Tinubu Na Katsalandan a Ayyukan EFCC? Shugaban Hukumar Ya Tsage Gaskiya

Tinubu Na Katsalandan a Ayyukan EFCC? Shugaban Hukumar Ya Tsage Gaskiya

  • Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya yi magana kan zargin cewa Shugaba Bola Tinubu na yi musu katsalandan
  • Ola Olukoyede ya musanta cewa shugaban ƙasan yana amfani da hukumar wajen muzgunawa ƴan jam'iyyun adawa
  • Shugaban na EFCC ya bayyana cewa shugaban ƙasan ya fi mayar da hankali wajen ganin shugabannin ma'aikatu sun sauke nauyin da aka ɗora musu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya yi magana kan zargin Shugaba Bola Tinubu na katsalandan kan ayyukanta.

Ola Olukoyede ya ƙaryata zargin da ke cewa Shugaba Bola Tinubu yana amfani da hukumar don gallazawa mambobin jam’iyyun adawa.

Ola Olukoyede, Bola Tinubu
Shugaban EFCC ya ce Tinubu bai yi musu katsalandan Hoto: @DOlusegun, @OfficialEFCC
Source: Twitter

Shugaban na EFCC ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a shirin Politics Today na tashar Channels Tv a ranar Laraba, 30 ga watan Afirilun 2025.

Kara karanta wannan

Okowa: EFCC ta tabo batun binciken abokin takarar Atiku bayan komawa APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me shugaban EFCC ya ce kan Tinubu?

Olukoyede ya bayyana zargin a matsayin wani makirci don karkatar da hankalin Shugaba Tinubu daga kyakkyawan aikin da yake yi.

A cewarsa, babban abin da Shugaba Tinubu ke mayar da hankali a kai shi ne, yadda shugabannin manyan ma’aikatu da hukumomin gwamnati ke sauke nauyin da aka ɗora musu.

"Ina ganin ya kamata ƴan Najeriya su yi godiya kan irin shugaban da muke da shi a wannan lokaci, kuma ina faɗi ne da gaske. Ba saboda ina kan wannan muƙamin ba ne."
"Duk wanda zai faɗi gaskiya, musamman waɗanda suke aiki tare da shugaban ƙasa, mambobin majalisar zartarwa ta tarayya, shugabannin hukumomi da ma'aikatu, duk lokacin da ka ga shugaban kasa, abin da yake nunawa shi ne 'Me ka yi?' 'Nawa ka dawo da shi?'”
"Mutumin nan ba shi da lokacin yin waɗannan abubuwan, mutane kawai suna ƙoƙarin karkatar da hankalin gwamnati, suna ƙoƙarin hana shugaban ƙasa ci gaba da aikinsa."

Kara karanta wannan

"Ɗan Arewa kaɗai," Dele Momodu ya faɗi wanda zai iya kayar da Shugaba Tinubu a 2027

"Duk wanda ke kusa da shi zai tabbatar maka da cewa baya son jin komai sai dai batun aiki da sakamako."

- Ola Olukoyede

Ola Olukoyede
Shugaban EFCC ya ce ana kokarin karkatar da hankalin Tinubu Hoto: @OfficialEFCC
Source: Facebook

Da yake mayar da martani kan zargin cewa EFCC na amfani da ƙarfinta wajen muzgunawa ƴan adawa, Olukoyede ya ce tarihin shari'o'in manyan mutane da hukumar ta gurfanar ya saɓawa wannan zargi.

Ya ƙara da cewa hukumar ta fi gurfanar da mambobin jam’iyyar APC mai mulki fiye da waɗanda ke cikin jam’iyyun adawa.

EFCC ta tabo batun bincikar Okowa

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya yi magana kan binciken tsohon gwamnan jihar Delta, Sanata Ifeanyi Okowa.

Ola Olukoyede ya bayyana cewa hukumar ba ta wanke tsohon gwamnan daga binciken da take masa ba kan zargin karkatar da kuɗin jihar.

Shugaban na EFCC ya bayyana cewa ana ci gaba da bincikar tsohon gwamnan wanda ya yi takarar mataimakin shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng