Mummunar Gobara Ta Tashi a Fitacciyar Kasuwar Wayoyi, Ta Kone Shaguna Masu Yawa
- Wata mummunar gobara da ta tashi a kasuwar Challenge da ke Ilorin da misalin ƙarfe 9:06 na dare, ta babbake akalla rumfuna 10 na wayar salula
- Hukumar kashe gobara ta Kwara ta ce haduwar layukan wutar lantarki ne ya haddasa gobarar da ta shafi shagunan saida wa da gyaran wayoyi
- 'Yan kasuwa sun yaba wa hukumar kashe gobara saboda daukin gaggawar da ta kai yayin da aka roki gwamnati ta tallafa wa wadanda abin ya shafa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kwara - Mummunar gobara ta tashi a daren Laraba a shahararriyar kasuwar wayoyi da ke cikin kasuwar Challenge a Ilorin, jihar Kwara, inda ta yi barna mai yawa.
Rahotanni sun bayyana cewa wutar ta tashi ne da misalin ƙarfe 9:06 na dare, inda ake zargin hadewar layukan wutar lantarki ne ya haddasa gobarar.

Source: Facebook
Gobara ta tashi a kasuwa a jihar Kwara
Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa kasuwar na da akalla shaguna 120, rumfunan saida kaya guda 80 da kuma kananun akwatunan sayar da wayoyi da dama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da 'yan kasuwa da wadanda ke zaune a kusa da kasuwar suka shiga dimuwa a daren Alhamis, rahoto ya nuna cewa rumfuna 10 ne wutar ta shafa.
Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle ya bayyana cewa gobarar ta shafi shagunan sayar da wayoyi da na gyaran wayoyin.
'Yan kwana kwana sun hana yaduwar wutar
Hassan Adekunle ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, yana mai cewa:
“Jami’anmu sun isa wurin cikin gaggawa inda suka iske shaguna da dama na ci da wuta. Kasuwar na da shaguna fiye da 120 da rumfuna 80 da kuma wuraren zama da yawa.
“Saboda saurin kai dauki, amfani da kwarewa da dabarun aikin kashe gobara, jami’anmu sun yi nasarar dakile yaduwar gobarar, inda suka takaita illarta zuwa rumfuna 10 kacal.
“Binciken farko ya nuna cewa haduwar layukan wayar lantarki ne ya haddasa gobarar, kuma mafi yawan wuraren da wutar ta shafa na saida waya ne da gyaranta.”
An yaba wa kokarin hukumar kwana kwana
Hassan Adekunle ya kara da cewa ‘yan kasuwa da masu ruwa da tsaki a kasuwar sun yaba da yadda hukumar ta kai dauki cikin hanzari tare da hana yaduwar wutar.
Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar, Falade Olumuyiwa, ya bayyana tausayinsa ga shugabannin kasuwar da ‘yan kasuwar da abin ya shafa.
Falade Olumuyiwa ya yi addu’ar Allah ya mayar da dukkanin asarar da aka tafka cikin sauki, ya kuma ba wadanda abin ya shafa hakurin rashinsu, inji rahoton Tribune.

Source: Twitter
An roki gwamnati ta kai wa 'yan kasuwar dauki
Shugaban kwamitin amintattu na kasuwar, Musa Abdulateef, ya ce har yanzu 'yan kasuwar na cikin dimuwa kan tashin wannan gobara.
Ya roki gwamnatin jihar Kwara karkashin Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq da sauran masu hannu da shuni da su taimaka wa wadanda abin ya shafa.
Wani daga cikin masu shagunan da abin ya shafa ya bayyana wa manema labarai cewa lamarin ya girgiza shi matuka, yana mai rokon gwamnati ta taimaka musu wajen farfado da kasuwancinsu.
Gobara ta kashe mutum 7, ta lalata miliyoyi
A wani labari, mun ruwaito cewa, hukumar kashe gobara ta Kano ta ce ta ceci rayukan mutane 7 da dukiyoyi kimanin Naira miliyan 180 daga gobara 77 a watan Fabrairu, 2025.
Rahotanni sun bayyana cewa gobarar ta yi sanadin mutuwa da asarar kadarori da darajarsu ta kai sama da Naira miliyan 50 a fadin jihar.
Daga cikin gobarar da aka fi tunawa da su akwai ta Bunkure, wuta ta kone gidaje, dabbobi, da rumbunan ajiye hatsi, lamarin da ya tayar da hankali.
Asali: Legit.ng


