Bashir Ahmad ya Karyata Ikirarin Cewa Gwamnatin Buhari Ta ci Bashin $400bn

Bashir Ahmad ya Karyata Ikirarin Cewa Gwamnatin Buhari Ta ci Bashin $400bn

  • Hadimin Buhari ya bayyana damuwa kan yadda Sanata Adeola ya yi ikrarin bashin da Buhari ya tarawa Najeriya
  • Shugaba Buhari ya bar Najeriya da bashi, lamarin da ake yiwa kallon ya bata tattalin arzikin kasar a halin yanzu
  • Gwamnatin Tinubu na ci gaba da bayyana yadda take shirin gyara tattalin arzikin kasar ta hanyar cire tallafin kan kusan komai

Najeriya - Tsohon Hadimin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya karyata ikirarin da Sanata Solomon Adeola ya yi, inda ya ce gwamnatin Buhari ta karɓi bashi har dala biliyan 400 domin farfado da darajar Naira.

A wani tsokaci da ya yi a shafin sa na X (Twitter), Bashir Ahmad ya bayyana cewa wannan magana ba gaskiya ba ce kuma babu wani rahoto daga hukumomin gwamnati da ya tabbatar da hakan.

Buhari bai ci bashin kudaden msau yawa ba, Bashir Ahmad
Bashir Ahmad ya karyata batun cin bashin Buhari | Hoto: @OfficialAPC
Source: Facebook

Ya ce:

"Ina fatan wannan kuskuren harshe ne, amma ikirarin cewa gwamnatin Buhari ta karɓi bashi dala biliyan 400 don daidaita darajar Naira ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

'Ka dawo da komai da ke wurinka': Gwamna ya dakatar da Sarki a Adamawa

“Kamar yadda Hukumar Kula da Bashi (DMO) ta fitar, zuwa watan Mayun 2023, jimillar bashin Najeriya ya tsaya ne a dala biliyan 108.3."

Bashin da ake bin Najeriya a lokacin Buhari

A cewar Bashir Ahmad, daga cikin wannan adadi, akwai bashin waje da ya kasance dala biliyan 43.2.

Hakazalikam sai bashin cikin gida da ya kai naira tiriliyan 49.9, wanda ya kama dala biliyan 65.1 bisa sauyin farashin canjin wancan lokacin.

Bashir Ahmad ya ƙara da cewa daga lokacin da Shugaba Buhari ya hau mulki a 2015 zuwa lokacin da ya sauka a 2023, bashin Najeriya ya ƙaru da kimanin dala biliyan 44.5 ne kacal; ba ko kusa da dala biliyan 400 da aka ambata ba.

Ya kara da cewa:

"Yana da muhimmanci a fayyace cewa a cikin shekaru takwas na gwamnatin Buhari, an samu gagarumin ci gaba da ayyuka masu inganci kamar gina layin dogo, samar da sabbin jiragen kasa, ayyukan wutar lantarki, asibitoci, manyan tituna da gadoji a faɗin ƙasar nan."

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu ke gyara ɓarnar da Buhari ya yi na karɓar bashin $400bn saboda Naira

Ikrarin sanata Adeola

Rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa ya nuna cewa Sanata Adeola, yayin wata ganawa da manema labarai, ya bayyana cewa gwamnatin Buhari ta karɓi bashi har zuwa dala biliyan 400 don farfado da darajar Naira.

Masana tattalin arziki sun bayyana cewa ko da yake gwamnatin Buhari ta karɓi bashi da yawa, an yi amfani da yawancin kudaden wajen aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa da kuma ceto tattalin arzikin Najeriya a lokacin matsin lambar farashin man fetur da annobar COVID-19.

Sai dai, wasu na ganin yadda bashin ya ƙaru ya haifar da ƙarin nauyi a kan aljihun gwamnatin tarayya da kuma ƙalubale ga tattalin arzikin ƙasa.

A karshe, Bashir Ahmad ya shawarci 'yan siyasa da su rinka tabbatar da sahihancin bayanan da suke fitarwa ga jama'a, musamman idan ya shafi lamurra masu matuƙar muhimmanci kamar bashin ƙasa.

Tsarin Tinubu na gyara Najeriya

Idan baku manta ba, tun bayan hawansa mulki a watan Mayu 2023, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fara aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki domin farfado da tattalin arzikin Najeriya.

Kara karanta wannan

Bayan komawa APC, Gwamna ya fara cin karo da matsalar farko a gwamnatinsa

Daga cikin matakan da ya dauka akwai cire tallafin man fetur da sakin darajar Naira, da kuma kafa tsare-tsaren bunkasa zuba jari a fannonin noma, fasaha da makamashi.

Wadannan sauye-sauye sun haddasa tsadar rayuwa, amma gwamnatin ta ce ana kokarin rage radadin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng