Okowa: EFCC Ta Tabo batun Binciken Abokin Takarar Atiku bayan Komawa APC

Okowa: EFCC Ta Tabo batun Binciken Abokin Takarar Atiku bayan Komawa APC

  • Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya yi magana kan binciken Ifeanyi Okowa
  • Ola Olukoyede ya bayyana cewa har yanzu ba a wanke tsohon gwamnan na jihar Delta ba, saɓanin rahotannin da ake yaɗawa
  • Ya kuma buƙaci ƴan Najeriya su ƙara haƙuri kan yadda hukumar ke gudanar da ayyukanta musamman binciken manyan ƴan siyasa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri kan ayyukan hukumar.

Ola Olukoyede ya buƙaci hakan ne yayin da hukumar ke fuskantar ƙaruwar matsin lamba dangane da jinkiri wajen gurfanar da shari’o’in cin hanci da rashawa na manyan mutane, ciki har da na masu fada a ji a siyasa da kuma na masu zamba.

Kara karanta wannan

Tinubu na katsalandan a ayyukan EFCC? Shugaban hukumar ya tsage gaskiya

EFCC ta yi magana kan binciken Ifeanyi Okowa
Shugaban EFCC ya ce ba a wanke Ifeanyi Okowa ba Hoto: EFCC Nigeria, Dr. Ifeanyi Okowa
Source: Facebook

Shugaban na hukumar EFCC ya buƙaci hakan ne yayin wata hira ta musamman da aka yi da shi a Channels Tva ranar Laraba, 30 ga watan Afirilun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙalubalen da hukumar EFCC ke fuskanta

Olukoyede ya kare yadda hukumar ke gudanar da ayyukanta, ya ce shari’o’in rashawa musamman waɗanda suka shafi manyan ƴan siyasa, suna da sarƙaƙiya sosai kuma ana yawan ɓata lokaci a kai ta hanyar amfani da dabarun shari’a.

"Mun gaji tsarin da cin hanci ke faɗa da masu bincikarsa, kuma yana yin hakan da cikakken ƙarfi na tasiri, dukiya da dabarun doka."
“Ba za mu yi gaggawa ba. Dole ne ƴan Najeriya su yi hakuri idan muna son samun hukunci na gaskiya da sakamako mai ɗorewa.”

- Ola Olukoyede

Me EFCC ta ce kan binciken Ifeanyi Okowa?

Ɗaya daga cikin shari’o’in da ke da tasiri a siyasa da ake sa ido a kai na da nasaba da tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, wanda ya kasance mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Okowa ya bayyana lokacin da Atiku zai fice daga jam'iyyar PDP

Shugaban EFCC
Olukoyede ya ce ana ci gaba da bincikar Okowa Hoto: EFCC Nigeria
Source: Facebook

Shugaban na EFCC ya tabbatar da cewa bincike kan lamarin Okowa har yanzu yana gudana.

"Ba a wanke shi ba. Na ga rahotanni da ke cewa hukumar EFCC ta wanke shi, wannan ba gaskiya ba ne. Har yanzu ana ci gaba da bincike a kai."

- Ola Olukoyede

Wannan bayani nasa na zuwa ne a daidai lokacin da jama’a ke ƙara nuna shakku game da ƙudirin hukumar EFCC na gurfanar da manyan ƴan siyasa da ke riƙe da muƙamai.

Okowa ya yi nadamar takara tare da Atiku

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa ya yi magana kan takarar da ya yi tare da Atiku Abubakar a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023.

Sanata Ifeanyi Okowa ya bayyana cewa ya yi nadamar zama ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na PDP.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ya yi nadamar yin takarar ne saboda hakan ya saɓa da muradun mutanensa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng