Lokaci Ya Yi: Tsohon Mataimakin Gwamna a Najeriya Ya Rasu

Lokaci Ya Yi: Tsohon Mataimakin Gwamna a Najeriya Ya Rasu

  • Lokaci ya cimma tsohon mataimakin gwamnan jihar Plateau, Sonni Gwanle Tyoden wanda ya rasu a ranar Lahadi, 4 ga watan Mayun 2025
  • Farfesa Sonni Gwanle Tyoden wanda ya kasance tsohon shugaban jami'ar Jos ya rasu ne bayan ya yi fama da ƴar gajeruwar rashin lafiya
  • Tsohon gwamnan Plateau, Simon Bako Lalong wanda suka yi aiki tare da Farfesa Tyoden, ya nuna alhininsa kan rasuwar marigayin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Tsohon mataimakin gwamnan jihar Plateau, Farfesa Sonni Gwanle Tyoden, ya yi bankwana da duniya.

Farfesa Sonni Gwanle Tyoden, wanda ya tsohon shugaban Jami’ar Jos, ya rasu ne da safiyar ranar Lahadi, 4 ga watan Mayun 2025 zbayan gajeruwar rashin lafiya.

Tsohon mataimakin gwamnan Plateau ya rasu
Farfesa Sonni Gwanle Tyoden ya rasu a ranar Lahadi Hoto: Caleb Mutfwang
Source: Facebook

Tsohon sakataren yaɗa labaransa, Mista Doman Wetkum, ne ya tabbatarwa da jaridar The Punch rasuwarsa.

Kara karanta wannan

APC ta ƙara ƙarfi a Kano, tsohon na hannun daman Kwankwaso ya koma jam'iyyar

“Eh da gaske ne. Ya rasu da safiyar ranar Lahadi. Abin takaici ne."

- Doman Wetkum

Simon Lalong ya yi ta'aziyyar Farfesa Tyoden

Jaridar Daily Trust ta ce tsohon gwamnan jihar Plateau kuma Sanata mai wakiltar Plateau ta Kudu, Simon Bako Lalong, ya bayyana baƙin cikinsa game da rasuwar Farfesa Sonni Tyoden, wanda ya rasu a Jos yana da shekaru 75.

A cewar wata sanarwa da hadiminsa na yaɗa labarai, Makut Macham, ya fitar a ranar Lahadi, Lalong ya jagoranci wasu tsofaffin mambobin majalisarsa zuwa gidan marigayin da ke Rayfield don yin ta’aziyya ga iyalansa.

Lalong ya bayyana Tyoden a matsayin abokin siyasa na haƙiƙa, amininsa, malami kuma wanda ya zama uba a siyasa, wanda ya yi aiki da ƙwarewa a matsayin mataimakin gwamna ƙarƙashin gwamnatin ceto ta jam’iyyar APC daga 2015 zuwa 2023.

Ya tuna cewa marigayin ya kawo kwanciyar hankali, hikima da ƙwarewa a cikin mulki, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar gwamnatinsu a cikin shekaru takwas.

Kara karanta wannan

Musa Kwankwaso ya faɗi maƙarƙashiyar da ake shiryawa NAHCON, Sheikh Pakistan

Sanatan ya ƙara da cewa Tyoden ya bambanta kansa a fagen ilimi ta hanyar koyarwa da bincike, inda ya horas da ɗalibai da dama da suka yi fice a fannoni daban-daban na rayuwa.

Ya yi addu’ar Allah ya jikansa, kuma ya bai wa uwargidansa, Abigail Tyoden, ƴaƴansu da dukkan ƴan uwansa haƙuri da juriyar rashin da suka yi.

Simon Bako Lalong
Simon Lalong ya je ta'aziyyar Sonni Gwanle Tyoden Hoto: Sen. Simon Bako Lalong
Source: Facebook

Yaushe za a yi jana'izar marigayin?

A madadin iyalan marigayin, Mista Gyenu Tyoden ya nuna godiya ga Lalong da tawagarsa bisa ziyarar ta’aziyya da suka kai musu.

Ya ƙara da cewa za a sanar da shirye-shiryen jana’izarsa a nan gaba.

Tsohon gwamnan Najeriya ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamna a mulkin soja a Najeriya, Manjo Janar Paul Ufuoma Omu, ya riga mu gidan gaskiya.

Paul Ufuoma Omu wanda ya mulki jihohin Cross Rivers da Akwa Ibom (waɗanda a baya ake kira jihohin Kudancin Gabas), ya yi bankwana da duniya ne a ranar Talata, 29 ga watan Afirilun 2025.

Marigayin wanda ya fito daga ƙauyen Igbide da ke ƙaramar hukumar Isoko ta Kudu a jihar Delta, ya rasu ne yana da shekara 84 a duniya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng