Tinubu Ya Yi Karatun Ta Natsu, Ya Gano Matsalar da Ya Kamata a Magance a Najeriya
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ya yarda ƙasar nan na fama da ƙalubalen rashin tsaro
- Mao girma Bola Tinubu ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na dawo da iko a yankuna musamman dazuka da ke ƙarƙashin miyagu
- Shugaban ƙasan ya bayyana cewa dole a magance matsalar rashin tsaro idan har ana son jawo masu zuba hannun jari a cikin ƙasar nan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na dawo da iko a yankunan da babu cikakken iko na gwamnati a faɗin ƙasar nan.
Shugaba Tinubu ya ce yana son dawo da ikon ne musamman a dazuka da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga dattawan jihar Katsina da shugabanni a wata liyafar dare da aka shirya a gidan gwamnati, a ziyararsa ta baya-bayan nan zuwa jihar.
Shugaba Tinubu ya yi alƙawarin amfani da sababbin na'urorin leƙen asiri da fasaha don yaƙar garkuwa da mutane, ƴan bindiga da ta'addanci a yankin.
Wace matsala Tinubu ya ce za a magance?
Yayin da yake magana kan matsalar rashin tsaro da ke addabar kasa, Tinubu ya ce hakan babban ƙalubale ne.
"Na yarda cewa matsalar tsaro babban ƙalubale ne ga ƙasar nan. Na yi wa jami’an sojoji jawabi inda na tabbatar da cewa za mu ɗauki dukkan matakan da suka dace don yakar ta’addanci da ƴan bindiga."
“Za mu zuba jari a fannin fasaha domin ƙwace dazuka. Tsaro batu ne na ƙasa baki ɗaya, ba wai na jiha ko yankuna kaɗai ba. Idan muna so mu jawo masu zuba hannun jari cikin gaskiya a Najeriya, dole ne mu magance matsalar tsaro."
"Zuba hannun jari na da tsoro, ba zai je wuraren da ake da ta’addanci da ayyukan ƴan bindiga ba. Za mu warware wannan matsala tare da haɗin gwiwar jihohi da ƙananan hukumomi."
- Shugaba Bola Tinubu

Source: Facebook
Tinubu ya ce tattalin arziƙi ya fara farfaɗowa
Shugaba Tinubu ya kuma nuna alamun farfadowar tattalin arziƙin Najeriya da ke karuwa, inda ya danganta ci gaban da aka samu kan wasu manufofi masu ƙarfi da gwamnatinsa ta aiwatar.
Ya ce gwamnatin tarayya tana duba yiwuwar ƙara inganta filin jirgin saman jihar Katsina domin samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziƙi.
Tinubu ya yabi Gwamna Radda
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙwararo yabo ga gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda.
Sjugaba Tinubu ya yabi gwamnan ne bisa gaskiyarsa, riƙon amana da jajircewarsa wajen sauke nauyin da ke kansa na mulkar mutanen Katsina.
Mai girma Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin tarayya tana tare da Gwamna Dikko Radda wanda ya kira a matsayin mai gaskiya da riƙon amana.
Shugaban ƙasan ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da taimakawa Gwamna Radda domin cigaba da ayyukan da yake yi a Katsina.
Asali: Legit.ng

