Kotu Ta Yi Hukunci a Ƙarar da Aka Nemi Tsige Mai Martaba Sarki daga Mulki
- Babbar kotun jihar Oyo ta tabbatar da naɗin Oba Francis Olushola Alao a matsayin sarkin Orile Igbon (Olugbon na Orile Igbon)
- Mai shari'a K.A. Adedokun ya kori karar da mutum huɗu ƴan gidan sarautar Akingbola suka shigar, suna kalubalantar naɗin basaraken
- A hukuncin da kotun ta yanke, ta ce masu karar ba su da hurumin ƙalubalantar naɗin sarkin kuma sun gaza gamsar da kotu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ibadan, jihar Oyo - Babbar kotun jihar Oyo da ke zamanta a Ibadan, a ranar Litinin, ta yi watsi da wata kara da da aka nemi tuɓe rawanin sarkin Orile Igbon (Olugbon na Orile Igbon).
Kotun ta yi fatali da karar wacce 'yan uwa hudu daga dangin Akingbola suka shigar, inda suke kalubalantar nadin Oba Francis Olushola Alao a matsayin Olugbon na Orile Igbon.

Kara karanta wannan
Tsohon dan majalisa ya dauki matakin kotu da Tinubu ya ayyana dokar ta baci a Ribas

Asali: Original
Me yasa kotu ta kori karar tsige sarki?
Mai shari’a K.A. Adedokun ne ya yanke hukuncin, yana mai cewa kotun ba ta da hurumin sauraron karar saboda wasu manyan dalilai na doka, rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar mai shari’a Adedokun, wadanda suka shigar da karar ba su da iko ma'ana damar da doka ta sahalewa mutum ya shigar da kara a kotu.
Alkalin ya ce masu karar sun gaza nuna gamsassun hujjojin da za su tabbatar da cewa su ne suka cancanta su nemi tsige Oba Alao daga kujerarsa a jihar Oyo.
Har ila yau, kotun ta bayyana cewa wadanda suka shigar da karar sun yi kuskure na rashin hadawa da karamar hukumar Surulere cikin karar, wadda ita ce mai hurumin jagorantar zabin sarki da amincewa da shi bisa doka.
Dalilin shigar da ƙara kan naɗin sarkin?
A karar da suka shigar, 'yan dangin Akingbola sun bayyana cewa an samu wasu kura-kurai da rashin bin tsarin doka yayin zaben sabon sarkin da kuma nadin Oba Alao a matsayin Olugbon.
Sai dai kotun ta ce ba su da hurumin da ya dace su kalubalanci nadin, ballantana su nemi tsige basaraken daga karagar mulki, kamar yadda Tribune ta tattaro.

Asali: Facebook
Wannan hukunci wata gagarumar nasara ce ga Oba Francis Olushola Alao, wanda ya kasance daya daga cikin fitattun sarakunan gargajiya a yankin Ibarapa da ke jihar Oyo.
Hankula sun kwanta a masarautar Orile Igbon
Masarautar Olugbon na daya daga cikin tsofaffin masarautu a yankin, kuma ana nadin sabon sarki ne ta hanyar bin tsari da al’ada tare da sahalewar hukumomin da suka dace.
Hukuncin na kotu ya kawo karshen rikicin da ya shafe lokaci, inda yanzu ake sa ran kwanciyar hankali da ci gaban da al’umma za su samu a yankin Orile Igbon.
Olubadan ya yi magana kan sarautar Sasa
A wani labarin, kun ji cewa Mai Martaba, Olubadan na Ibadan a jihar Oyo, Oba Owolabi Olakulehin ya ce sarkin Sasa ba shi da wani matsayi a doka.
Mai martaba sarkin ya ce doka ba ta san da sarkin Sasa a matsayin wakilin Olubadan ba, yana mai cewa ba shi da inganci.
Basaraken ya bayyana hakan ne a ranar Litinin da ta gabata, 8 ga watan Afrilun 2025 a wurin taron majalisarsa da aka gudanar a fadarsa da ke Ibadan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng