Ndume Ya Dakata da Sukar Tinubu, Ya Kwararo Yabo ga Shugaban Kasa
- Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Muhammad Ali Ndume ya kwararo yabo ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
- Ali Ndume ya yabi shugaban ƙasan ne kan matakin da ya ɗauka na hana shigo da kayayyakin da za a iya samar da su a cikin gida
- Sanatan wanda ya yabi da matakin, ya ce hakan zai taimakawa masana'antu tare da bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar nan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya yabawa Shugaba Bola Tinubu.
Sanata Ali Ndume ya yabawa shugaban ƙasan ne bisa ɗaukar matakin dakatar da shigo da kayayyakin waje da za a iya samar da su a cikin gida.

Source: Twitter
Tsohon mai tsawatarwar na majalisar dattawan ya yi wannan yabon ne a wata sanarwa da ya fitar a Abuja a ranar Talata, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan
Hadakar Atiku ta fara gigita APC, an fallasa abin da Tinubu ke kullawa 'yan adawa
Bola Tinubu ya hana shigo da kayan waje
Umarnin shugaban ƙasa ya buƙaci dukkan ma’aikatun gwamnati na tarayya da su fifita amfani da kayayyakin da ake samarwa a cikin gida wajen kashe kuɗin jama’a.
Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta ƙasa da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa a ranar Litinin.
Meyasa Sanata Ndume ya yabi Tinubu?
Da yake mayar da martani, Ndume ya bayyana wannan mataki a matsayin abin da zai taimaka gaya wajen bunƙasa masana’antu da ƴan kasuwa na cikin gida, farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa da kuma samar da ayyukan yi ga ƴan Najeriya.
"Abin farin ciki ne jin cewa Shugaba Tinubu ya ɗauki wannan matakin jarumtaka na hana shigo da kayayyakin da za a iya samar da su a cikin gida."
"Wannan zai taimaka sosai wajen haɓaka kasuwancin cikin gida, musamman a wannan lokaci da tattalin arziƙin Najeriya ke fuskantar matsaloli."

Kara karanta wannan
Tinubu ya yi karatun ta natsu, ya gano matsalar da ya kamata a magance a Najeriya
“Idan aka aiwatar da wannan mataki yadda ya kamata, zai kare masana'antun cikin gida da ke fafutukar tsayawa da kafafunsu daga ƙuncin gasa da kamfanonin waje waɗanda ke shigo da kayayyaki masu rahusa da waɗanda ba su da inganci."
“Idan aka kare masana’antun cikin gida, matasa za su samu ayyukan yi, hakan kuma zai haɓaka GDP ɗinmu, darajar Naira za ta ƙaru, domin za a rage matsin lamba a kan ajiyar kuɗin ƙasashen waje, kasancewar buƙatar canji daga masu shigo da kaya daga waje za ta ragu sosai."
- Sanata Ali Ndume

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta ce sanatan ya kuma buƙaci gwamnatin tarayya da ta sanya haraji mai tsoka kan wasu kayayyakin waje domin hana ƴan Najeriya sayensu, tare da ƙarfafa musu gwiwa su zabi kayayyakin da aka ƙera a cikin gida.
Tinubu ya faɗi ƙalubalen da ya fuskanta
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ya fuskanci ƙalubale mai yawa a farkon mulkinsa.
Shugaban ƙasan ya ce ƙalubalen matsin tattalin arziƙi da ya fuskanta a farkon fara mulkinsa sun yi masa yawa.
Mai girma Bola Tinubu ya bayyana cewa yadda aka taso shi a gaba da suka, ya ssnya ya tsinci kansa cikin ruɗani.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng