Sanata Ndume bai Gaji ba, Ya Sake ba Shugaba Tinubu Muhimmiyar Shawara
- Sanata Mohammed Ali Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu ya ba da sabuwar shawara ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
- Ali Ndume ya yi kira gaTinubu da ya magance matsalar hauhawar farashin kayayyaki da rashin aikin yi da ake fama da su
- Sanatan ya kuma ba gwamnonin jihohin Najeriya shawara su yi koyi da takwaransu Borno wajen inganta aikin noma
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Sanata Ali Ndume ya fito ya sake ba da shawara ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Sanata Ali Ndume ya yi kira ga Tinubu da tawagarsa ta tattalin arziƙi kan su ɗauki matakan gaggawa domin shawo kan hauhawar farashi da rashin aikin yi da ke ƙara ta’azzara a Najeriya.

Asali: Twitter
Jaridar Vanguard ta ce Sanata Ndume ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Talata, 15 ga watan Afirilun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ndume ya jaddada cewa ɗaukar waɗannan matakai na da matuƙar muhimmanci domin ƴan Najeriya su amfana da cikakken sauyin da gwamnati ke yi.
Sanata Ali Ndume ya yabawa Bola Tinubu
Sanatan ya kuma yabawa shugaban ƙasa bisa ayyana dokar ta-baci kan batun tsaron abinci, inda ya nuna cewa matakin ya dace.
“Dole ne gwamnatin tarayya ta mayar da hankali kan yawan hauhawar farashi, ta nemo hanyar rage shi. Dole kuma ta tabbatar da daidaiton darajar Naira a kan Dala, musamman ganin cewa muna dogaro ne da kayan da aka shigo da su daga waje."
- Sanata Ali Ndume
Wace shawara Ndume ya ba Tinubu?
Ya shawarci gwamnatin Tinubu da ta yi cikakken amfani da damar da ke cikin shigar Najeriya a ƙungiyar tattalin arziƙin BRICS, wadda ta haɗa ƙasashen Brazil, Rasha, Indiya, China da Afirka ta Kudu.
Ndume ya nuna cewa Najeriya na iya cin gajiyar ciniki da sauran kuɗaɗe kamar Yuan na China maimakon dogaro da Dalar Amurka kaɗai.
Sanata Ndume ya kuma ba da shawarar kafa wani sashe da za a kira 'ma’aikatar inganta ayyukan gwamnati' a ofishin sakataren gwamnatin tarayya (SGF).
Ya bayyana cewa wannan sabuwar ma'aikatar za ta zama mai lura da tabbatar da cewa ma’aikatu, hukumomi da sassan gwamnati, na bin tsari wajen aiwatar da kasafin kuɗi.

Asali: Twitter
Ndume ya magantu kan samar da abinci
Ndume ya jaddada muhimmancin ƙara yawan amfanin gona domin rage farashin kayayyaki a kasuwa, tare da buƙatar gwamnonin jihohi su yi koyi da gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum.
Ya yaba da matakin Zulum na ayyana dokar ta-baci kan abinci da kuma samar da dubban injinan noman zamani, kayan ban ruwa da kuma takin zamani cikin farashi mai rangwame ga manoma.
Ndume ya kuma shawarci Shugaba Tinubu da ya sanya irin wannan dokar ta-ɓaci a fannin tattalin arziƙi da tsaron ƙasa, a matsayin wata hanya ta bunƙasa ci gaban ƙasa baki ɗaya.
Shugaban majalisa ya godewa Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ya yaba da halascin da Shugaba Bola Tinubu ya yi masa a siyasance.
Abbas Tajudeen ya bayyana cewa shugaban ƙasan ya goya masa baya a lokacin da yake neman kujerar shugabancin majalisar wakilai.
Shugaban majalisar ya ce duk da sunayen da aka gabatarwa shugaban ƙasan, ya tsaya tsayin daka domin ganin cewa ya samu muƙami
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng