Wata mata ta kashe miji da kanin ta da shinkafar bera a Katsina
Labarin da muke samu da dumin sa daga Katsina na nuni ne da cewa wata matar aure mai shekaru 15 a duniya mai suna Dausiya Abdulmumin dake zaune a unguwar Danmayaki a cikin karamar hukumar Bakori ta kashe mijinta da kuma kanin ta.
Mun samu dai cewa matar ta kashe mijin nata ne mai suna Saminu Usaman mai shekaru 27 a duniya sai kuma Muhammad Abdulmumin dake zaman kanin ta mai shekaru 18 a duniya a kwanan baya.
Legit.ng haka zalika ma dai ta samu cewa amaryar da ta yi kisan duka-duka satin ta biyu da aure inda ake zargin cewa bata son mijin ne.
Binciken farko-farko dai sun tabbatar da cewa Dausiya din ta yi anfani ne da shinkafar bera da ta sa a cikin abincin gidan wanda kuma hakan yayi sanadiyyar kisan na mijin na ta da kanin ta dake zaune a gidan.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng