'Dan Daba Dujal Ya Mika Wuya bayan Kashe Mutane da Dama a Kano da Jigawa

'Dan Daba Dujal Ya Mika Wuya bayan Kashe Mutane da Dama a Kano da Jigawa

  • Matashi dan shekara 20, Umar Auwal, ya mika kansa ga rundunar ‘yan sandan Kano tare da amsa laifin kashe mutane da dama a Kano da Jigawa
  • A cikin amsarsa, ya bayyana yadda ya kashe mutane a Sabon Gari da Kurna a jhar Kano da kuma Ringim a Jigawa, yana sace wayoyi da babura
  • Kwamishinan ‘yan sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori PhD, ya yi kira ga sauran masu laifi su tuba domin ba za su samu mafaka ba a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa wani matashi dan shekara 20 mai suna Umar Auwal wanda aka fi sani da 'Abba Dujal', ya mika kansa ga hukumomi.

Matashin ya mika wuya ne bayan dogon samamen da jami’an tsaro suka gudanar a wasu muhimman wurare na jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta kafa sababbin dokoki a Filato saboda kashe kashe

Sanda
Dan daba Dujal ya mika wuya ga 'yan sanda. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Facebook

Bayanin ya fito ne daga kakakin ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce Abba Dujal mazaunin karamar hukumar Wudil ne, kuma ya amsa aikata manyan laifuffuka da suka hada da kisan kai, fashi da makami da kuma satar babura da wayoyi.

Abba Dujal ya ce ya kashe mutane da dama

Abba Dujal ya bayyana cewa ya kashe wani mutum mai suna ‘Boka’ a unguwar Sabon Gari na Kano, inda ya sace wayar Infinix Hot 40i, ya kuma sayar da ita a kan N40,000.

Haka zalika ya bayyana yadda ya kashe wani mutum a Kurna, Kano, tare da sace wayar Samsung S26 da ya sayar a kan N160,000.

A Jigawa kuwa, ya ce ya kashe wani mutum a karamar hukumar Ringim tare da sace babur dinsa da ya sayar da shi a kan N300,000.

Dujal ya shafe shekara 7 bai yi sallah ba

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun sake tabargaza a Filato, sun kashe mutane kusan 50

Da ake yi masa tambayoyi a ofishin 'yan sanda, Abba Dujal ya ce yanzu haka ya shekara bakwai bai yi sallah ba.

Ya ce an saka shi a Islamiyya amma malamin ya dawo da shi gida saboda fitinar da yake yi a makarantar.

A fannin karatun boko kuma, Abba Dujal ya ce ya taba shiga firamare amma daga nan bai kara gaba ba.

Sanda
Kwamishinan 'yan sanda ya bukaci 'yan daba su mika wuya a Kano. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Asali: Twitter

Za a binciki Abba Dujal a Kano

Rundunar ta tabbatar da cewa a halin yanzu, an tsare wanda ake zargin a sashen binciken manyan laifuffuka na CID domin cigaba da bincike da kuma tabbatar da gaskiyar ikirarin da ya yi.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana jin dadinsa kan matakin da Dujal ya dauka na mika wuya.

CP Bakori ya ce rundunar ‘yan sanda ba za ta lamunci ta’addanci ba, kuma za ta yi duk mai yiwuwa wajen dakile laifuffuka a jihar.

Kara karanta wannan

Portable: Ƴan sanda sun kama fitaccen mawakin Najeriya, an ji laifin da ya aikata

Jami'an tsaro sun yi zama a Filato

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Filato ta yi zama na musamman domin duba hanyoyin magance kashe kashe.

Gwamnan jihar, sojoji, 'yan sanda, shugabannin kananan hukumomi sun tattauna a gidan gwamnati domin shawo kan lamarin.

Hakan na zuwa ne bayan wasu 'yan bindiga sun kai hari karamar hukumar Bassa sun kashe mutane kimanin 50 a dare daya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng