Bayan Kashe Mutane kusan 50, Gwamnan Plateau Ya Fito Ya Nemi Alfarma

Bayan Kashe Mutane kusan 50, Gwamnan Plateau Ya Fito Ya Nemi Alfarma

  • Gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang ya nuna takaicinsa kan hare-haren ta'addanci da aka kai kan bayin Allah a jihar
  • Caleb Mutfwang ya nemi afuwar mutanen ƙaramar hukumar Bassa gaanwar da gwamnati da hukumomin tsaro suka yi wajen kare rayukansu da dukiyoyinsu
  • Ya buƙaci mutanen yankin da ka da gwiwoyinsu su yi sanyi wajen ƙoƙarin da suke yi na kare kansu
  • Gwamnan wanda ya je ziyarar gani da ido inda aka kai harin, ya kuma buƙaci jama'a da su ci gaba da ba da haɗin ga hukumomin tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang ya nemi afuwa kan kashe-kashen da aka gudanar a jihar.

Gwamna Mutfwang ya nemi afuwar ne daga wajen al’ummar ƙaramar hukumar Bassa kan gazawar gwamnati da hukumomin tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyi.

Kara karanta wannan

"Kai ne ka jawo": Atiku ya fadi alakar Tinubu da kisan gillar mutane 54 a Filato

Gwamna Caleb Mutfwang
Gwamna Mutfwang ya nemi afuwa kan kashe-kashe a jihar Hoto: Caleb Mutfwang
Asali: Facebook

Gwamnan Mutfwang ya bayyana hakan ne a ranar Talata a fadar Sarkin Miango, wanda shi ne babban basaraken al’ummar Miango a jihar, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kashe mutane 51 a safiyar ranar Litinin a garin Zikke da ke cikin ƙaramar hukumar Bassa, inda aka ƙona gidaje tare da raba mutane da muhallansu.

Gwamnan Plateau ya ba da haƙurin kashe-kashe

Lamarin na zuwa ne kusan makonni biyu bayan makamancin irin harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a ƙaramar Hukumar Bokkos.

Ƙasa da kwana guda bayan harin na baya-bayan nan, Gwamna Mutfwang ya ba da haƙuri saboda rashin iya kare rayukan mutane da gwamnati ta yi, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Ya buƙaci jama'a da ka da su gaji da ƙoƙarin da suke yi na kare yankunansu, tare da bada haɗin kai ga hukumomin tsaro ta hanyar bayar da muhimman bayanai domin taimakawa wajen gano masu aikata laifuka da kuma fallasa dabarunsu.

Kara karanta wannan

Bayan gargadin Tinubu kan harin Filato, gwamna, sojoji da 'yan Sanda sun yi zama

Gwamna Mutfwang ya je yin jaje

Gwamna Caleb Mutfwang
Gwamnan Mutfwang ya ba da hakuri kan kashe-kashe a Plateau Hoto: Caleb Mutfwang
Asali: Facebook

Gwamna Mutfwang, tare da manyan jami’an tsaro da mambobin majalisar zartarwar jihar, sun ziyarci garin Zikke domin jajantawa al’umma bisa kisan mutane fiye da 50 a harin da aka kai a ranar Litinin.

Mai martaba Sarkin ƙasar Irigwe, Ronku Aka, wanda shi ne Brangwe na Irigwe, ya buƙaci gwamnati da ta taimaka wa al’ummomin yankin ta hanyar samar da ababen more rayuwa.

Gwamnan da tawagarsa sun kuma ziyarci wasu daga cikin iyalan da suka rasa ƴan uwansu a harin.

Kwankwaso ya yi alhini kan rikicin Plateau

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP a zaɓen 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, ya nuna takaicinsa kan kashe-kashen da ake yi a jihar Plateau.

Kwankwaso ya yi kira da babbar murya ga hukumomi su ɗauki matakan da za su taimaka wajenn cafke masu hannu a rikicin tare da tabbatar da cewa sun fuskanci hukunci.

Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya kuma jajantawa mutanen ƙauyuka uku na ƙaramar hukumar Bassa kan ɓarnar da maharan suka yi musu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng