'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Dasa Bam a Borno, an Samu Asarar Rayuka
- An samu asarar rayuka a jihar Borno bayan wani bam da ƴan ta'addan Boko Haram suka dasa ya fashe a jihar Borno
- Fashewar bam ɗin ta auku ne a kan hanyar Damboa zuwa birnin Maiduguri a ranar Asabar, 12 ga watan Afirilun 2025
- Lamarin ya jawo asarar rayukan matafiya da bam ɗin ya tashi da su yayin da wasu da dama daga cikinsu suka samu raunuka
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Ƴan ta'addan Boko Haram sun dasa bam wanda ya yi sanadiyyar rasuwar matafiya a jihar Borno.
Fashewar bam ɗin ta jawo rasuwar mutane bakwai a kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa.

Asali: Original
Tashar Channels tv ta rahoto cewa fashewar bam ɗin ta auku ne a ranar Asabar, 12 ga watan Afirilun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Boko Haram: Bam ya tashi da matafiya a Borno
Fashewar ta faru ne sakamakon wani bam da ƴan ta'addan Boko Haram suka dasa a hanyar wacce ta lalace kuma aka daina amfani da ita.
Jaridar Daily Trust ta ce wata majiya ta sanar mata da cewa fashewar ta auku ne a Gidan Kaji da misalin ƙarfe 12:00 na rana.
Hanyar Damboa zuwa Maiduguri dai tana ratsawa ta cikin dajin Sambisa inda nan ne mafakar ƴan ta'addan Boko Haram.
Majiyoyi da dama sun bayyana cewa fashewar ta faru ne yayin da motoci ƙarƙashin jagorancin sojoji ke jigilar fasinjoji daga Damboa zuwa Maiduguri a ranar Asabar.
Fashewar bam ɗin ta kuma jawo mutane da dama sun jikkata bayan da suka samu raunuka daban-daban.
Hanyar Maiduguri zuwa Damboa na haɗa babban birnin jihar da wasu ƙananan hukumomi a Kudancin Borno, kuma ta shafe fiye da shekaru 10 tana fuskantar hare-haren Boko Haram.
Boko Haram sun takurawa hanyar Maiduguri/Damboa

Kara karanta wannan
Atiku, El Rufai, Malami da sauran manyan ƴan adawa da suka ziyarci Buhari a Kaduna
An rufe hanyar inda aka hana jama’a amfani da ita na tsawon lokaci, har sai zuwa lokacin gwamnatin Gwamna Babagana Zulum aka buɗe ta.

Asali: Facebook
An buɗe hanyar ne domin ba da dama ga matafiya su riƙa zuwa Damboa, Chibok da sauran yankunan Kudu maso Gabashin Borno, tare da rakiyar dakarun sojoji da ke ba da kariya.
Rakiyar sojojin tana gudana sau biyu a kowane mako, kuma ana fara tafiya ne bayan dakarun sun binciki hanyar don tabbatar da babu wani bam da aka dasa.
Wannan tsarin ya daɗe yana gudana sama da shekaru biyu.
Mutanen da suka jikkata, waɗanda har yanzu ba a tabbatar da adadinsu ba, an garzaya da su zuwa asibiti a Maiduguri domin samun kulawar gaggawa.
Ƴan ta'addan Boko Haram sun kai hari a Borno
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan ta'addan Boko Haram ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Borno.
Ƴan ta'addan na Boko Haram sun kai harin ne wani sansanin sojoji da ke ƙauyen Izge da ke ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar.
Harin ya jawo sanadiyyar rasuwar jami'an sojoji guda biyu, yayin da aka hallaka ƴan ta'adda masu yawa yayin artabun da aka yi.
Tsagerun ƴan ta'addan sun kai harin ne a cikin tsakar dare a sansanin sojojin da ke ƙauyen Izge.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng