Dakarun Sojoji Sun Bankado Shirin 'Yan ISWAP na Kafa Sansanoni a Jihohin Arewa 2

Dakarun Sojoji Sun Bankado Shirin 'Yan ISWAP na Kafa Sansanoni a Jihohin Arewa 2

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar bankaɗo wani shirin ƴan ta'addaan ISWAP na kafa sansanoni a jihohin Bauchi da Plateau
  • Sojojin sun gano shirin ne bayan cafke wasu ƴan ta'addan ISWAP da suka yi basaja domin faɗaɗa ayyukan ƙungiyar
  • Jami'an tsarom sun su nasarar cafke ƴan ta'addan ne a yankin Yelwa da ke ƙaramar hukumar Shendam ta jihar Plateau

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Dakarun sojoji na rundunar Operation Safe Haven (OPSH) sun bankaɗo wani makirci na ƙungiyar ƴan ta'addan ISWAP.

Dakarun sojojin sun gano yunƙurin ƴan ta'addan na kafa sansanoni a jihohin Plateau da Bauchi.

Dakarun sojojin Najeriya
Dakarun sojoji sun gano shirin kafa sansanonin 'yan ISWAP a jihohin Plateau da Bauchi Hoto: @HQNigerianArmy (X)
Asali: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar OPSH, Manjo Samson Zhakom, ya fitar a ranar Lahadi, 13 ga watan Afirilun 2025, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bude wuta kan jami'an tsaro, an samu asarar rayuka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun bankaɗo shirin ƴan ISWAP

Sanarwar ta ce dakarun sojojin sun kama wasu mutane biyu da ake zargin ƴan ISWAP ne yayin wani samame da suka kai ranar Juma'a, 11 ga watan Afirilu a yankin Yelwa da ke ƙaramar hukumar Shendam a jihar Plateau.

An bayyana sunayen waɗanda aka kama a matsayin Abdulkadir Dalhatu da Ubaidu Hassan, dukkansu ƴan shekaru 25.

Mutanen sun yi basaja ne a matsayin masu sana'ar ɗinki domin ɓoye ainihin aikinsu na taimakawa ISWAP wajen faɗaɗa ayyukanta zuwa yankin Arewa ta Tsakiya.

Binciken farko ya nuna cewa wani kwamanda daga ISWAP ne ya turo su domin kafa sababbin wuraren aikata ta'addanci a jihohin Plateau da Bauchi.

Sojoji sun fatattaki ƴan bindiga

Dakarun sojoji
Dakarun sojoji sun samu nasara kan 'yan bindiga Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

A wani samame na daban, dakarun rundunar OPSH sun kai farmaki a maɓoyar wani babban mai laifi da ake nema ruwa a jallo a ƙauyen Mazat, ƙaramar hukumar Barkin Ladi.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun samu gagarumar nasara kan 'yan bindiga a Katsina

Ko da yake wanda ake nema ya gudu kafin zuwan sojojin, amma sun gano bindiga ƙirar AK-47, gidan harsashi da wasu kayayyakin da aka binne a cikin ginin.

Hakazalika, dakarun sojoji na sashe na biyu, sun yi kwanton ɓauna ga ƴan bindiga bayan sun samu sahihan bayanan sirri.

Sojojin sun yi kwanton ɓauna ga ƴan bindigan ne a hanyar Pinau-Bangalala da ke ƙaramar hukumar Wase, inda suka kashe ɗaya daga cikin su, yayin da sauran suka tsere da raunuka.

A wani lamari mai ban tausayi, al’ummar ƙauyen Zogu da ke gundumar Miango a ƙaramar hukumar Bassa sun shiga cikin jimami bayan wasu ƴan ta’adda sun kashe wani mutum da ƴaƴansa biyu a wani harin ta'adddanci da suka kai da sassafe ranar Asabar.

Dakarun sojoji sun hallaka hatsabibin ɗan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun rundunar sojojin ƙasa da na sama sun samu nasara kan ƴan bindiga a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Duk da hare haren Boko Haram, gwamnati za ta shigar da tubabbun 'yan ta'adda cikin al'umma

Dakarun sojojin sun samu nasarar hallaka.wani riƙaƙƙen ɗan bindiga mai suna Gwaska a wani samame da suka kai.

Jami'an tsaron sun kuma yi nasarar halllaka ƴan bindiga sama da 100 a hare-haren haɗin gwiwa da suka kai kan miyagun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng