Gwamnati Ta Yi Martani da Kotun Amurka Ta Yi Umarnin a Yi wa Tinubu Tonon Silili

Gwamnati Ta Yi Martani da Kotun Amurka Ta Yi Umarnin a Yi wa Tinubu Tonon Silili

  • Fadar shugaban kasa ta yi magana a kan umarnin da kotun Amurka ta bayar na cewa a saki bayanan binciken Bola Tinubu kan zargin safarar kwayoyi
  • Mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa babu sabon abu da za a gani a cikin bayanan da za a saki
  • Mista Onanuga ya kara da cewa tun tuni wani jami'in FBI ya fitar da rahoto kan binciken, kuma jama'a na da damar ganin abin da ya binciko game da Tinubu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja –Fadar shugaban kasa ta mayar da martani kan hukuncin da wata kotu a Amurka ta yanke a kan Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Hukuncin ya umarci hukumomin gwamnatin tarayya su saki bayanan da suka shafi zargin da ake wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu dangane da safarar miyagun kwayoyi.

Tinubu
Gwamnati ta yi martani kan bayyana bincike a kan Tinubu Hoto: Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Federal Bureau of Investigation/FBI
Asali: Facebook

A sanarwar da mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya wallafa a shafin X a ranar Lahadi, ya bayyana cewa hukuncin kotun bai zargi Tinubu da wani laifi ba.

A ranar 8 ga Afrilu, wata kotun Amurka ta umurci Hukumar binciken manyan laifuffuka ta Amurka (FBI) da Hukumar yaki da miyagun kwayoyi (DEA) su fitar da sakamakon binciken Tinubu.

Yadda kotu ta yi hukunci kan Tinubu

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa an yanke wannan hukunci ne bayan karar da wani dan Amurka mai suna Aaron Greenspan ya shigar, wanda kuma shi ne ya kafa dandalin PlainSite.

Greenspan ya shigar da bukatu 12 na neman bayanai ga hukumomin gwamnatin tarayya shida daban-daban a Amurka.

Ya mika bukatun ne saboda yana neman bayanan binciken da suka shafi wata kungiya ta masu safarar hodar iblis a birnin Chicago tun farkon shekarun 1990.

Cikin wadanda Greenspan ya nemi bayanansu akwai sunayen mutane hudu da ake zargin suna da alaka da safarar kwayoyin, ciki har da shugaban Najeriya, Bola Tinubu.

Tinubu: Martanin gwamnati kan umarnin kotu

A martaninsa game da hukuncin, Bayo Onanuga ya bayyana cewa babu wani sabon abu da zai fito fili daga wannan hukunci, kasancewar rahotannin FBI da DEA sun wanke Tinubu fiye da shekaru 30 da suka wuce.

Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

A cewarsa:

“’Yan jarida sun nemi jin martanin fadar shugaban kasa kan hukuncin da wani alkalin kotun Washington DC ya yanke a makon jiya, inda ya umurci FBI da DEA su saki rahotannin da ke da alaka da Bola Ahmed Tinubu.”
“Martaninmu shi ne kamar haka: babu wani sabon abu da zai fito. Rahoton jami’in FBI mai suna Agent Moss da na hukumar DEA sun jima suna cikin kundin bayanan da jama'a za su iya gani na sama shekaru 30. Rahotannin ba su zargi shugaban Najeriya da wani laifi ba. Lauyoyi suna nazarin hukuncin.”

Kotu ta ba da umarnin kan Bola Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa wata kotu a Amurka, ta yanke hukunci, inda ta umurci hukumar FBI da ta DEA da su fitar da bayanan bincike kan Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.

An zargi shugaba Bola Ahmed Tinubu da hannu dumu-dumu a cikin wata hadaddiyar masu safarar miyagun kwayoyi, wanda ake zargin ya gada hannu da wasu mutum uku.

Alkalin kotun, Beryl Howell, ne ya bayar da wannan hukunci bisa buƙatar Aaron Greenspan, wanda ya nemi bayanai a kan Lee Andrew Edwards, Mueez Abegboyega Akande, Abiodun Agbele da Bola Tinubu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng