Ana Shirin Dakatar da Samar da Lantarki a Najeriya kan Bashin Naira Tiriliyan 4
- Kamfanonin samar da lantarki (GenCos) sun yi barazanar dakatar da aiki sakamakon bashin Naira tiriliyan 4 da suke bin gwamnatin tarayya
- Shugaban kwamitin GenCos, Kanal Sani Bello (mai ritaya), ya ce rashin biyan kuɗin da suke bi na hana su iya gudanar da ayyukansu yadda ya kamata
- Rahotanni sun nuna cewa bayan gwamnati, kamfanonin rarraba wuta da kwastomomi ma suna taka rawa wajen kawo cikan game da samar da wuta
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kamfanonin samar da wutar lantarki a Najeriya, wato GenCos, sun fitar da sabuwar sanarwa mai cike da gargadi cewa za su dakatar da ayyukansu.
Kamfanonin sun bayyana cewa za su dakatar da aiki idan har gwamnatin tarayya ta ci gaba da yin watsi da bashin Naira tiriliyan 4 da suke binta.

Asali: Getty Images
Daily Trust ta wallafa cewa shugaban kwamitin amintattun GenCos, Kanal Sani Bello (mai ritaya), ya ce sun ɗauki matakin ne saboda mawuyacin halin da bangaren samar da wuta ke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sani Bello ya ce kamfanonin sun kasa samun kudin da ya kamata a biya su, duk da cewa suna ci gaba da fadada ayyukansu.
Sanarwar ta ce GenCos na fuskantar babban koma baya saboda rashin biyan kuɗin da suke tsammanin samu.
Shirin dakatar da samar da wutar lantarki
Kanal Bello ya bayyana cewa rashin kudin da suke fama da shi na iya shafar samar da lantarki a Najeriya.
“Rashin biyan kuɗin da ya kamata a rika samu daga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki na iya shafar ayyukan da muke.
"Hakan barazana ne ga dukkan ayyukan samar da lantarki.”
Ya ce har ila yau, matsalar samun dalar Amurka don sayen kayan aikin gyara da sabunta injinan lantarki na ƙara dagula al’amura.

Kara karanta wannan
Portable: Ƴan sanda sun kama fitaccen mawakin Najeriya, an ji laifin da ya aikata
Ya bayyana haka ne kasancewar yawancin ayyuka a fannin suna buƙatar kuɗin kasashen waje, musamman Dalar Amurka.
Bello ya kara da cewa kudin da GenCos suka samu a 2024 bai wuce kashi 30% na kuɗin da ya kamata su samu ba, kuma babu abin da ya canja a 2025.

Asali: Getty Images
A karkashin haka ya ce lamarin na hana su biyan buƙatun kuɗi ga kuma sauran haraji da cajin da ke cinye musu kudi.
Me GenCos ke bukata a yanzu?
Kamfanonin sun bukaci a biya su dukkan kuɗin da suke bi, a sake tsara tsarin biyan kuɗi domin ba su fifiko da biyan cikakken kuɗinsu a kan lokaci.
Punch ta wallafa cewa ma'aikatar makamashi ta ce tana sane da halin da ake ciki kuma tana kokarin shawo kan matsalar.
Najeriya za ta hana shigo da kayan sola
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta fara shirye shirye domin hana shigo da kayan sola.

Kara karanta wannan
Zamfara: Bayan kisan ɗan bindiga, miyagu sun ɗauki fansa, sun ƙona masallacin Juma'a
Rahoton da Legit ta hana ya nuna cewa gwamnatin Najeriya za ta dauki matakin ne kokarin bunkasa harkar kere-kere a cikin gida.
Baya ga haka, an bayyana cewa matakin zai taimaki Najeriya wajen rage dogaro da amfani da kayayyakin kasashen waje.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng