Dalilin Tinubu na Shafe Kwanaki 59 a Paris a Lokuta 8 da Ya Kai Ziyara Faransa

Dalilin Tinubu na Shafe Kwanaki 59 a Paris a Lokuta 8 da Ya Kai Ziyara Faransa

Shugaba Bola Tinubu ya shafe akalla kwanaki 59 a birnin Paris na Faransa, a ziyarce-ziyarce takwas, tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Faransa ta zama kasar da Tinubu ke matukar sha’awa, inda ziyarce ta kan dalilin aiki da kashin kai, lamarin da ya sa ta zama kasar da fi kai wa ziyara.

Tinubu ya ziyarci Faransa sau 8 tun bayan hawa mulki a 2023
An ji dalilin Tinubu na zuwa Faransa sau 8 tun bayan hawansa mulki a 2023. Hoto: @PBATMediaCentre
Asali: Twitter

Tafiye-tafiyen Tinubu zuwa kasar Faransa

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa ko tun kafin ya zama shugaban Najeriya, Tinubu ya riga ya nuna soyayya ta musamman ga kasar Faransa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan ya sa ake ganin cewa tun kafin rantsar da shi a ranar 29 ga Mayu, ya ziyarci Faransa a matsayin zababben shugaban kasa.

Bayan hawansa mulki, Faransa ce kasar farko da Tinubu ya fara ziyarta.

Yawaitar ziyarce-ziyarcen da yake kaiwa kasar ya sa 'yan Najeriya da dama ke guna-guni, musamman ganin cewa shugaban Faransa Emmanuel Macron bai kai irin wannan ziyarar zuwa Najeriya ba.

Kara karanta wannan

Buhari ya yi wa Sheikh Pantami wasa da dariya da ya ziyarce shi a Kaduna

Ziyarar baya-bayan nan

A ranar 2 ga Afrilun 2025, fadar shugaban kasa ta sanar cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai tafi birnin Paris, Faransa “don gajeriyar ziyarar aiki.”

Bayo Onanuga, mai magana da yawun shugaban kasa, ya bayyana cewa, Tinubu zai yi amfani da wannan ziyarar domin "duba yadda mulkinsa ke tafiya, da kuma nazarin manyan nasarorin da ya samu."

Ya kuma ce Tinubu zai yi amfani da ziyarar wajen nazarin sauye-sauyen da gwamnatinsa ta kawo, tare da tsara dabarun samar da ci gaba a kasar kafin cikarsa shekara biyu a mulki.

Wannan lokaci na nazarin mulkinsa, zai taimaka wajen zurfafa sauye-sauyen da ake yi da kuma hanzarta ba da fifikon ci gaban kasa a shekara mai zuwa.

Onanuga ya ce nasarorin tattalin arzikin da aka samu a baya-bayan sun hada da karin kudin ajiyar Najeriya na kasashen waje zuwa dala biliyan 23.11, kamar yadda CBN ya bayyana.

Kara karanta wannan

Tsohon ɗan majalisa ya hango wanda zai ci zaɓe idan Atiku, Obi da El-Rufa'i suka haɗe a 2027

Ya tabbatar da cewa Shugaba Tinubu zai ci gaba da tuntubar 'yan tawagarsa da kuma kula da al'amuran mulki yayin da yake a Paris, sannan "zai dawo gida cikin makonni biyu."

Kafin wannan ziyarar, Shugaba Tinubu ya ziyarci birnin Paris na Faransa har sau bakwai.

Yuni, 2023

Bayan makonni uku da rantsar da shi a ranar 29 ga Mayu, 2023, Shugaban Tinubu ya bar Abuja zuwa Faransa don halartar taron koli na NGFP, inda ya kwashe kwanaki hudu.

A lokacin da yake birnin Paris, ya shiga cikin shugabannin duniya wajen tattaunawa da rattaba hannu kan yarjejeniyar hada-hadar kudi ta duniya.

Wannan yarjejeniya na bai wa kasashe masu rauni fifiko don samun tallafi da jari bayan mummunan tasirin sauyin yanayi, matsalar makamashi da annobar COVID-19.

A cewar wata sanarwa daga Dele Alake, hadimin Tinubu kan ayyuka na musamman, a lokacin, an shirya amfani da wannan ziyarar ne domin binciko hanyoyin dawo da walwalar kudi ga kasashen da ke fama da matsalolin biyan bashi, musamman wadanda suka fi fuskantar matsin lamba.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Zariya da wani magidanci ya kashe ɗan uwansa da duka

Satumba, 2023

A watan Satumbar 2023, Shugaba Bola Tinubu ya ziyarci birnin New York na Amurka inda ya halarci Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya, daga nan kuma ya wuce zuwa Faransa.

Majiyoyin fadar shugaban kasa sun bayyana cewa Tinubu ya je Paris domin ya dan huta. An ce ya kwashe kusan kwanaki biyar a Faransa.

A taron UNGA, Shugaba Tinubu ya caccaki yawaitar juyin mulkin soji a nahiyar Afirka, yana mai cewa hakan ba daidai ba ne kuma baya wakiltar muradun jama’a.

Shugaba Tinubu ya dage cewa dole Afirka ta tsaya kai da fata wajen kare tsarin dimokuradiyya a matsayin mafita mafi kyau ga muradun jama’a.

“Juyin mulkin soja ba daidai ba ne, kamar yadda kowanne tsarin siyasar farar hula da ke haifar da zalunci ya zama abin kyama,” in ji Tinubu a jawabinsa na farko a babban taron.

Game da Jamhuriyar Nijar, Tinubu ya bayyana cewa har yanzu Kungiyar ECOWAS na ci gaba da tattaunawa da shugabannin mulkin sojin kasar.

Kara karanta wannan

Atiku, Obi da El Rufai na shirin haɗewa, Tinubu ya bude kofar kayar da shi a 2027

Janairu, 2024

A watan Janairu 2024, shugaban kasa ya sake barin Abuja zuwa Faransa bisa ziyarar kashin kai kamar yadda mai magana da yawunsa na wancan lokacin, Ajuri Ngelale, ya bayyana.

Ngelale ya ce ana sa ran Shugaba Tinubu zai dawo gida a makon farko na watan Fabrairu. Shugaban ya kwashe kwanaki 14 a Faransa.

“Shugaba Bola Tinubu ya bar Abuja zuwa Paris, Faransa, a ranar Laraba, 24 ga Janairu, 2024, domin ziyarar kashin kai. Zai dawo gida a makon farko na watan Fabrairu,” in ji sanarwar.

Agusta, 2024

A daya daga cikin ziyarce-ziyarcensa, Shugaba Tinubu ya bar Abuja a ranar 19 ga Agusta zuwa Faransa.

Ziyarar shugaban kasar ta zo ne a daidai lokacin da ake samun takaddama tsakanin kamfanin kasar Sin, Zhongshan Fucheng da gwamnatin jihar Ogun.

Jirgin da shugaban kasa ya yi amfani da shi ya kasance daya daga cikin jiragen shugaban kasa guda uku da wata kotun Faransa ta rike a madadin kamfanin kasar Sin.

Kara karanta wannan

Manyan ƴan adawa na shirin haɗaka, ɗan majalisa ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP

Jaridar Legit.ng Hausa ta fahimci cewa jirgin ya sauka a Faransa kwana guda kafin shugaban kasa ya tafi.

Ana gobe zai tafi Paris, Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban kasar na wancan lokaci, ya bayyana cewa Tinubu zai tafi Faransa a ranar Litinin, 19 ga Agusta daga Abuja.

Duk da cewa sanarwar bata bayyana dalilin ziyarar ba da lokacin da zai shafe, Ngelale ya ce: “Shugaban kasa zai dawo gida bayan dan gajeren zaman aiki a Faransa.”

Sai dai, rahotanni sun bayya cewa Shugaba Tinubu ya kwashe kwanaki hudu kafin ya dawo gida Najeriya.

Oktoba, 2024

A farkon watan Oktobar bara, Shugaba Tinubu ya bar Abuja don yin hutu na makonni biyu a matsayin bangare na hutunsa na shekara-shekara.

Mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, a cikin wata sanarwa, ya bayyana cewa:

“Shugaban kasa Bola Tinubu zai bar Abuja yau (2 ga Oktoba) zuwa Burtaniya don fara hutu na makonni biyu, a matsayin wani bangare na hutun shekara-shekara.

Kara karanta wannan

'Arewa ta hada kai da Kudu maso Gabas': An ji dabarar kwace mulki daga hannun Tinubu

“Zai yi amfani da makonni biyun ne a matsayin lokacin tunani da kuma nazari kan sauye-sauyen tattalin arzikin da mulkinsa ke yi. Zai dawo gida bayan cikar hutun.

Sai dai a ranar 11 ga Oktoba, Shugaba Tinubu ya bar Burtaniya zuwa Faransa domin wani muhimmin taro, kamar yadda mai taimaka masa kan harkokin siyasa, Ibrahim Masari, ya bayyana.

A wani sako da ya wallafa a ranar 11 ga Oktoba, Masari ya tabbatar da tafiyar Tinubu daga Birtaniya zuwa Faransa, kamar yadda muka ruwaito.

“A yau, na samu damar ziyartar Shugaba Asiwaju Bola Tinubu (GCFR) a gidansa da ke Burtaniya, inda muka tattauna. Daga nan muka wuce zuwa Paris, Faransa don wata muhimmiyar ziyara,” in ji Masari.

Masari bai bayyana cikakken bayani kan ganawar da aka yi a Paris ba. Amma Shugaban ya kwashe kwanaki takwas a Faransa kafin dawowa gida.

Nuwamba, 2024

Tafiye-tafiyen da Tinubu ya yi zuwa Faransa daga hawansa shugaban kasa
Tinubu ya ziyarci kasar Faransa sau 8 daga hawansa mulki zuwa yanzu. Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

A watan Nuwamba, shugaban kasa ya sake komawa Faransa, wannan karon da matar sa a wata ziyarar gwamnati ta kwanaki uku.

Kara karanta wannan

An bayyana shirin Atiku da Obi na haduwa da El Rufa'i a SDP domin kifar da Tinubu

Ziyarar ta gudana ne a bisa gayyatar Shugaban Faransa Emmanuel Macron, domin “karfafa dangantaka tsakanin Najeriya da Faransa,” a cewar fadar shugaban kasa.

Cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga ya fitar mai taken ‘Shugaba Tinubu ya fara ziyarar gwamnati a Paris’, ya bayyana cewa:

“Ziyarar na da nufin karfafa hadin gwiwa a fannoni da dama, ciki har da noma, tsaro, ilimi, lafiya, matasa, kirkire-kirkire da sauya makamashi."

A cewar Onanuga, tare da Shugaba Macron, Shugaba Tinubu zai tattauna kan shirin musayar matasa da kara masu kwarewa a bangarorin fasaha, kirkira da shugabanci.

Ziyarar ta kuma kunshi muhimman tattaunawar siyasa da diflomasiyya kan batutuwan da suka shafi harkokin kudi, ma’adinai, kasuwanci, jari da sadarwa.

Haka zalika, shugabannin biyu sun halarci wani taro da Majalisar Kasuwancin Faransa da Najeriya ta shirya domin hada kai da ‘yan kasuwa wajen ci gaban tattalin arziki.

Brigitte Macron da Uwargidan Shugaban Najeriya sun tattauna batun karfafa mata, yara da kuma mabukata ta hannun shirin Renewed Hope na uwargidan shugaban kasa.

Kara karanta wannan

'Ba ni ba neman sanata': Gwamna ya ce yana gama wa'adinsa zai yi ritaya a siyasa

Shugaba Tinubu da matarsa sun halarci liyafar cin abinci da Shugaba Macron ya shirya musu.

Fabrairu, 2025

A farkon wannan shekara, a watan Fabrairu, muka ruwaito cewa Shugaba Tinubu ya sake kai ziyarar kashin kai zuwa Faransa.

Fadar shugaban kasa ta sanar cewa Tinubu ya bar Abuja zuwa birnin Paris kafin wucewa zuwa Addis Ababa, babban birnin Habasha.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Onanuga, ya bayyana cewa yayin da yake a Faransa, Tinubu ya gana da Shugaba Emmanuel Macron kafin ya wuce Addis Ababa.

Shugaban ya kwashe kwanaki bakwai a Faransa kafin ya wuce Habasha.

A Habasha, Shugaba Tinubu ya halarci taron shugabannin Afirka karo na 46 da taron shugabannin kasashe Tarayyar Afirka (AU) karo na 38 daga 12 zuwa 16 ga Fabrairu, 2025.

Zuwa Paris: 'Yan Najeriya sun dura kan Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai yi tafiya zuwa birnin Paris na ƙasar Faransa a ranar Laraba, 2 ga watan Afrilun 2025.

Kara karanta wannan

APC ta yi bayani kan shirin sauya mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima

Fadar shugaban Najeriya ta ce Mai girma Bola Ahmed Tinubu zai je birnin Paris ne domin yin ƴar gajeriyar ziyarar aiki ta kwanaki 14.

Ƴan Najeriya sun yi martani bayan samun labarin cewa Shugaba Tinubu zai sake tafiya zuwa ƙasar waje watanni da dawowars.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.