An Gano Yadda Dan Kunar Bakin Wake Ya So Kutsawa Barikin Sojoji a Abuja

An Gano Yadda Dan Kunar Bakin Wake Ya So Kutsawa Barikin Sojoji a Abuja

  • Wani bawan Allah da aka kyautata zaton dan kunar bakin wake ne ya yi yunkurin tafka tsiya a yayin da ya so kai mummunan hari Abuja
  • Jami'an tsaro ne suka fara tare mutumin yayin da ya ke kokarin shiga barikin sojoji na Mogadishu, wanda aka fi sani da Barikin Abacha
  • Rundunar soji da sashen kawar da bama-bamai na yan sanda sun fara bincike don gano asalin abin da ya fashe da tabbatar da tsaron jama'a

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Wani mutum da ake zargin dan kunar bakin wake ne ya mutu a ranar Litinin bayan wani bam da ya ɗaura a jikinsa ya tashi da shi.

Abin fashewar ya tarwatse da shi a lokacin da yake ƙoƙarin kutsa kai cikin Barikin Mogadishu da aka fi sani da Barikin Abacha a Abuja.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: 'Bam' ya tashi a kusa da sojoji a Abuja, mutane sun shiga fargaba

Abuja
Dan kunar bakin wake ya hallaka kansa a Abuja Hoto: Getty images
Source: Getty Images

The Nation ta wallafa cewa majiyoyi daga rundunar soji sun bayyana cewa lamarin ya faru da misalin ƙarfe 2:14 na rana a ƙarƙashin gadar da ke kusa da Barikin.

Sun bayyana cewa lamarin ya afku a kusa da wurin da ake sauke fasinjoji kafin su shiga samu abin hawan da zai shigar da su zuwa barikin sojojin.

Abuja: 'Dan kunar bakin wake ya kashe kansa

A cewar rahoton Punch, ɗaya daga cikin majiyoyin ya ce mutumin ya fito daga cikin wata mota kirar Volkswagen Golf, kuma ya fara tafiya zuwa wurin binciken tsaro.

Majiyar ta ce:

“Wani mutum da ba a san ko wanene ba, wanda ke ɗauke da bam da aka kulla (IED), ya fito daga cikin mota a kusa da Barikin Mogadishu a ƙarƙashin gadar ƙafa, kuma ya yi ƙoƙarin shiga barikin."
“Lokacin da motsinsa ya zama abin zargi, soja da ke bakin aiki ya tsayar da shi tare da umartarsa da ya ja baya don tantance shi. Amma sai ya matsa kaɗan gaba, nan take bam ɗin da yake ɗauke da shi ya tashi, ya kashe shi tare da jikkata wasu mutane biyu.”

Kara karanta wannan

Kano: Kotun shari'a ta yi hukunci, za a kashe matashin da ya babbake masallata

Abuja: Sojoji, 'yan sanda sun fara bincike

Har zuwa lokacin da ake haɗa wannan rahoto, mai magana da yawun rundunar soji ta Najeriya, Laftanar Kanal Onyechi Anele, bai fitar da wata sanarwa ba game da lamarin.

Yan sanda
Rundunar yan sanda ta tabbatar da afkuwar fashewar bam a Abuja Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Sai dai Mai magana da yawun yan sanda, SP Josephine Adeh, ta bayyana cewa fashewar ta faru ne da misalin ƙarfe 2.50 na rana a hanyar Mararaba-Nyanya da ke Abuja.

Ta ce:

“An ceto wani mutum guda daga wurin da lamarin ya faru, kuma an garzaya da shi asibiti inda ake kula da lafiyarsa.”

Ta ƙara da cewa an fara cikakken bincike da haɗin gwiwar masu nazarin fashewar bama-bamai don gano musabbabin da kuma nau’in fashewar.

'Yan bindiga sun mamaye unguwar Abuja

A baya, mun wallafa cewa Wasu gungun ‘yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai hari a unguwar Grow Homes da ke cikin Chikakore, wani yanki na Kubwa a Abuja.

Wani mazaunin unguwar ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi awon gaba da wani namiji da kuma wata mace. Sai dai daga bisani an same ta a cikin unguwar, bayan sun sake ta.

Rahoton ya ce maharan sun yi amfani da dare da rashin isasshen tsaro wajen kutsa kai cikin yankin, wanda ke a matsayin unguwa mai tasowa a babban birnin tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng