Ana Jimamin Rikicin Plateau, 'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane a Benue

Ana Jimamin Rikicin Plateau, 'Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane a Benue

  • Ƴan bindiga waɗanda ake zargin miyagun makiyaya ne, sun kai harin ta'addanci a ƙaramar hukumar Otukpo ta jihar Benue
  • Miyagun ƴan bindigan sun kai harin ne da yammacin Talata, 15 ga watan Afirilun 2025, suka kashe mutum bakwai har lahira
  • Harin wanda ƴan bindigan suka kai a ƙauyen Otobi, ya yi sanadiyyar raunata mutane masu yawa da ba a san adadinsu ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Wasu ƴan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kai hari a ƙauyen Otobi da ke yankin Akpa a jihar Benue.

Ƴan bindigan sun kai harin ne a yankin wanda yake a ƙaramar hukumar Otukpo ta jihar Benue da yammacin ranar Talata, 15 ga watan Afirilun 2025.

'Yan bindiga sun kai hari a Plateau
'Yan bindiga sun kashe mutum 7 a Plateau Hoto: Rev. Fr. Hyacinth Iormem Alia
Asali: Twitter

Tashar Channels tv ta ce an tabbatar da rasuwar mutane bakwai sakamakon harin da ƴan bindigan suka kai a ƙauyen.

Kara karanta wannan

Tsohon ciyaman da kansila sun rasu da mutanen gari suka yi gaba da gaba da ƴan bindiga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka kai hari a Benue

Ƴan bindigan sun kuma raunata wasu mutane da dama waɗanda ba a tantance adadinsu ba, yayin da kuma suka ƙona gidaje masu yawa, cewar rahoton jaridar The Punch.

Wani ganau da ya shiga cikin tawagar tsaro da ta je kai ɗauki ya tabbatar da cewa ƴan bindigan da ake zargi makiyaya ne, sun kashe mutane bakwai daga cikin mazauna yankin.

Ya ƙara da cewa har yanzu tawagar tsaron na ci gaba da bincike don gano waɗanda suka jikkata.

A cewar ɗan majalisar da ke wakiltar mazabar Otukpo-Akpa a majalisar dokokin jihar Benue, Kennedy Angbo, harin ya fara ne kusan ƙarfe 5:30 na yamma a ranar Talata.

Ɗan majalisar, wanda mazaunin yankin Akpa ne, ya bayyana cewa har yanzu ba a san adadin waɗanda suka mutu ba, amma mutane da dama sun tsere daga yankin sakamakon harin.

Wani mazaunin ƙauyen Otobi, mai suna Edwin Emma, ya ce akwai fargabar cewa mutane da dama sun mutu, inda ya yi kira g gwamnati da hukumomin tsaro da su kawo musu ɗauki.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hare hare a Zamfara, sun tafka barna mai yawa

“Muna fuskantar hari daga makiyaya a Otobi, yanzu haka da na ke magana matata da ƴaƴana sun tsere daga ƙauyen saboda harin da ake kai mana, don Allah muna kira a kawo mana ɗauki."

- Wani mazaunin ƙauyen

Ƙauyen Otobi wanda ke ɗauke da babbar madatsar ruwa ta ma’aikatar ruwa ta tarayya, ya fuskanci hare-haren ƴan bindiga har sau biyu a cikin watan Afirilu.

Ba a ji ta bakin ƴan sandan Benue ba

'Yan bindiga sun yi ta'asa a Benue
'Yan bindiga sun.kashe mutane a Benue Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Rundunar ƴan sanda ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba har zuwa lokacin da aka kammala haɗa wannan rahoton.

A jihar Plateau da ke makwabtaka da Benue a yankin Arewa ta Tsakiya, fiye da mutane 100 aka kashe cikin makonni biyu da suka gabata a sakamakon hare-haren da wasu mahara suka kai.

Ƴan bindiga sun farmaki wurin ibada

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai farmaki a wani wurin ibada da ke jihar Kogi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bude wuta kan jami'an tsaro, an samu asarar rayuka

Ƴan bindigan sun kai farmakin ne a wani tsauni yayin da mabiya addinin Kirista ke gudanar da ibadar dare a ƙaramar hukumar Lokoja.

Ƴan bindigan a yayin harin, sun yi awon gaba da mutane masu yawa waɗanda ba san adadinsu ba zuwa cikin daji.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng