Alaƙa Ta Fara Gyaruwa, Tinubu Zai Tura Tagawa Nijar domin Isar da Saƙonsa ga Tchiani

Alaƙa Ta Fara Gyaruwa, Tinubu Zai Tura Tagawa Nijar domin Isar da Saƙonsa ga Tchiani

  • Gwamnatin Najeriya za ta tura ministan harkokin waje, Yusuf Maitama Tuggar, zuwa Jamhuriyar Nijar domin isar da sakon Bola Tinubu
  • Tun da Janar Abdourahamane Tchiani ya kifar da Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023, alakar da ke tsakanin Najeriya da Nijar ta tabarbare
  • Ziyarar na zuwa ne bayan rikicin juyin mulkin, Najeriya na kokarin farfado da dangantaka da hadin gwiwar tsaro da kasuwanci da makwabciyarta
  • Najeriya na fatan kulla sababbin yarjejeniyoyi, tare da karfafa tsaro, farfado da cinikayya da kuma dangantaka ta juna tsakanin al’ummominsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - A wata muhimmiyar ziyara ta diflomasiyya domin dawo da amana da hadin kai, Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar, zai kai ziyara Jamhuriyar Nijar.

Yusuf M. Tuggar zai mika sako na musamman daga Bola Tinubu ga Janar Abdourahamane Tchiani a ranar Laraba, 16 ga Afrilu, 2025.

Kara karanta wannan

Karfin shugaban rikon Rivers zai ragu, majalisa ta kafa kwamitin lura da ayyukansa

Tawagar Tinubu za ta shiga Jamhuriyyar Nijar
Bola Tinubu zai tura tawaga ta musamman zuwa Nijar a gobe Laraba. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Muhammad Badamasi.
Asali: Facebook

Musabbabin ziyarar tawagar Tinubu zuwa Nijar

Ziyarar na nuna wani sabon salo a dangantakar Najeriya da Nijar, bayan rikicin juyin mulkin Yulin 2023 da ya dagula huldar kasashen biyu, cewar Zagazola Makama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tuggar zai tattauna da ministan harkokin wajen Nijar kan batutuwa masu muhimmanci irin su tsaro, kasuwanci, ci gaba da hadin gwiwar iyaka.

Ziyarar na zuwa ne a lokacin da yankin ke fuskantar sauye-sauye bayan ficewar Nijar, Mali da Burkina Faso daga ECOWAS.

Tattaunawar Najeriya da Nijar na nuni da yunkurin sabunta dangantaka da gina wata sabuwar fahimta bisa moriyar juna da mutunta juna.

Tawagar Najeriya za ta kunshi manyan jami’an diflomasiyya, masu ba da shawara da jami’an tsaro domin tsara sabon tsari na hadin gwiwa.

Ana sa ran zai gana da Shugaba Abdourahamane Tchiani domin tattauna yadda za a daidaita alakar diflomasiyya ta doka da tsarin dindindin.

A cewar wata majiya daga ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, ziyarar na da nufin karfafa fahimta da gina dangantaka mai dorewa da Nijar.

Kara karanta wannan

Rigima ta ɓarke a ofishin jam'iyyar APC, an tarwatsa taron naɗa sabon ɗan takara

Ziyarar na nuni da jajircewar Shugaba Tinubu wajen dawo da Nijar cikin tsarin zaman lafiya da hadin gwiwa a yammacin Afirka.

Tawagar Tinubu za ta shiga Nijar
Bola Tinubu zai tura tawaga mai ƙarfi Nijar yayin da ta yi tsami. Hoto: Federal Ministry of Foreign Affairs.
Asali: Twitter

Abubuwan ci gaba da ziyarar za ta samar

Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya na fatan irin wadannan dabaru za su taimaka wajen kwantar da tarzoma a Nijar ba tare da amfani da soja kawai ba.

Najeriya da Nijar na da mahimman hanyoyin ciniki, musamman daga jihohin Arewa zuwa yankunan Zinder da Maradi a Nijar.

Rikicin tsaro da rufe iyakoki ya durkusar da harkokin kasuwanci, yana cutar da ‘yan kasuwa da dama masu dogaro da cinikayya tsakanin kasashen biyu.

Ana fatan ziyarar za ta kai ga bude kasuwannin iyaka, hadin gwiwar sintirin tsaro da kuma sabunta manyan ayyukan ci gaba na iyaka.

Ziyarar ta nuna yadda Najeriya ke kokarin kafa sabuwar alakar tsaro da tattalin arziki, tare da hada kai da Nijar a wajen ECOWAS.

Tawagar ministan za ta mika shawarwari ga gwamnati Nijar kan tsaron iyaka, farfado da tattalin arziki da diflomasiyya ta al’umma.

Kara karanta wannan

Abin ya fara damun Tinubu, an 'gano' shirinsa kan ƴan APC da ke son komawa SDP

Nijar ta ayyana Hausa a matsayin harshen kasa

Mun ba ku labarin cewa gwamnatin sojan Nijar ta ayyana Hausa a matsayin harshen kasa, tare da cire Faransanci wanda ya samo asali daga mulkin mallaka.

Rahotanni suka ce Hausa ta riga ta zama gama gari a Nijar, musamman a Zinder, Maradi da Tahoua, yayin da kashi 13% kacal ke jin harshen Faransanci.

Nijar ta fice daga tasirin Faransa, ta kori sojojinta, ta canja sunayen tituna, tare da shiga sahun kasashe irinsu Mali.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng