Akwai Wata a Kasa: Kungiyar NCM Ta Gargadi 'Yan Najeriya kan Hadewar Atiku da El Rufai
- Ƙungiyar NCM ta yi magana kan sauyin ra'ayin siyasa da Nasir Ahmed El-Rufai y a samo dangane da Alhaji Atiku Abubakar
- A cikin wata sanarwa, shugaban NCM ya nuna shakku kan yadda tsohon gwamnan na Kaduna ya koma yana ɗasawa da Atiku
- Lawal Nuhu Ahmed ya bayyana cewa sauyin ra'ayin da El-Rufai ya samu bai rasa nasaba da matsalolin da yake fuskanta a siyasance
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Ƙungiyar Northern Conscience Movement (NCM) ta nuna damuwa kan ɗasawar da Nasir El-Rufai ya koma yana yi yanzu da Atiku Abubakar.
Ƙungiyar ta nuna shakku kan sauyin matsayar siyasa da tsohon gwamnan na Kaduna ya yi kwanan nan, inda yanzu ya fara nuna girmamawa ga tsohon mataimakin shugaban ƙasan wanda a baya ya riƙa suka.

Asali: Twitter
Hakan na ƙunshe ne a cikin cikin wata sanarwa da jagoran ƙungiyar NCM, Lawal Nuhu Ahmed, ya sanyawa hannu, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An nuna shakku kan alaƙar El-Rufai da Atiku
Ƙungiyar ta nuna shakku kan sahihancin girmamawar da El-Rufai ke nuna wa Atiku, musamman ganin irin kalaman suka masu zafi da ya taɓa yi masa a baya.
Sanarwar ta kuma yi magana kan lokaci da yanayin yadda sauyin ya faru, tana nuna cewa biyayyar na da alaƙa da ƙalubalen siyasa da El-Rufai ke fuskanta a halin yanzu, ciki har da rikicinsa da Shugaba Bola Tinubu.
"Ƙungiyar NCM ta ga dacewar bayyana matsayarta kan wannan sabon lamari mai ban mamaki, inda tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ke nuna yabo da girmamawa ga tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar."
“Wannan sauyin kalaman siyasa daga El-Rufai, wanda a baya ya kasance mai suka sosai ga Atiku, yana janyo tambayoyi masu yawa kan gaskiya da daidaiton matsayarsa a siyasa."

Kara karanta wannan
Atiku, El Rufai, Malami da sauran manyan ƴan adawa da suka ziyarci Buhari a Kaduna
"A baya El-Rufai bai taɓa yin shakku ba wajen caccakar Atiku. Ya kira Atiku ‘maƙaryaci’ da kuma zargin cewa yana da son mulki."
“Waɗannan kalamai ba kawai yarfe ba ne na siyasa ba, sun samo asali ne daga zarge-zargen da suka daɗe suna bibiyar Atiku a siyasar Najeriya."
- Lawal Nuhu Ahmed

Asali: Twitter
“Amma wannan sabon sauyin da El-Rufai ya yi ya janyo tambayoyi, musamman idan aka yi la’akari da matsalolin siyasarsa na yanzu, kamar rikicinsa da Shugaba Bola Tinubu wanda ya naɗa shi a matsayin minista, amma daga baya majalisar dattawa ta ƙi amincewa da naɗin."
“Waɗannan abubuwa na iya nuni da cewa El-Rufai ya sauya dangantaka ta siyasa saboda buƙatarsa ba wai don sauyin ra’ayi ba ne."
“Muna jan hankalin jama’a da ka da su ɗauki wannan girmamawar da El-Rufai ke nunawa a matsayin sulhu na gaskiya, sai dai a duba shi a matsayin wani yunƙuri da ke da nasaba da yadda siyasar Najeriya ke canzawa lokaci zuwa lokaci."
El-Rufai ya magantu kan ziyartar Buhari
A wani labarin kuma, kun ji cewa babban jigo a jam'iyyar SDP, Nasir Ahmed El-Rufai ya yi magana kan ziyarar da jiga-jigan ƴan adawa suka kai wa Muhammadu Buhari.
Tsohon gwamnan na Kaduna, ya bayyana cewa bai kamata abokan hamayya su damu ba kan ziyarar da suka kai wa tsohon shugaban ƙasan.
El-Rufai ya bayyana cewa ziyarar da suka kai wa tsohon shugaban ƙasan ba ta da alaƙa da siyasa face ziyarar sada zumunci.
Asali: Legit.ng