Zamfara: Bayan Kisan Ɗan Bindiga, Miyagu Sun Dauki Fansa, Sun Ƙona Masallacin Juma'a
- Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kona masallacin Juma’a, asibitin kula da lafiya da gidaje fiye da goma a Biyabiki, Zamfara
- Hare-haren sun faru ne da misalin karfe 8 na dare a ranar Asabar, a matsayin ramuwar gayya kan kisan 'yan uwan Adamu Aliero
- Shaidu sun ce ba a yi garkuwa ko kisa ba, amma 'yan bindigar sun kona gine-gine sannan suka tsere bayan kusan awa guda suna barna
- Mutanen garin sun bayyana cewa suna cikin fargaba tun bayan kisan Isuhu Yellow, inda suka danganta wannan da yakin ramuwar gayya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kona masallacin Juma’a a jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya.
Miyagun sun kuma kona cibiyar kula da lafiya da gidaje fiye da goma a kauyen Biyabiki, karamar hukumar Tsafe.

Asali: Original
Ana zargin kai harin ramuwar gayya a Zamfara
Harin dai ya faru ne da misalin karfe 8 na dare ranar Asabar 12 ga watan Afrilun 2025, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana kyautata zaton harin ramuwar gayya ne daga mabiyan riƙakken dan bindiga a yankin, Adamu Aliero.
Majiyoyi daga kauyen sun bayyana cewa harin na da nasaba da kisan dan uwan Adamu Aliero da ake kira Isuhu Yellow da dansa a wani hari.
Shaidu sun ce ‘yan bindigar sun shigo kauyen, suka kona gine-gine, ba tare da kashe kowa ko yin garkuwa da wani ba, sannan suka tsere.
Majiyar ta ce:
“Sun kona wurare kawai, ciki har da masallacin Juma’a da asibitin gari, sun lalata gidaje goma a harin da ya dauki kusan awa guda."
Menene dalilin kai mummunan harin a Zamfara?
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun kai farmaki a kauyen Tsageru tun da sassafe, inda suka kona gidaje a wani hari da aka tsara.
“Ba mu san dalilin kona kadarorin gwamnati da gidajen mutane ba.
“Tun kisan Isuhu Yellow, garuruwanmu na cikin barazana, muna ganin wannan wani bangare ne na yakin ramuwar gayya.
- Cewar wata majiyar

Asali: Twitter
Babu labari daga rundunar yan sandan Zamfara
Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sanda ta Zamfara, DSP Yazid Abubakar ya ci tura, domin bai dauki kira ba.
Sabon harin ya nuna irin rashin tsaron da ke addabar Zamfara, inda 'yan bindiga ke ci gaba da addabar kauyuka duk da matakan soja.
Kisan Dan uwan Aliero ya ta da rigima
Mun ba ku labarin cewa rikakken ɗan bindiga, Ado Aliero, ya kira taron gaggawa bayan kashe ɗan uwansa, Isuhu Yellow, da yaran Dogo Gide suka yi a Zamfara.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa an gudanar da taron ne a sansanin Aliero da ke dajin Munhaye, ƙaramar hukumar Tsafe.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa an ga ɗaruruwan ‘yan bindiga a babura suna tafiya zuwa Munhaye don halartar taron da Aliero ya kira.
Ana zargin kashe Isuhu Yellow wata alama ce ta rikicin da ke tsakanin Aliero da Gide, wanda ke haddasa tashin hankali da asarar rayuka a yankin.
Asali: Legit.ng