Abuja: Shugaba Tinubu Ya Gabatar da Kasafin Naira Tiriliyan 1.78 ga Majalisa

Abuja: Shugaba Tinubu Ya Gabatar da Kasafin Naira Tiriliyan 1.78 ga Majalisa

  • Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya mika kasafin kudin Naira tiriliyan 1.78 na birnin Abuja ga Majalisar Dokoki ta Kasa domin a amince da shi
  • Tinubu ya bayyana cewa ya aika kasafin ne da sahalewar sashe na 299 na kundin tsarin mulki, wanda ke ba shi damar mika kasafin Abuja ga majalisa
  • Ya ce za a yi amfani da 85% na kasafin wajen kammala ayyuka da aka fara, yayin da 15% zai tafi wajen sababbin ayyuka da nufin bunƙasa birnin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kasafin kudin Naira tiriliyan 1.78 na babban birnin tarayya (FCT) ga Majalisar Dokoki ta Kasa.

A wata wasika da Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas ya karanta a zauren majalisar a ranar Talata, Shugaba Tinubu ya bukaci ‘yan majalisar da su hanzarta amincewa da kasafin.

Kara karanta wannan

Majalisa za ta yi amfani da dattawan Najeriya domin yi wa Fubara da Wike sulhu

Tinubu
Tinubu ya mika kasafin kudin Abuja ga majalisar Najeriya Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Tinubu ya ce amincewa da kasafin cikin gaggawa zai taimaka wajen aiwatar da muhimman ayyukan ci gaba a birnin tarayya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasikar ta kara da bayyana cewa an mika kasafin ne domin ba wa gwamnati damar inganta rayuwar mazauna babban birnin tarayya da gudanar da manyan ayyukan ci gaba.

Tinubu ya aika kasafin Abuja zuwa majalisa

The Nation ta wallafa cewa Shugaba Tinubu ya bayyana cewa gabatar da kasafin kudin ya yi daidai da sashi na 299 na kundin tsarin mulkin Najeriya.

Ya ce wannan sashe yana bai wa shugaban kasa ikon mika kasafin kudin Abuja ga majalisar dokoki domin su amince da shi.

Tinubu
Tinubu ya bukaci majalisa ta gaggauta amincewa da kasafin kudin Abuja Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

A wasikar, Tinubu ya ce:

"Amincewa da wannan kasafi zai taimaka wajen zuba jari da zai habaka bangaren kiwon lafiya da walwalar jama’a, kara yawan amfanin gona, da kuma samar da ayyukan yi."

Ayyukan da Tinubu ya kulla a sabon kasafi

Kara karanta wannan

Peter Obi ya gano yadda gwamnatocin Najeriya ke jawo talauci a kasa

Yayin da yake bayani kan yadda za a kashe kudin, Tinubu ya bayyana cewa 85% na kudin za a karkatar da su ne zuwa kammala ayyukan gine-gine da ci gaba da aka riga aka fara.

Ya kara da cewa sauran 15% na kudin za su tafi ne wajen fara sababbin ayyukan more rayuwa a sassa daban-daban na birnin tarayya.

Tinubu ya ce:

"Ina rokon Majalisar Dokoki da ta ba wannan kasafi muhimmancin gaggawa, domin inganta ci gaba a babban birnin tarayya."

Sanata Ndume ya yabi shugaba Tinubu

A baya, kun ji cewa Sanata Ali Ndume, ya yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa matakin da ya ɗauka na hana shigo da kayayyakin waje da ake iya samar da su a Najeriya.

Gwamnatin tarayya dai ta ba da sabon umarni ga ma’aikatun gwamnati da su daina amfani da kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje, idan ana iya samar da su a cikin gida.

Da yake tsokaci a kan wannan mataki, Sanata Ndume ya bayyana cewa yana da matuƙar muhimmanci kuma zai taimaka wajen farfaɗo da masana'antu da tattalin arziki a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng