Sarakunan Arewa Sun Hadu a Borno domin Taro kan Matsalar Tsaro
- Majalisar Sarakunan Arewa ta gudanar da taron gaggawa a Maiduguri domin tattauna matsalar tsaro a yankin Arewa
- Taron na gudana ne a daidai lokacin da ake fuskantar hare-kungiyar haren Boko Haram da ISWAP a Jihar Borno da kewaye
- Sarakuna, jami’an tsaro da manyan jami’an gwamnati sun halarci taron domin lalubo mafita ga kalubalen tsaro a Arewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa (NTRC) ta gudanar da zaman kwamitinta na zartarwa karo na bakwai a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
Taron ya zo a dai-dai lokacin da matsalolin tsaro ke kara ta'azzara a yankin Arewa maso Gabas, musamman sababbin hare-haren da kungiyoyin Boko Haram da ISWAP ke kaiwa.

Asali: Twitter
A wani rahoto da tashar Talabijin ta NTA ta wallafa a X, an bayyana cewa taron zai mayar da hankali ne kan tsaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton VON ya tabbatar da cewa taken taron shi ne: "Karfafa tsaro a matsayin hanyar cigaban Arewa."
An gudanar da zaman ne a dakin taro na musamman, kuma ya tattara manyan sarakuna daga jihohin Arewa, jami’an tsaro da wakilan gwamnati.
Zulum ya koka kan matsalar tsaro
Taron na gudana ne yayin da Gwamna Babagana Umara Zulum ya yi gargadi da cewa Boko Haram na kara karfi a jihar Borno.
Haka zalika, Shehun Borno, Mai Martaba Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi, ya nuna matukar damuwa game da barazanar da matsalolin tsaro ke yi wa yankin Arewa maso Gabas.
Me ake sa ran za a tattauna a taron?
Kasancewar taron na zuwa me a lokacin da matsalolin Boko Haram da ISWAP ke neman rusa ci gaban da aka samu a yaki da ta’addanci, ana sa ran zai mayar da hankali kan matsalar.
Mai alfarma sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar III ne ya jagoranci tawagar taron kuma mai alfarma Shehun Borno ne ya tarbe su.
Cikin manyan sarakunan da suka taka baya wa Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar III akwai mai martaba sarkin Gummi, Lawal Hassan Gummi.

Asali: Twitter
Karin bayani kan taron majalisar sarakuna
Sarakunan Arewa suna taruwa lokaci bayan lokaci domin tattauna matsalolin da suka shafi yankinsu ko ma Najeriya baki daya a karkashin majalisarsu.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa sarakunan sun gudunar da taron majalisar na 6 ne a jihar Kaduna, inda suka tattauna muhimman abubuwa da suka shafi Arewa.
A wannan karon, sarakunan Arewa sun gabatar da taron ne a dakin taro na gidan gwamnatin Borno kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
Gwamnan Filato zai magance matsalar tsaro
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Filato ya yi alkwarin kawo sauyi a harkokin tsaro da suka addabi mutane da dama a jihar.

Kara karanta wannan
Tsohon dan majalisa ya dauki matakin kotu da Tinubu ya ayyana dokar ta baci a Ribas
Gwamnan ya bayyana haka ne bayan wani taron gaggawa da suka gudanar tare da sojoji da 'yan sanda kan tsaron jihar.
Caleb Mutfwang ya bayyana cewa kimanin mahara 100 ne suka kai hari karamar hukumar Bassa a daren Lahadi kuma sun kashe mutane da dama.
Asali: Legit.ng