Dokar Ɓatanci: Gwamnatin Kano Ta Yi Martani ga Kotun ECOWAS kan Hukuncinta

Dokar Ɓatanci: Gwamnatin Kano Ta Yi Martani ga Kotun ECOWAS kan Hukuncinta

  • Gwamnatin Kano ta bayyana cewa ba za ta janye dokokin batanci ba, duk da hukuncin kotun ECOWAS da ke adawa da hakan
  • Kotun ECOWAS ta bayyana cewa wasu sashe na dokokin Kano sun sabawa ka’idar kare hakkin bil’adama, lamarin da ya tayar da ƙura
  • Kwamishinan yaɗa labarai na Kano, Ibrahim Waiya, ya ce dokokin na kare addini ne kuma suna wakiltar muradin al’ummar Musulmi na jihar
  • Ya ce Kano na da hurumin kafa dokokin da suka dace da al’adunta, inda ya ƙara da cewa za su ci gaba da kiyaye dokar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Gwamnatin Jihar Kano ta yi martani ga matakin da kotun ECOWAS ta dauka kan dokar batanci.

Gwamnatin ta kare dokar batancin da ta kafa, tana mai cewa tana da ikon kare tsarkin addini a jiharta.

Kara karanta wannan

Faɗin gaskiya ya yi rana: Gwamma ya naɗa mata 2 masu ɗauke HIV a muƙamai na musamman

Gwamnatin Kano ta mayar da martani ga kotun ECOWAS
Gwamnatin Kano fadi matsayarta bayan hukuncin kotun ECOWAS kan dokar batanci. Hoto: Sanusi Bature Dawakin-Tofa, @ecowas_cedeao.
Asali: Twitter

A wata sanarwa da ya fitar ga Punch, Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Ibrahim Waiya, ya ce jihar ba za ta ja da baya ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dokar batanci: Wane hukunci ECOWAS ta yi?

Kotun ECOWAS ta yanke hukunci cewa wasu sashe na dokokin saɓo da addini na Kano ba su yi daidai da ka’idar kare hakkin dan Adam ba.

Kotun ta bayyana cewa sassan doka na laifuffuka da na dokokin da Sharia na jihar Kano sun tauye ’yancin fadin albarkacin baki.

Ta kuma umurci gwamnatin Najeriya ta soke ko ta gyara wadannan dokokin da suka saba wa tsarin doka na duniya.

Gwamnatin Kano ta kalubalanci hukuncin kotun ECOWAS kan dokar batanci
Gwamantin Kano ta yi fatali da hukuncin kotun ECOWAS kan dokar batanci a jihar. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Asali: Facebook

Dokar batanci: Martanin Abba Kabir ga ECOWAS

Waiya ya ce ba za su lamunci kowane irin matsin lamba ba daga ko ina na inda ya ce za su kare dabi'u da al'adun jihar.

Ya ce:

"Ba za mu lamunci matsin lamba daga waje ba, dole mu kare dabi’u da imaninmu, dkkan dokokinmu alƙibla ce ta muradun jama'a.”

Kara karanta wannan

Kotun ECOWAS ta yi hukunci kan sahihancin dokar batanci ga ma'aiki a Kano

Ya ce kariyar gwamnatin Kano tana kan tsarin mulkin Najeriya, inda kowace jiha ke da ikon kafa dokokin da suka dace da al’ummarta.

Ya ƙara da cewa:

“Jama’ar Kano sun ba mu amanar kiyaye zaman lafiya da ƙimomin addininsu, wadannan dokoki za su ci gaba da kasancewa.
“Muna girmama ikon kotun, amma dokokinmu dole su dace da tsarin ɗabi’a da addinin mutanenmu."

Duk da hukuncin kotun ECOWAS, Ibrahim Waiya ya jaddada kudirin gwamnati wajen kiyaye tsarkin addini da daidaito a cikin al’umma.

Gwamnatin ta Kano ta ce dokokin batanci ba sabawa suka yi ba, illa dai suna nuna yadda tsarin doka na Najeriya ya ke.

An sake kama mafarautan Kano a Edo

Mun ba ku labarin cewa rundunar ‘yan sanda ta Edo ta ce an cafke mafarauta hudu daga Kano da makamai yayin da suka isa jihar ranar Asabar da dare.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Moses Yamu, ya bayyana cewa an kama mafarauta ne ba Fulani makiyaya ba.

An bayyana sunayen mafarautan da aka kama da Yusuf Abdulkarim, Mujaheed Garba, Shittu Idris, da Jamilu Habibu, kuma daga Doguwa a Kano suka fito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.