Peter Obi Ya Fusata da Gwamnan Binuwai Ya Yi Masa Korar Kare

Peter Obi Ya Fusata da Gwamnan Binuwai Ya Yi Masa Korar Kare

  • Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP, Peter Obi, ya bayyana takaicinsa kan yadda ake siyasantar da komai a Najeriya
  • Obi ya bayyana hakan ne yayin da yake zargin gwamnatin Binuwai da hana shi kai ziyara ta jin ƙai zuwa sansanonin 'yan gudun hijira a jihar
  • A nata ɓangaren, gwamnatin Binuwai ta kare kanta inda ta ce ba ta da masaniya kan ziyarar, saboda haka ba ta shirya bayar da tsaro ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Benue –Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi, ya koka kan yadda aka hana shi ziyarartar 'yan gudun hijira a Binuwai

Obi ya kara da cewa yadda gwamnatin Binuwai ta hana shi zuwa aikin jin kai da ya saba ya nuna yadda abubuwan alheri ke kara komawa batun siyasa a kasar nan.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta fadi ainihin abin da ya kai Bola Tinubu Faransa

Hyacinth
Gwamnatin Binuwai ta fusata Obi Hoto: : @PeterObi/Dr Hyacinth lormem Alia
Asali: Twitter

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Litinin, Obi ya bayyana bakin cikinsa kan yadda gwamnatin Binuwai ta hana shi ziyartar sansanonin 'yan gudun hijira da asibitoci a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Peter Obi ya caccaki gwamnatin Binuwai

Punch ta ruwaito cewa Obi ya ce ziyarar da ya shirya, wadda aka tsara ta kasance ranar Lahadi, 14 ga Afrilu, na daga cikin ziyara ga jihohi biyu da ya fara daga Filato a ranar 13 ga Afrilu, sannan ya wuce Binuwai.

Ya bayyana cewa yayin da gwamnan Filato ya karɓe shi hannu bibbiyu, bai samu damar yin magana kai tsaye da gwamnan Binuwai, Fasto Hyacinth Alia ba.

Ya ce:

“Na yi ƙoƙari sau da dama in tuntubi gwamnan Binuwai kai tsaye amma hakan ya ci tura. Na samu nasarar tuntubar ADC dinsa, wanda ya shaida min cewa gwamnan na cikin muhimmin taro kuma zai kira ni kafin ƙarfe goma na dare a ranar.”

Kara karanta wannan

"Ni ma zan lallaɓa," Ndume ya faɗi dalilin da ya sa manyan ƴan siyasa ke zuwa wurin Buhari

Gwamnan Binuwai ya yi watsi da Obi

Obi ya bayyana cewa har zuwa yammacin Lahadi, 14 ga Afrilu, ba a sake jin komai daga gwamnan ba, sai ADC dinsa ya ce bai iya samun shi ba tsawon kwana uku.

Amma a hanyarsu ta zuwa Makurdi daga Jos da safe a ranar Litinin, Mista Obi ya ce jami’an tsaronsa sun samu wata sanarwa daga gwamnatin Binuwai da ke nuna cewa ba a maraba da ziyararsa.

Peter
Tsohon ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter Obi Hoto: Mr. Peter Obi
Asali: Facebook

Ya ce:

“Abin mamaki, yayin da muke tattaunawa da jami’an tsaro kan lamarin, ADC din gwamnan ya turo min sanarwar kai tsaye.”

Obi ya ce sanarwar na dauke da bayanan tafiyarsa da ya riga ya tura wa ADC da jami’an tsaro na jihar a ziyararsa ta jin kai, wacce ba ta dauke da wata manufa ta siyasa.

Ya ce:

“Wannan abu ne da na dade ina yi tun kafin in shiga siyasa. Har yanzu ina ci gaba da haka (aikin jin kai). A lokacin girgizar kasa a Haiti ma, na nemi izinin zuwa kasar domin taimako.”

Kara karanta wannan

"Na yi wa Allah alƙawari," Gwamna Alia ya yi magana da aka fara raɗe raɗin zai bar APC

Martanin gwamnatin Binuwai ga Obi

A cikin wata sanarwa da ya fitar a baya ranar Litinin, gwamna Alia ta bakin mai magana da yawunsa, Tersoo Kula, ya ce gwamnatin jihar ba ta da masaniya kan ziyarar.

Ya ce saboda haka, gwamnati ba za ta iya tabbatar da tsaron kowa ba, musamman ga wanda ya shigo jihar ba tare da sanarwa ba.

Ya ce:

“Ga duk wanda ke shirin zuwa jihar Binuwai ba tare da sanin gwamna ba, yana da muhimmanci ya sake nazari kan shirin, domin ba za mu iya tabbatar da tsaronsa ba.”

Gwamna Alia ya kuma ja hankalin jama’a da hukumomin tsaro da su guji duk wani taro da za a fassara da siyasa, yana mai kira da a ci gaba da zama lafiya da bin doka.

'Akwai talauci a Najeriya,' Obi

A baya, mun wallafa cewa Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, ya bayyana damuwarsa kan halin matsin rayuwa da talauci da al’ummar Najeriya ke fama da shi.

Kara karanta wannan

Akpabio ya fadi abin da ya sani kan yunkurin hallaka Sanata Natasha

Peter Obi ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 10 ga Afrilu, yayin taron kwamitin zartaswa na ƙasa (NEC) na LP da aka gudanar a otel ɗin Transcorp Hilton da ke Abuja.

Ya ce gwamnati a kowane mataki na da rawar da za ta taka wajen magance matsalolin da suka dabaibaye 'yan Najeriya, musamman ta fannin tattalin arziki da walwala.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng