Tsaurin Ido: An Sace Motar Ofishin Nuhu Ribadu a Masallacin Juma'a da Ke Abuja

Tsaurin Ido: An Sace Motar Ofishin Nuhu Ribadu a Masallacin Juma'a da Ke Abuja

  • Rundunar ‘yan sanda ta fara binciken satar motar jami’in ofishin Nuhu Ribadu da aka ajiye yayin sallar Juma’a a yankin Area 10 a Abuja
  • Majiyoyi sun ce an ajiye motar ne karfe 1:05 na rana domin yin sallah, amma bayan dawowa daga masallaci sai aka gane an sace ta
  • An kai rahoton satar motar ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro ne zuwa ofishin ‘yan sanda na Garki da misalin karfe 2:00 na rana
  • Rundunar ‘yan sanda ta kaddamar da bincike da tsauraran matakan duba motoci a shigowa da fita domin kamo masu laifi da dawo da motar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Rundunar ‘yan sanda ta Najeriya reshen Abuja ta kaddamar da bincike kan sace mota a masallacin Juma'a.

Rundunar ta fara farautar barayin da suka sace motar jami’in ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu a Abuja.

Kara karanta wannan

Yadda darektan APC ya yi wani irin mutuwa a hannun ƴan bindiga a Abuja

Yadda aka sace motar ofishin Nuhu Ribadu a masallacin Juma'a
Yan sanda sun fara bincike kan sace motar ofishin Nuhu Ribadu a masallacin Juma'a da ke Abuja. Hoto: Nuhu Ribadu.
Asali: Facebook

Majiyoyi sun shaida wa Zagazola Makama cewa lamarin ya faru ranar Juma'a 11 ga Afrilun 2025 da misalin karfe 1:05 na rana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ribadu ya sha alwashi kan matsalar tsaro

Hakan na zuwa ne kwanaki biyu bayan Nuhu Ribadu ya ce tsaro ya inganta da kuma fadin kokarin Gwamnatin Tarayya kan haka.

Malam Nuhu Ribadu ya fadi haka yayin kai ziyarar ta'aziyya ga Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina bisa rasuwar mahaifiyarsa.

Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro ya ce alamu sun nuna cewa an samu raguwar matsalar tsaro a jihar Katsina.

Tsohon shugaban EFCC ya ce Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da goyon bayan ƙoƙarin da jihar Katsina take yi na dawo da tsaro da zaman lafiya.

Wasu barayi sun sace motar Nuhu Ribadu a masallacin Juma'a
Yan sanda sun bazama neman barayin da suka sace motar ofishin Nuhu Ribadu a masallacin Juma'a a Abuja. Hoto: Nuhu Ribadu.
Asali: Facebook

Yadda aka sace motar ofishin Ribadu a masallaci

Jami’in da ke ofishin Ribadu ya ajiye motar kirar 'Toyota Hilux' mai launin baki a Area 10, a gaban ofishin AMAC domin halartar sallar Juma’a.

Kara karanta wannan

Buhari ya yi wa Sheikh Pantami wasa da dariya da ya ziyarce shi a Kaduna

Da ya dawo daga masallaci sai ya tarar da cewa an sace motar, wanda hakan ya tayar da hankali sosai.

Majiyar ta kara da cewa an kai rahoton lamarin ofishin ‘yan sanda na Garki da misalin karfe 2:00 na rana.

Hakan yasa aka hanzarta aiwatar da duba kowace mota da ke shiga da fita daga birnin domin dakile barayin.

Rundunar ta ce suna ci gaba da kokari domin kama wadanda suka aikata laifin da dawo da motar da aka sace.

Za a ci gaba da zurfafa bincike har sai an kamo wadanda ke da hannu a satar motar jami’in ofishin Nuhu Ribadu.

Matasa sun yi sata ana sallar tarawihi

Kun ji cewa wasu matasa barayi sun sace babura guda uku yayin sallar Tarawihi a wani masallaci da ke Tipper Garage a Kuje a Abuja.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne ana tsaka da sallar inda masu baburan suka ankara da sace musu su jim kadan bayan kammala sallah.

Majiyoyi sun ce an kai rahoton lamarin ga ‘yan sintiri da kungiyar masu babura, amma ‘yan sanda sun ce ba su samu labarin satar ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.