Sojoji Sun Gwabza Fada da Ƴan Ta'adda, An Kashe Hatsabibin Ɗan Bindiga, Gwaska

Sojoji Sun Gwabza Fada da Ƴan Ta'adda, An Kashe Hatsabibin Ɗan Bindiga, Gwaska

  • Rundunar sojojin kasa da na saman Najeriya sun hallaka jagoran 'yan bindiga Gwaska da yaransa 100 a wani farmaki da suka kai Katsina
  • An kai farmakin ne a sansanonin 'yan bindiga da ke Kankara da Faskari bisa bayanan leken asiri, kuma an lalata makaman su da kwace babura
  • Gwamna Dikko Umaru Radda ya jinjina wa jami’an tsaro, yana mai cewa za a dawo da zaman lafiya Katsina idan aka samu hadin kan jama'a
  • A zantawar mu da Nura Haruna Maikarfe, wani mai tsokaci kan lamurran tsaro a shiyyar Funtua, ya ce tabbas ana samun nasara a yaki da tsaro

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - Rundunar sojin kasa da na sojin saman Najeriya sun kashe wani hatsabibin dan bindiga mai suna Gwaska a jihar Katsina.

A samamen hadin gwiwa da sojojin sama da na kasa suka kai sansanin Gwaska, an ce jami'an tsaron sun hallaka sama da 'yan bindiga 100.

Kara karanta wannan

Yadda riƙaƙƙen ɗan bindiga ke bautar da jama'a, ya yi musu barazanar noma

Sojojin Najeriya sun kashe hatsabibin dan bindiga, Gwaska a Katsina
Sojojin sama da na kasa sun kashe Gwaska, hatsabibin dan bindiga a Katsina. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Sojoji sun farmaki sansanin 'yan bindiga a Katsina

Mai sharhi kan lamuran tsaro a shiyyar Arewa maso Gabas da kuma Tafkin Chadi, Zagazola Maka ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya nuna cewa sojoji sun gudanar da wannan samamen ne a ranar 10 ga Afrilu, inda dakarun runduna ta 17 da ra 213 suka kai farmakin da goyon bayan jiragen yakin sojin sama.

An kai farmakin ne a sansanin ‘yan bindigar da ke a garuruwan Mununu Bakai, Zango, Jeka Arera, Malali, da Ruwan Godiya da ke kan iyakokin kananan hukumomin Kankara da Faskari.

Kwamishinan tsaro da harkokin gida na jihar Katsina, Dr. Nasir Mua’zu, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.

Sojoji sun kashe jagoran 'yan bindiga, Gwaska

Dr. Nasir Mua’zu, ya ce an gudanar da farmakin ne bisa sahihan bayanan leken asiri, kuma ya yi sanadin hallaka jagoran 'yan bindigar, Gwaska.

Kara karanta wannan

Najeriya ta hada kai da kasar Japan domin tallafawa manoma 500,000

Sanarwar kwamishinan ta ce an dade ana farautar Gwaska da tawagarsa, kasancewarsa na biyu ga wani jagoran kungiyar 'yan ta'addar ISWAP.

Rahotanni sun bayyana cewa Gwaska ya bar garin Danmusa ya koma dazukan Mununu kafin sojojin Najeriya su kai masa wannan hari.

“Dakarun sun kwato kuma suka lalata manyan bindigogi guda biyu, da bindigogi na gida da sauran makamai domin hana sake amfani da su,” inji kwamishinan.

A cewar Mua’zu, wannan farmaki ya tarwatsa ƙungiyar ta’addanci da ke addabar yankunan Faskari, Kankara, Bakori, Malumfashi da Kafur.

Sojoji sun kakkabe 'yan ta'adda a Faskari, Sabuwa

A wani rahoton mai alaka da wannan, jami’an tsaro sun kaddamar da wani samame kan wata mashahuriyar hanyar 'yan bindiga da ke Dutsen Wori.

Dutsen Wori wani gari ne da ke kan hanyar Dandume zuwa Kandamba, a gefen garin Dandume da ke iyaka da kananan hukumomin Faskari da Sabuwa.

Wannan farmaki da aka kai misalin ƙarfe 3:45 na safiya, ya jawo mutuwar wasu 'yan bindiga shida ciki har da jagoransu, yayin da wasu da dama suka tsere da raunukan harbin bindiga.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kwato manyan bindigogi, sun gwabza fada da 'yan fashi

Dakarun sojin sun kuma samu nasarar kwato babura guda bakwai, yayin da wasu 'yan bindiga hudu suka tsere cikin daji.

Kwamishinan tsaron ya ce an bi sawun 'yan bindigar daga sansanoninsu da ke Maigora/Doroyi a Faskari, tare da ƙarin cewa babu wani jami'in tsaro da ya samu rauni a farmakin.

Gwamnan Katsina ya jinjinawa jami'an tsaro

Sojoji sun kakkabe 'yan ta'adda a Katsina
Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda a Katsina. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Gwamna Dikko Umaru Radda na jihar Katsina ya jaddada aniyar gwamnatinsa na kawar da matsalar 'yan bindiga a jihar.

Ya yaba da ƙoƙarin da jami’an tsaro suka yi, tare da nanata kudirin gwamnati na haɗin gwiwa da al’umma don dawo da zaman lafiya.

Ya kuma nuna kwarin guiwar cewa da haɗin kai da taimakon Allah, za a dawo da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.

Kwamishinan ya ƙara da cewa wannan farmaki na cikin manyan dabarun da hukumomin tsaro ke aiwatarwa domin kwato jihar da yankin Arewa maso Yamma daga ‘yan ta’adda.

Kara karanta wannan

'Ba mu karyata Zulum ba,' Gwamnati ta yi gyara kan batun dawowar Boko Haram

'Ana samun nasara kan 'yan ta'adda' - Nura

A zantawar Legit Hausa da Nura Haruna Maikarfe, wani mai tsokaci kan lamurran tsaro a shiyyar Funtua, ya ce tabbas ana samun nasara a yaki da tsaro.

"Duk wanda ya ce maka wai ba a samun nasar kan 'yan ta'adda, to wallahi yana fadin son zuciyarsa ne kawai, amma mu da muke cikin ƙauyukan nan, mun san abin da ke faruwa.
"N yarda cewa matsalar tsaro na da girma, kuma kullum ana kyankyasar sababbin yan ta'adda, amma kuma, jami'an tsaronmu kullum cikin kashe su suke.
"Yaushe rabon da ka ji an ce ƴan bindiga sun tare hanyar Funtua zuwa Sheme, ko Sheme zuwa Faskari? Wannan ya fara zama tarihi, ko ba su daina duka ba, to an karya lagonsu."

- Nura Haruna.

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar Katsina, da su kara karfin jami'an tsaro a jihar, musamman. kananan hukumomin shiyyar Funtua, inda aka fi matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

Rundunar sojoji ta yi kakkausar martani ga Zulum kan hare haren Boko Haram

Jami'an tsaro sun gwabza da 'yan ta'adda a Katsina

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ‘yan sanda da hadin gwiwar 'yan banga sun ceto mutane har bakwai da aka sace a jihar Katsina, bayan sun yi artabu da ‘yan bindiga.

Kakakin ‘yan sandan jihar, Abubakar Sadiq, ya ce an jami'ai sun kai dauki cikin gaggawa da aka ce an farmaki Dutsinma da Malumfashi.

A Dutsinma, an ceto mata biyar, sai a Malumfashi, ‘yan sanda suka kubutar Hafsat Amadu da Musa Sani bayan fafatawa da ‘yan ta'addan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.