Gwamna Alia Ya Ciri Tuta a Arewa, Ya ba Ma'aikatan Jiharsa Hutun Kwanaki 3

Gwamna Alia Ya Ciri Tuta a Arewa, Ya ba Ma'aikatan Jiharsa Hutun Kwanaki 3

  • Gwamnatin jihar Benue ta ware Alhamis, Juma’a da Litinin a matsayin ranakun hutu ga ma'aikatan gwamnati domin bukukuwan Easter
  • Sakataren gwamnatin jihar, Serumun Aber ya bayyana cewa za a rufe dukkanin ofisoshi, ma’aikatu da hukumomi a wadannan kwanaki
  • Gwamna Alia ya bukaci jama’a su yi amfani da wannan lokaci don tsarkake ruhu, addu’a da sadaukarwa, sannan su dawo da aiki ranar Talata

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Benue - Gwamnatin jihar Benue ta ware kwanaki uku a matsayin ranakun hutun aiki ga ma’aikatan gwamnati domin bukukuwan Easter.

Wannan sanarwa ta fito ne daga sakataren gwamnatin jihar, Serumun Aber, a ranar Talata, 15 watan Afrilun 2025.

Gwamnatin Benue ta ba ma'aikata hutun Easter na kwanaki 3
Gwamnan jihar Benue, Rev. Fr. Dr. Hyacinth Iormem Alia. Hoto: @benuestategovt
Asali: Twitter

Gwamnatin Benue ta ba da hutun kwanaki 3

Jaridar Punch ta rahoto Serumun Aber a cikin sanarwar yana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Gwamnan Benue, Reverend Fr. Dr. Hyacinth Iormem Alia, ya ayyana Alhamis, Juma’a da Litinin a matsayin ranakun hutu na aiki ga dukkan ma’aikatan gwamnati a fadin jihar.

Kara karanta wannan

Bayan kashe mutane 54 a jihar Filato, Tinubu ya fadawa gwamna abin da zai yi

"Mai girma gwamna ya dauki wannan matakin ne domin nuna muhimmancin bukukuwan 'Easter Triduum' ga al’ummar Kirista a jihar Benue."

Sanarwar ta kara da cewa wannan mataki ya dace da bukatar bai wa ma’aikata dama su yi shagulgula da ibadun Easter Triduum ba tare da takura ba.

A cewar gwamnatin Benuwa, Kiristoci a fadin duniya na amfani da ibadun Easter Triduum a matsayin lokaci na tsarkake ruhi da sada zumunci.

Easter: Lokutan rufe ofisoshi a jihar Benue

Sanarwar ta yi magana kan lokacin da za a rufe ofisoshi, inda Serumun Aber ya ce:

"Za a rufe dukkanin ofisoshin gwamnati, ma'aikatu, sassa da hukumomi (MDAs) a wadannan kwanaki uku na hutu.
"Gwamnati na fatan jama’a za su yi amfani da wannan dama domin samun hutu, da kuma kasancewa cikin iyalai da masoya a wannan lokaci mai muhimmanci."

Gwamna Alia ya kuma tura sakon fatan alheri ga dukkanin Kiristoci da ke Benue da ma wajen jihar, inda ya yi addu’ar cewa bukukuwan Easter za su kawo farin ciki, zaman lafiya da tsarkake zukatan mutane.

Kara karanta wannan

Dakatar da Fubara: Mata sun cika tituna a Rivers suna zanga zanga

Easter: An fadi ranar komawa aiki a Benue

Sanarwar ta cigaba da cewa:

"Allah ya sa mu kammala wadannan bukukuwa cike da kwarin gwiwar riko da gaskiya, burin yin hidima ga mutane da kuma azamar kawo ci gaba a jihar Benue."

An bukaci al’umma su yi amfani da wannan lokaci wajen karfafa kyawawan dabi’u na hakuri, juriya da taimakon juna domin samar da kyakkyawar al’umma da ci gaba mai dorewa.

A ƙarshe, gwamnati ta bukaci ma’aikata su koma bakin aiki ranar Talata bayan hutu, tare da kama aiki cikin ƙwarin gwiwa domin cigaban jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.