Yaki da Yunwa: An ba Malaman Gona Babura 300 domin Shiga Lungu da Sako a Jigawa
- Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da rabon babura 300 ga malaman gona domin saukaka zirga-zirga da wayar da kan manoma
- Rahotanni sun tabbatar da cewa an raba baburan ne a matsayin rance ba mai kudin ruwa ba, kuma za su biya su ne a cikin watanni 60
- An bayyana cewa shirin na daga cikin kokarin gwamnati na sauya fasalin harkar noma da tabbatar da wadatar abinci a fadin Jigawa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Jigawa - Gwamnatin Jihar Jigawa ta kaddamar da wani shiri na bunkasa harkar noma ta hanyar rabon babura guda 300.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an raba baburan ne ga ma’aikatan wayar da kan manoma a mataki na biyu na Shirin Karfafa Ma’aikatan Noma (JAESP).

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan yadda aka kaddamar da shirin ne a cikin wani sako da mai magana da yawun gwamna Umar Namadi, Garba Muhammad ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Umar Namadi ne ya kaddamar da rabon baburan a Dutse ranar Asabar 13 ga Afrilu, 2025, wanda ke cikin shirinsa na bunkasa noma da tabbatar da isasshen abinci ga al’ummar jihar.
Babura 300 da aka raba na cikin jimillar guda 1,700 da gwamnati ke shirin bayarwa domin saukaka ayyukan ma’aikatan gona a sassa daban-daban na jihar.
Karin bayani kan raba babura a Jigawa
A wajen bikin rabon baburan, Gwamna Namadi ya bayyana cewa an raba abubuwan hawan ne a bisa rancen da ba shi da kudin ruwa, kuma za a biya kudinsu cikin watanni 60.
Ya ce hakan zai ba ma’aikatan damar isa ga manoma a karkara cikin sauki domin isar da sababbin dabarun noma da tallafin da ya dace.
"Mun kuduri aniyar sauya fasalin noma a jihar Jigawa.
"Wadannan babura za su taimaka wa ma’aikatanmu wajen isar da sababbin hanyoyin noma da fasahohi daga cibiyoyin bincike zuwa hannun manoma,"
- Gwamna Umar Namadi
Ya kara da cewa shirin yana da nufin kara yawan amfanin gona, kara kudin shiga ga manoma, da wadatar da abinci a fadin jihar.
Mutanen Jigawa sun yi wa Namadi godiya
Taron rabon baburan ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, masu ruwa da tsaki a fannin noma, da kuma wadanda suka amfana.
Bayan kammala rabon, mutanen da suka ci moriyar shirin sun bayyana godiyarsu bisa tallafin da suka ce zai sauya yadda noma ke gudana a karkara.

Asali: Facebook
Shugaban masu karbar tallafin, ya ce a baya suna fuskantar matsalolin zirga-zirga da ke hana su kai wa ga manoma a kan lokaci.
A karshe, Gwamna Namadi ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da zuba jari a fannin noma domin farfado da tattalin arzikin jihar.
Za a tallafawa manoma 500,000 a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya za ta yi hadaka da kasar Japan domin tallafawa manoma a jihohi.
Ministan noma, Sanata Abubakar Kyari da ministan kudi, Wale Edun ne suka tattauna da jami'an Japan a Abuja.
An bayyana cewa kimanin manoma 500,000 ne za a tallafawa a karkashin shirin da kayan aiki domin bunkasa samar da abinci a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng