'Yan Ta'adda Sun Sake Tabargaza a Filato, Sun Kashe Mutane kusan 50

'Yan Ta'adda Sun Sake Tabargaza a Filato, Sun Kashe Mutane kusan 50

  • Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan al’ummar Zike da ke karamar hukumar Bassa, inda suka kashe mutane 40 a wani sabon hari a Filato
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa mutane da dama sun jikkata yayin harin, kuma ana kula da su a asibitoci daban-daban na fadin jihar
  • Shugabannin Kiristoci sun shirya yin zanga-zangar lumana ranar Litinin 21 ga Afrilu domin nuna fushinsu kan kashe-kashen da suka addabi jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Plateau - Wani sabon hari da wasu da ake zargi da ‘yan bindiga ne suka kai a safiyar Litinin ya yi sanadin mutuwar mutane 40 a jihar Filato.

Rahotanni sun nuna cewa an kai harin ne a garin Zike da ke Kimakpa, yankin Kwall a karamar hukumar Bassa ta Jihar Filato.

Kara karanta wannan

Zamfara: Bayan kisan ɗan bindiga, miyagu sun ɗauki fansa, sun ƙona masallacin Juma'a

An kai hari Filato
'Yan ta'adda sun kai sabon hari jihar Filato. Hoto: Plateau Sate Government
Asali: Facebook

Wani shugaban al’umma daga yankin Kwall, Wakili Tongwe, ya shaidawa Channels TV cewa maharan sun shigo kauyen da safiyar Litinin kuma suka fara harbe-harbe ba kakkautawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce su da wasu jami’an tsaro suna sintiri a wani yanki dabam a lokacin da aka kai harin, kuma duk da sun tunkari maharan, tuni sun yi barna da dama kafin a fatattake su.

Baya ga haka, Wakili Tongwe ya bayyana cewa maharan sun jikkata mutane da dama wanda ya yanzu haka suna asibitoci suna karbar magani.

Kiristoci za su shirya zanga zanga a Filato

Kashe kashe na tayar da kura a tsakanin al’ummar Kirista a jihar, inda suka bayyana shirin gudanar da zanga-zangar lumana ranar Litinin, 21 ga Afrilu, 2025.

Sun bayyana cewa za su yi zanga zangar ne domin nuna fushinsu kan yadda ake ci gaba da kashe mutane ba tare da hukunta masu laifi ba.

Kara karanta wannan

Yadda riƙaƙƙen ɗan bindiga ke bautar da jama'a, ya yi musu barazanar noma

Shugaban kungiyar Gideon and Funmi Peace Foundation, kuma mamba a kwamitin shirya zanga-zangar, Dr. Gideon ParaMallam, ya tabbatar da shirin zanga zangar.

Ya bayyana cewa za a gudanar da gangamin daga Tashar PRTV zuwa Gidan Gwamnati da ke Little Rayfield a Jos.

Punch ta wallafa cewa ya ce:

“Daga 27 ga Maris zuwa 2 ga Afrilu, an kashe mutane fiye da 80 a Karamar Hukumar Bokkos kadai. Wannan bai haɗa da wanda aka kashe a Bassa da sauran sassan Najeriya ba,”

Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN), reshen Jihar Filato, na jagorantar shirin zanga-zangar, inda suka bukaci mabiya addinin Kirista su sa tufafi baƙi a ranar.

Sun bayyana launin baƙi a matsayin alamar baƙin ciki, ja a matsayin kira da a daina kashe-kashe, yayin da fari ke nuni da nuna damuwa cikin lumana.

Sun bukaci gwamnatin tarayya da ta dauki matakin dakile harin, tare da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya musamman a yankunan da ke fama da irin wannan rikici.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke mutane sama da 100 da suka kai farmaki cikin dare a Abuja

Tinubu
An bukaci gwamnati ta magance kashe kashe a Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

'Yan sanda sun kwato bindigogi a Kaduna

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan Najeriya ta sanar da wata gagarumar nasara da ta samu a Kaduna.

Rundunar ta bayyana cewa ta samu kama wasu tarin bindigogi a wata tashar mota da ake zargin za a mika ga 'yan ta'adda.

A wani samame da rundunar ta kai kan wasu 'yan ta'adda, ta ceto mutanen da aka sace su 17 wanda galibinsu mata ne da yara kanana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng