Gwamnati Ta Kafa Sababbin Dokoki a Filato saboda Kashe Kashe

Gwamnati Ta Kafa Sababbin Dokoki a Filato saboda Kashe Kashe

  • Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang, ya bayyana kaduwarsa kan sabon harin da aka kai a Zikwe da ke garin Bassa, aka kashe mata, maza da yara kanana
  • Ya sanar da sababbin dokoki da suka hada da haramta kiwo da daddare, hana jigilar shanu bayan karfe 7:00 na yamma da takaita zirga-zirgar babura
  • Gwamna Mutfwang ya bayyana cewa za a ba wadanda suka jikkata kulawar lafiya kyauta kuma an tura kayan agaji zuwa wuraren da abin ya shafa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Plateau - Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya bayyana alhini kan harin da aka kai kauyen Zikwe da ke karamar hukumar Bassa a daren Lahadi, 13 ga Afrilu.

Harin ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da jimamin rasa sama da rayuka 50 a wani mummunan hari da aka kai garin Bokkos a jihar, lamarin da ya jefa Filato cikin tashin hankali.

Kara karanta wannan

'Dan daba Dujal ya mika wuya bayan kashe mutane da dama a Kano da Jigawa

Caleb
Gwamnatin Filato ta kafa sababbin dokoki saboda hare hare. Hoto: The Government of Plateau State
Asali: Facebook

Gwamnan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ya fitar a X, ya bayyana harin a matsayin kisan gilla da ake kai wa jihar da gangan, yana mai cewa “Filato ba za ta rushe ba.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sababbin dokokin da aka kafa a Filato

Domin dakile faruwar irin wadannan hare-hare, Gwamna Mutfwang ya sanar da wasu sababbin matakai da za su fara aiki daga Laraba, 16 ga Afrilu.

Rahotanni sun nuna cewa cikin dokokin akwai haramta kiwon dabbobi da daddare a fadin jihar baki daya.

Haka kuma, gwamnati ta hana jigilar shanu bayan karfe 7:00 na yamma, sannan an takaita zirga-zirgar babura daga karfe 7:00 na yamma zuwa 6:00 na safe a fadin jihar.

Gwamnan ya ce cibiyoyin lafiya da ke yankunan da lamarin ya shafa za su rika bai wa wadanda suka jikkata kulawa kyauta, tare da tura kayan agaji domin tallafa wa wadanda abin ya shafa.

Kara karanta wannan

Karfin shugaban rikon Rivers zai ragu, majalisa ta kafa kwamitin lura da ayyukansa

Caleb
Gwamnan Filato ya ce za a kai kayan agaji wuraren da aka kai hari. Hoto: The Government of Plateau State
Asali: Facebook

Kiran gwamna ga sarakunan jihar Filato

Gwamna Mutfwang ya yi kira ga sarakunan gargajiya da shugabannin matasa da su kafa rundunonin sintiri tare da hadin gwiwar jami’an tsaro.

Ya bukaci su yi haka ne domin kare kauyuka da al’umma daga barazanar hare-haren da ake fama da su.

Ya ce:

“Dole mu hada kai domin kare filayenmu tare da tabbatar da bin doka,”

Gwamnan ya kara da cewa zai tabbatar da cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai an dawo da zaman lafiya a Filato.

A karshe, ya jajanta wa iyalan wadanda harin ya rutsa da su a Zikwe da Bokkos, yana mai cewa:

“Radadin da kuka shiga ya shafe mu. Za mu tashi tsaye, mu tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a Filato.”

Dan daba Dujal ya shiga hannun 'yan sanda

A wani rahoton, kun ji cewa kasurgumin dan daba da ya saba kashe mutane da sace sace a jihar Kano da aka fi sani da Abba Dujal ya mika wuya ga 'yan sanda.

Kara karanta wannan

Kisan mutum 54: Bincike ya jefo shakku a adadin wadanda aka hallaka a Filato

Abba Dujal ya ce ya kashe mutane a jihohin Kano da Jigawa tare da sace musu wayoyi da baura a lokuta mabambanta.

Kakakin 'yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce za a gudanar da bincike domin tabbatar da abin da Dujal ya fada.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng