Kishi Kumallon Mata: Yadda Matar Aure Ta Hallaka Kishiyarta a Katsina
- Wata matar aure ta faɗa komar ƴan sanda bayan an zarge ta da aika-aika kan abokiyar zamanta a Katsina
- Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta tabbatar da cafke matan auren kan zargin kashe kishiyarta har lahira
- Mijin matan ne dai ya kai rahoton lamarin ga ƴan sanda bayan ya dawo kasuwa ya tarar mummunan abu a gidansa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta cafke wata matar aure mai shekaru 25 da haihuwa mai suna Rabi’a Labaran, bisa zargin kashe kishiyarta, Zainab Lawal mai shekaru 30.
Ana zargin matar auren ne da kashe kishiyarta bayan wani saɓani da ya faru a tsakaninsu a garin Daura da ke jihar Katsina.

Source: Facebook
Tashar Channels tv ta ce hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan Katsina, DSP Abubakar Sadiq-Aliyu ya fitar a ranar Lahadi, 25 ga watan Mayun 2025.
Matar aure ta kashe kishiyarta a Katsina
Mummunan lamarin mai ban tausayi ya faru ne da daren ranar 24 ga watan Mayu, 2025, a bayan makarantar firamare ta Dadi da ke unguwar Sabon Gari a garin Daura.
Kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa saɓanin da ya haɗa matan biyu ya rikide zuwa rikici mai muni wanda ya jawo aka samu asarar rai, rahoton The Punch ya tabbatar.
DSP Abubakar Sadiq ya ce bayan faruwar lamarin, mijin matan Nasir Yusuf, ya kai rahoto zuwa ofishin ƴan sanda na Sabon Gari.
Ya sanar da ƴan sanda cewa ya dawo daga kasuwa ya samu matarsa ta fari, Zainab Lawal, ƴar shekara 30, kwance cikin jini, bayan an daɓa mata wuka sau da dama.
Kakakin ƴan sandan ya ƙara da cewa bayan karɓar rahoton, DPO na yankin ya jagoranci jami’an tsaro zuwa wurin da abin ya faru, inda suka garzaya da matar zuwa asibitin tarayya da ke Daura domin ba ta agajin gaggawa.
Sai dai, likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da mutuwarta.
Yayin bincike, an kama kishiyarta, wato Rabi’a Labaran, mai shekara 23, bisa zargin hannu a cikin lamarin.
Wacce ake zargin ta amsa laifinta, tana mai cewa saɓani tsakaninsu ya rikiɗe zuwa faɗa, wanda ya haifar da wannan mummunan lamari.

Source: Original
Kwamishinan 'yan sanda ya ba da shawara
Yayin da ake ci gaba da bincike, kwamishinan ƴan sandan jihar Katsina, Bello Shehu, ya ja hankalin jama’a da su guji duk wani nau’in tashin hankali a cikin gida tare da nisantar ɗaukar doka a hannunsu.
Kwamishinan ya bukaci jama’a da su riƙa neman mafita ta fuskar doka a duk lokacin da rikici ya taso, domin daukar doka a hannu na haifar da ɓarna.
An cafke kishiya mai azabtar da jarirai
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan sanda sun cafke wata mata kan zargin azabtar da jarirai a jihar Adamawa.
Ƴan sanda sun cafƙe matar ne bayan an zarge ta da laifin azabtar da jarirai guda biyu waɗanda ke ƙarƙashin kulawarta.
Mutanen unguwa sun gayawa ƴan sanda cewa matar mai shekara 37 a duniya ta saba nuna wannan mummunar ɗabi'ar duk da ba ta taɓa haihuwa ba.
Asali: Legit.ng

