An Hallaka DPO a Kano yayin da Rikici Ya Barke tsakanin Matasa da 'Yan Sanda

An Hallaka DPO a Kano yayin da Rikici Ya Barke tsakanin Matasa da 'Yan Sanda

  • Wasu matasa sun kai hari ofishin 'yan sanda a Rano, jihar Kano, sakamakon mutuwar wani matashi da aka kama da zargin shan ƙwaya
  • Shugaban ofishin 'yan sandan Rano ya rasu sakamakon raunuka da ya samu a harin; wanda aka kona motocin sintiri biyu da wasu 10
  • An kama mutum 27 da ake zargi, yayin da kwamishinan 'yan sanda ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano – Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da mutuwar shugaban ofishin 'yan sanda (DPO) bayan wani hari da 'yan daba suka kai ofishinsu a karamar hukumar Rano.

Rundunar ta ce lamarin ya faru ne da yammacin Lahadi, 25 ga Mayu, yayin da wasu matasa suka fusata saboda mutuwar wani matashi da aka kama.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan daba sun farmaki kamfanin simintin a Gombe, an kashe mutum 1

Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da mutuwar DPO bayan 'yan daba sun farmaki ofishin 'yan sanda a Kano
Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa. Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

DPO ya mutu bayan harin ofishin 'yan sanda

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanar da hakan a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar Kiyawa ta ce an cafke matashin mai suna, Abdullahi Musa, mai gyaran babur, bayan korafe-korafe daga jama’a cewa yana barazana ga mutane idan ya sha miyagun ƙwayoyi.

Sanarwar ta ce:

“Bayan kama shi, jikin Musa ya yi tsanani a hannun ‘yan sanda, inda aka garzaya da shi asibitin Rano, amma ya rasu washegari da safe yayin da ake jinyarsa."

Bayan isar labarin rasuwarsa, wasu matasa suka mamaye ofishin ‘yan sanda na Rano inda suka farfasa gine-gine, suka kona wasu sassa na ofishin da kuma motocin sintiri guda biyu, sannan suka lalata wasu motoci 10.

'Yan sanda sun cafke mutane 27 a Kano

Sanarwar ta bayyana cewa DPO din da ke bakin aiki a lokacin ya samu raunuka masu tsanani yayin harin, kuma aka garzaya da shi asibitin koyarwa na Aminu Kano, inda ya rasu daga baya.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kama wanda ya jagoranci kashe DPO a Kano da wasu mutane 40

Rundunar ta ce ta kama mutane 27 da ake zargi da hannu a harin, kuma an dawo da zaman lafiya a yankin.

Kwamishinan ‘yan sandan Kano, Ibrahim Bakori, ya kai ziyara wurin da abin ya faru tare da yin gaisuwar ta’aziyya ga Sarkin Rano, Alhaji Mohammed Umar.

Kwamishinan 'yan sandan Kano ya ba da tabbacin gudanar da bincike kan mutuwar DPO
Kwamishinan 'yan sandan Kano, CP Ibrahim Bakori. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Twitter

'Yan sanda za su fara bincike kan lamarin

Ya ba da umurnin gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin lamarin, tare da tabbatar da gaskiya da adalci ga wadanda aka zalunta.

Ibrahim Bakori ya jajanta wa iyalan DPO din da ya rasu tare da roƙon jama’a da su kwantar da hankalinsu, su bar hukuma ta yi bincike cikin natsuwa.

A ƙarshe, mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar, ya tabbatar da cewa za su ci gaba da kiyaye doka da oda a jihar, tare da buƙatar haɗin kai daga jama’a yayin bincike.

Karanta sanarwar Kiyawa a nan kasa:

Rikicin 'yan daba a Kano

A 'yan shekarun nan, matsalolin aikata laifuka sun kara kamari a Kano da wasu sassan Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

An kai farmaki gidan boka, an kama mutane 3 suna kokarin asiri da yarinya

Daga fashi da makami zuwa ta'ammali da miyagun ƙwayoyi, rahotanni da dama na nuna cewa rashin tsaro da lalacewar tarbiyya na kara tsananta.

Ana samun matasa da dama suna shiga harkokin daba da ‘yan kungiyar asiri, musamman a cikin birane da unguwannin da ke fama da talauci da rashin aikin yi.

Haka kuma, ana kara samun tashin hankali tsakanin jama’a da jami’an tsaro, inda rashin yarda da yadda ake gudanar da bincike ko tsare mutane ke haddasa rigingimu da cin zarafi.

A wasu lokuta, jama’a na daukar doka a hannunsu saboda rashin amincewa da hanyoyin hukuma. Wannan kuwa yana nuna irin gibin da ke tsakanin al’umma da jami’an tsaro.

Wani abin damuwa shi ne yadda karancin ilimi da rashin kulawa daga iyaye da shugabanni ke barin matasa cikin duhu, suna komawa zuwa hanyar da bata dace ba.

A wannan hali, akwai bukatar hadin gwiwa tsakanin malamai, shugabanni, da jami’an tsaro domin farfado da tarbiyya da tabbatar da zaman lafiya a Kano da sauran yankunan Arewa.

'Yan Kano sun yi martani

Kara karanta wannan

Yadda aka samu 'dan sandan da aka kashe a Kano da hannu a kisan 'barayin kaji' tun 2021

A zantawar Legit Hausa da wasu 'yan asalin Kano, sun nuna damuwa kan yadda jama'a ke daukar doka a hannu, har ta kai ga kisan kai.

Abba Hassan Gezawa ya ce abin da matasan suka yi, ya saba wa ka'idar shari'ar Musulunci, yana mai cewa:

"Ko da ace akwai kwararan hujjoji da suka nuna DPO din ne ya kashe Abdullahi, to bai kamata gungun mutane su kashe dan sandan ba, sai su hada hujjoji, su yi kararsa, ko a kotun Musulunci ce, tun da shi ma ai Musulmi ne.
"Idan aka gabatar da kwararan hujjoji, kotu za ta iya yanke masa hukuncin kisa daidai da laifin da ya yi. Amma yanzu da aka kashe shi, wace riba aka samu?
"Za a ci gaba da kama mutane yayin da ake bincike kan wadanda suka kashe dan sandan, karshe, wani ya tafi kenan, zai kare rayuwarsa a gidan yari."

- Abba Gezawa.

Shi kuwa Ismail A.T.O, gargadar 'yan sanda ya yi kan irin tsaurin da suke sanya wa wajen tafiyar da masu laifi.

"Wani lokacin su ma 'yan sandan da laifinsu. Muna karanta wa a Facebook da sauran kafofin watsa labarai yadda ake zargin 'yan sanda da azabtar da wadanda ake zargi.

Kara karanta wannan

An kama wanda ya shiga har gida ya yi wa matar aure yankan rago a Kano

"An ce dokar kasa ta ce a gaggauta kai wanda ake zargi kotu a awanni 24, ko kuma awanni 48 idan babu kotu a kusa, to amma me ke faruwa yanzu? Sai ka tarar an ajiye wanda ake zargi kwana da kwanaki, ana azabtar da shi.
"Ga 'yan sandan da ke yi hakan, ya kamata su daina, ko ba don komai ba, sai dai kiyaye doka da odar da ta kafa aikinsu na dan sanda, tare da yi wa 'yan kasa adalci."

- Ismaill A.T.O.

Matasa sun kona ofishin 'yan sanda a Kano

Tun da fari, mun ruwaito cewa, fusatattun matasa sun kona ofishin 'yan sanda a Rano, Kano, bayan rikici ya barke sakamakon mutuwar wani matashi a hannun 'yan sanda.

Masu zanga-zangar sun zargi DPO Baba Ali da dukan da ya kai ga mutuwar Musa yayin da yake bincike a kansa, abin da ya tayar da hankula a yankin.

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa za a gudanar da bincike, yayin da aka raunata DPO da wasu mutane biyu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com