Yadda Riƙaƙƙen Ɗan Bindiga Ke Bautar da Jama’a, Ya Yi Musu Barazanar Noma
- Wani hatsabibin ɗan bindiga mai suna Kachalla Jiji Dan Auta ya mamaye kauyuka uku a Anka, jihar Zamfara, ya kakabawa mutane bauta
- Kauyukan da abin ya shafa sun hada da Yan Yatankari, Yar Sabaya da Birnin Doki, inda mutanen ke yin aikin leburanci a gonakin Dan Auta
- Rahotanni sun bayyana cewa Dan Auta ya gargadi mutanen yankin da su dawo ranar Litinin, 14 ga Afrilun shekarar 2024 domin ci gaba da noma
- Jama’a na kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su kawo dauki, domin kubutar da mutanen da aka mayar bayi a karkashin dan bindigar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Anka, Zamfara - Wani hatsabibin dan bindiga ya addabi wasu yankuna da ƙauyuka da dama a jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya.
'Dan ta'addan da ake kira Kachalla Jiji Dan Auta ya kakabawa mutanen wasu kauyuka uku aikin bauta a karamar hukumar Anka da ke jihar.

Asali: Original
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shafin Bakatsina mai sharhi kan matsalolin tsaro ya wallafa a manhajar X a jiya Juma'a 11 ga watan Afrilun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yabawa gwamnati kan kashe dan bindiga
Duk da wannan masifa da yankin ke ciki, wasu mazauna karamar hukumar Anka sun yabawa gwamnatin tarayya kan kokarin magance matsalar tsaro.
Al’ummar karamar hukumar Anka a Zamfara sun yaba wa Bola Tinubu, Bello Matawalle da Janar Christopher Musa kan hallaka dan bindiga Mati.
Shugaban al’ummar Anka, Muhammed Usman, ya gode wa Matawalle bisa taimakon sojoji wajen farmakin da ya hallaka ɗan bindigar.
An ce sojojin sun kai farmakin ne a karkashin "Operation Munzo", suka kwato makamai da lalata sansanonin 'yan bindiga a yankin.

Asali: Facebook
Zamfara: Yadda ɗan ta'adda ke bautar da al'umma
A cikin sanarwar, rahoton ya ce ɗan bindigar ya tilasta mutanen yankin leburanci musamman a gonaki tare da yi musu barazana.
Kauyukan da ake magana sun hada da Yan Yatankari, Yar Sabaya da kuma Birnin Doki duka a karamar hukumar Anka da ke jihar wacce ke fama da matsalolin tsaro.
Majiyoyi sun ce Dan Auta ya yi wa yan yankin barazana idan har ba su dawo ranar Litinin 14 ga watan Afrilun 2025 ba.
Ya umarci su dawo domin ci gaba da ayyukan da gindaya musu bayan wanda suka yi na aikin gona wanda ya jefa tsoro a zukatan mafi yawan mazauna yankunan.
Ana kokarin ankarar da hukumomi su san halin da mutanen yankin su ke ciki.
Ƴan bindiga na kaura daga Zamfara zuwa Sokoto
Kun ji cewa majiyoyi sun nuna 'yan bindiga fiye da 200 sun tsere daga dazukan Zamfara zuwa yankin Isa da Sabon Birni a jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya.
Rahotanni sun ce hare-haren sojoji a Danjibga da wasu dazukan Kudancin Zamfara ne suka tilasta wa 'yan bindigar guduwa daga maboyarsu.
An ce 'yan bindigar na amfani da dazukan Gusami, Rugu da Rukudawa suna shiga Dutsi har zuwa Fakai da yankin Isa bayan zargin shan wuta daga harin sojoji a yankin Arewa maso Yamma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng