Yan Sanda Sun Yi Ƙarin Haske bayan Kama Wasu Mafarauta 4 daga Kano da Makamai a Edo
- Rundunar ‘yan sanda ta Edo ta ce an cafke mafarauta hudu daga Kano da makamai yayin da suka isa jihar ranar Asabar da dare
- Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Moses Yamu, ya bayyana cewa an kama mafarauta ne ba Fulani makiyaya ba
- Sunayen mafarautan da aka kama sun hada da Yusuf Abdulkarim, Mujaheed Garba, Shittu Idris, da Jamilu Habibu, kuma daga Doguwa a Kano suka fito
- An gano bindigogi guda uku, harsasai, wuka da adduna tare da su, inda kwamishinan ‘yan sanda ya bukaci mutane su guji yada ƙarya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Benin-City, Edo - Rundunar ‘yan sanda ta fayyace jita-jitar cafke Fulani makiyaya da makamai a wani yanki da ke jihar Edo.
Rundunar a ranar Asabar ta bayyana cewa an cafke wasu mafarauta hudu daga jihar Kano dauke da makamai a jihar ba Fulani ba ne.

Asali: Original
Edo: Sanarwar ƴan sanda kan cafke mafarauta
CSP Moses Joel Yamu, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ya fitar da sanarwa da rundunar ta wallafa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta fayyace jita-jitar da ake yaɗawa daren Asabar 12 ga watan Afrilun 2025 cewa an kama makiyaya hudu.
Rundunar yan sanda ta bayyana cewa ba makiyaya ba ne aka kama, sai dai mafarauta kuma suna hannun yan sanda.
Rundunar ta bayyana sunayensu da Yusuf Abdulkarim, Mujaheed Garba, Shittu Idris da Jamilu Habibu.

Asali: Twitter
Abubuwan da aka samu a hannun mafarautan Kano
An gano bindigogi uku na gargajiya, gidan harsasai guda shida da babu komai, adduna hudu da wukake biyu a hannunsu lokacin kama su.
Sanarwar ta ce:
"Rundunar ‘yan sanda ta Edo ta samu jita-jitar kama makiyaya hudu dauke da bindiga a Americanus Hotel kusa da Ramat Park."
"Rundunar na sanar da jama’a cewa maarauta hudu daga Kano ne aka kama da bindigogi, harsasai da adduna, kuma aka mika su ga ‘yan sanda."

Kara karanta wannan
Atiku, El Rufai, Malami da sauran manyan ƴan adawa da suka ziyarci Buhari a Kaduna
"Bincike na farko ya nuna mafarauta ne daga Doguwa a Kano, suna hanyar zuwa kauyen Uvbe a karamar hukumar Orhionmwon a jihar Edo."
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Monday Agbonika, ya yi kira da a daina yada jita-jita marasa tushe da ka iya tayar da hankulan jama'a wanda ka iya haddasa tsoro.
Edo: Mataimakin gwamnan Kano ya yabawa Okpebholo
Mun ba ku labarin cewa mataimakin gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya tabbatar da ’yan Arewa da ke zaune a Edo suna cikin aminci da kwanciyar hankali.
Gwarzo ya bayyana haka ne bayan dawowarsa daga ziyarar tabbatar da zaman lafiya da kuma duba lamarin kisan da ya faru a garin Uromi.
Mataimakin gwamnan ya yabawa gwamnatin Edo saboda matakin da ta dauka na rusa kungiyar ƴan sa-kai, kama mutum 14 da kuma canja kwamishinan ’yan sanda.
Ya bayyana cewa an mika rahoto ga Gwamnan jihar Edo, wanda ya yi alkawarin biyan diyya ga iyalan mamatan da suka rasa ransu bayan yi musu kisan gilla.
Asali: Legit.ng