An Dakatar da Manyan Alkalan Najeriya 3, Za Su Rasa Albashin Wata 12

An Dakatar da Manyan Alkalan Najeriya 3, Za Su Rasa Albashin Wata 12

  • Majalisar NJC ta dakatar da alkalan kotu uku na shekara guda ba tare da albashi ba, saboda aikata manyan laifuffukan da suka sabawa doka
  • NJC ta umarci gwamnan Imo da ya soke nadin shugaban alkalan jihar tare da bukatar wasu jami’ai biyu su kare kansu cikin kwanaki bakwai
  • Majalisar ta kafa kwamiti tara don bincikar alkalai 27 da ake zargi da laifuffuka daban-daban, karkashin jagorancin CJN Kudirat Kekere-Ekun

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Majalisar shari’a ta kasa (NJC) ta sanar da da dakatar da wasu alkalan kotu uku na tsawon shekara daya, kuma ba za su sami albashin wata 12 ba.

Jane E. Inyang na kotun daukaka kara, reshen Uyo; Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya, Abuja; da Aminu Baffa Aliyu na babbar kotun tarayya a Zamfara su ne aka dakatar.

Kara karanta wannan

Ranar ma'aikata: Sababbin bukatun da kungiyoyin kwadago suka tura ga Tinubu

Majalisar NJC ta dakatar da wasu manyan alkalai 3 na shekara 1 ba tare da albashi ba
Alkalan Najeriya. Hoto: @njcNig
Source: Twitter

NJC za ta ladabtar da wasu alkalai

Majalisar NJC ta ba gwamnan Imo, Hope Uzodimma umarnin soke nadin Mai shari'a Theophilus Nnamdi Nzeukwu a matsayin shugaban alkalan jihar, inji rahoton Leadership.

An dauki wannan babban matakin ne taron majalisar NJC karo na 108 da aka gudanar a ranar 29 da 30 ga Afrilu, 2025.

NJC ta kuma bukaci shugaban alkalan jihar Imo da ya bayyana wa majalisar dalilin da zai sa ba za a dauki matakin ladabtarwa a kansa ba, cikin kwanaki bakwai.

Haka zalika, NJC ta bukaci shugaban kotun al'adu na jihar Imo da ya bayyana dalilin da yasa ya jagoranci zaman hukumar nada ma’aikatan shari’a (JSC), ba bisa ka’ida ba.

Kemi Babalola, mataimakiyar daraktar yada labarai ta NJC, ta ce majalisar ta kafa kwamiti tara domin bincikar alkalai 27 kan zargin aikata laifuffuka daban-daban.

A taron wanda ya gudana karkashin jagorancin shugabar alkalan Najeriya, Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, NJC ta cimma matsaya kamar haka:

Kara karanta wannan

Giwa: Gobara ta tashi a rumbun makaman sojojin Najeriya a Maiduguri

1. An dakatar da Justice Inyang

Majalisar ta dakatar da Justice Jane E. Inyang ta kotun daukaka kara, reshen Uyo, na shekara guda ba tare da albashi ba.

An dauki matakin dakatarwar ne bayan da kwamitin bincike na NJC ya gano cewa Inyang ta karya doka ta 3(5) na kundin da’ar alakalai ta 2016."

Inyang ta yi amfani da mukaminta ta hanyar bayar da umarnin da bai dace ba, don sayar da gidan man fetur da wasu harkokin kasuwanci na Hon. Udemesset.

2. An dakatar da Justice Ekwo

Hakazalika, majalisar NJC ta dakatar da Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya, Abuja, na tsawon shekara guda ba tare da albashi ba.

An saka shi a jerin wadanda majalisar za ta rika sanya wa ido na tsawon shekaru biyar, kuma an haramta masa karin matsayi na shekaru biyar.

Zargin da ake yi masa ya samo asali ne daga wata kara mai lamba FHC/ABJ/CR/184/2021, inda ya yanke hukunci kan wata bukata ba tare da sauraron bangarorin da ke karar ba.

Kara karanta wannan

Portable: Bayan zayyano laifuffukansa, kotu ta tura fitaccen mawaki gidan kaso

Don haka, NJC ta ce ya karya dokoki na 3.1 da 3.3 na kundin da’ar alkalan Najeriya na 2016, kamar yadda Punch ta ruwaito.

3. An dakatar da Justice Aminu Baffa

Shi ma Justice Aminu Baffa Aliyu na babbar kotun tarayya, a Zamfara, an dakatar da shi na shekara guda ba tare da albashi ba.

Hakazalika, an sanya shi a jerin wadanda za a sanya wa ido na tsawon shekaru uku, kuma ba zai iya samun karin girma a cikin shekarun ba.

An same shi da laifin rashin da’a a wata shari'a mai lamba FHC/GS/CS/30/2021, wadda aka yi tsakanin gwamnatin jihar Zamfara da hukumar EFCC.

An ce Aminu ya bayar da umarni da ya hana hukumomin tsaro aiwatar da aikinsu na doka, tare da watsi da tsarin bin hukuncin da aka riga aka yanke.

NJC ta dakatar da wasu alkalai 3 tare da albashinsu na tsawon shekara 1
Justice Jane E. Inyang (Hagu) | Justice Inyang Ekwo (Dama). Hoto: @njcNig
Source: Twitter

NJC ta kori shugaban alkalan jihar Taraba

A wani labarin, mun ruwaito cewa, majalisar Alkalan Najeriya (NJC) ta dakatar da alkalin alkalan jihar Taraba, Mai shari’a F.B. Andetur, tare da umarnin ritayar dole daga aiki.

Kara karanta wannan

'Ya aikata laifuffuka 9': Kotu ta yanke wa matashi hukuncin ɗaurin shekaru 63

An dauki matakin ne bayan an gano cewa Andetur ya karya doka ta jinkirta yanke hukunci har na tsawon wata 30 bayan kammala shari’a.

NJC ta umurce shi da ya mika ragamar aiki ga alkali mafi girma a jihar, tare da bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da binciken wasu alkalan kan laifuffuka daban daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com