'Ba Zan Yi Alkawarin Tsaronku ba': Gwamna ga Ƴan Siyasa Masu Zuwa Jiharsa
- Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya ce ba zai iya ba da tabbacin tsaron wanda ya kawo masu ziyara ba tare da izini ba
- Ya bayyana haka cikin wata sanarwa da kakakinsa Tersoo Kula ya fitar, ya bukaci bin tsarin ziyarar sansanonin ‘yan gudun hijira
- Alia ya ce yanzu haka yana ganawa da manyan jami’an gwamnati kan matsalolin jihar, kuma ba ya sa ran wani bako a ranar
- Gwamnan ya umurci hukumomin tsaro da jama’a su dauki sanarwar da muhimmanci, domin kiyaye doka da oda a jihar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Makurdi, Benue - Gwamnan jihar Benue, Rabaran Hyacinth Alia ya gargadi yan siyasa da ke shigowa jihar kan matsalar tsaro.
Gwamnan ya ce ba zai iya ba da tabbacin tsaro ga duk wanda ya kai ziyara jihar ba tare da saninsa ba.

Asali: Twitter
Gwamnan ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Kakakinsa, Tersoo Kula, ya fitar ranar Litinin 14 ga watan Afrilun 2025, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Peter Obi ya caccaki gwamnatin Benue
Hakan na zuwa bayan tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP, Peter Obi, ya bayyana takaicinsa kan yadda ake siyasantar da komai a Najeriya.
Obi ya bayyana hakan ne yayin da yake zargin gwamnatin Benue da hana shi kai ziyara ta jin ƙai zuwa sansanonin 'yan gudun hijira a jihar.
Sai dai a bangarenta, gwamnatin Benue ta kare kanta inda ta ce ba ta da masaniya kan ziyarar, saboda haka ba ta shirya bayar da tsaro ba.

Asali: Twitter
Gwamna ya gargadi masu shiga jiharsa babu izini
Alia ya gargadi duk wanda ke shirin ziyartar sansanonin ‘yan gudun hijira a jihar da ya nemi izini daga hukumar kula da gaggawa ta jihar.
Sanarwar ta ce:
“Gwamnan jihar Benue, Rabaran Hyacinth Alia, na sanar da jama’a cewa ba ya sa ran ganin wani bako na musamman yau a jihar.
Ya kuma gargadi ziyarce-ziyarce da ka iya rikidewa taron siyasa ba tare da izini ba, yana kira da a kiyaye doka da oda, cewar Vanguard.
Ya kara da cewa:
“Duk wanda ke tunanin zuwa Benue ba tare da sanin Gwamna ba, ya sake tunani, domin ba za a iya tabbatar da tsaronsa ba.
“Haka kuma, duk wanda ke son ziyartar sansanonin ‘yan gudun hijira dole ne ya samu izini daga hukumar BSEMA na jihar Benue.
“Muna rokon jami’an tsaro da al’umma su lura da wannan sanarwa tare da tabbatar da zaman lafiya da doka a fadin jihar.”
Gwamna ya ƙaryata shirin barin APC
Mun ba ku labarin cewa Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue ya musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa yana shirin tattara kayansa ya bar APC.
Rabaran Alia ya ce yana nan daram a APC sai ya cika alkawarin da ya ɗaukar wa Allah, kansa da al'umma na ceto Benue daga halin wayyo Allah.
Faston ya kuma musanta cewa alaƙa ta yi tsami tsakaninsa da sakataren gwamnatin tarayyya, George Akume, ya ce bai san da zancen ba.
Asali: Legit.ng