Yadda Aka Kashe Tantirin Dan Bindiga a Hanyar Zuwa Tadi wajen Bazawarsa a Zamfara
- Faɗa kan mace ya jawo sanadiyyar halaka wani tantirin ɗan bindiga, Kachalla Namadi wanda ya addabi mutane a jihar Zamfara
- Wasu ƴan bindiga da ke saɓani da Kachalla Namadi kan wata bazawara ne suka yi masa kwanton ɓauna sannan suka hallaka shi
- Saɓanin su ne dai ya samu asali ne bayan Kachalla Namadi ya haƙiƙance cewa sai ya auri bazawarar wani ɗan bindiga da aka kashe
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Wani hatsabibin ɗan bindiga mai suna Kachalla Namadi, ya rasa ransa a hannun wasu ƴan bindiga da ba sa ga maciji da juna.
Ƴan bindigan da ake zargin na wata ƙungiya ne sun hallaka Kachalla Namadi ne a wani harin kwanton ɓauna da suka kai masa.

Source: Original
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka kashe Kachalla Namadi a Zamfara
Lamarin ya faru ne a ranar 11 ga watan Afirilu, 2025, a wani wuri kusa da ƙauyen Kangon Fara Mana, wanda ke gabashin garin Magami a cikin ƙaramar hukumar Gusau ta jihar Zamfara.
Majiyoyi sun bayyana cewa Kachalla Namadi na kan hanyarsa ta zuwa ziyartar wata bazawara a ƙauyen lokacin da harin ya auku.
Ana kyautata zaton bazawarar da zai ziyarta matar wani tsohon ɗan bindiga ne da ya mutu, kuma ana zargin cewa wasu daga cikin ƴan ƙungiyar da suka farmake shi sun nuna sha’awar auren ta.
Sai dai Kachalla Namadi ya nace cewa dole sai an ba shi ita a matsayin wacce zai aura.
Wannan matsin lamba da ya dinga yi kan matar ya haifar da rikici da ƙiyayya a tsakaninsa da ƴan bindigan, inda daga bisani ake zargin wasu daga cikin abokan gabar tasa suka shirya masa kwanton ɓauna.
Sun harbe shi kafin ya isa wurin bazawarar tasa, lamarin da ya yi sanadiyyar gamuwarsa da ajalinsa.
Kachalla Namadi ga addabi mutane a Zamfara
Kachalla Namadi ya kasance wani sanannen ɗan bindiga wanda yake a ƙauyen Madada da ke cikin yankin Dan Sadau a ƙaramar hukumar Maru.

Source: Twitter
Ya shahara wajen kai hare-hare da addabar al’umma a sassan jihar Zamfara da kewaye.
Haka kuma, an ruwaito cewa yana da fiye da yara 50 daga mata daban-daban da ya aura ko ya tilasta musu zama tare da shi.
Mutuwarsa na daga cikin jerin hare-haren da ke nuna rashin jituwa da rikice-rikice a tsakanin ƙungiyoyin ƴan bindiga da ke aiki a yankin Arewa maso Yamma.
Sojoji sun hallaka hatsabibin ɗan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka wani tantirin ɗan bindiga, Kachalla Bello Kaura a jihar Zamfara.
Dakarun sojojin na Operation Fansan Ƴamma sun hallaka ɗan bindigan ne a ƙauyen Goburawar Dawan Jiya.
Haziƙan dakarun sojojin sun hallaka Kachalla Bello Kaura ne tare da mayaƙansa a wani farmaki da suka kai a maɓoyarsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

