."
Fatima Zahra:
"Masha Allah. Allah ya raya jariri. Ban san abin faɗa ba, abin mamaki ne sosai."
Mahajjaciya ta rasu a Saudiyya
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata mahajjaciya daga jihar Edo ta riga mu gidan gaskiya yayin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2025.
Hajiya Hadizatu Dazumi mai shekara 75 ta rasu ne a wani asibiti da ke birnin Makkah na ƙasar Saudiyya.
Mahajjaciyar dai ta rasu ne bayan ta kammala ɗawafi a Ka'aba lokacin da rashin lafiya ya kama ta.
Asali: Legit.ng


