Yadda Darektan APC Ya Yi Wani irin Mutuwa a Hannun Ƴan Bindiga a Abuja

Yadda Darektan APC Ya Yi Wani irin Mutuwa a Hannun Ƴan Bindiga a Abuja

  • Babban jigo a jam'iyyar APC, Rauf Adeniji ya rasu a hannun masu garkuwa da mutane, bayan sace shi a watan Janairun 2025
  • An gano rasuwarsa ne kawai bayan da ‘dan uwansa, Akinropo Adesiyan, da aka ceto ranar 7 ga Afrilu, ya bayyana gaskiyar lamarin
  • Masu garkuwar sun shigo gidan ne da dabara, suka yi amfani da karyar suna neman wanda ya tsallaka katanga domin su iya kutsa kai
  • Bayan kashe matar Adesiyan a gabansa, radadin abin ya yi wa Adeniji nauyi sosai, wanda hakan ya haifar da mutuwarsa cikin sa’o’i kadan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Rasuwar Rauf Adeniji, babban jigon jam’iyyar APC, ta girgiza jam’iyyar da kasa baki ɗaya.

Adeniji ya kasance Daraktan Gudanarwa na jam’iyyar kafin sace shi wanda ya rasa ransa bayan sa'o'i kaɗan.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume na shirin ficewa daga APC ya haɗe da El Rufai a SDP? Ya yi bayani da bakinsa

Babban daraktan APC ya mutu a hannun yan bindiga
Jam'iyyar APC ta yi jimamin rasuwar daraktanta a Abuja. Hoto: All Progressives Congress.
Asali: Twitter

Jigon APC ya mutu a hannun yan bindiga

Premium Times ta ce an sace shi ne a ranar 26 ga Janairun 2025 tare da ‘dan uwansa, Akinropo Adesiyan, da matarsa, Esther Adesiyan, a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An bayyana cewa jigon APC ya mutu jim kaɗan bayan sace shi, amma sai kwanan nan ne aka gano hakan daga ‘dan uwansa.

Majiyoyi sun ce akwai yunkurin ɓoye bayani daga jami’an tsaro da jam’iyyar APC kan yadda aka sace Adeniji da yadda ya mutu a cikin daji.

Wani jigon jam’iyyar APC, Jamiu Olawumi, ya ce masu garkuwa sun zo da karyar cewa wani ya tsallaka katanga don su iya kutsa gidan.

Sun ce wai suna kokarin kama wanda ya shigo, amma sai suka farmaki mazauna gidan bayan an buɗe ƙofa.

Ya ce:

“Babu wanda ya san halin da suke ciki har sai da safiyar washegari aka samu gawar wata mace, matar dan uwansa.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kwato manyan bindigogi, sun gwabza fada da 'yan fashi

“An kashe ta a cikin daji aka jefar da gawarta kusa da hanya, daga nan babu labarinsu har kwanan nan."
APC ta tabbatar da mutuwar daraktanta a Abuja
An fadi irin mutuwar da daraktan APC ya yi a hannun yan bindiga. Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Asali: Twitter

Kudin fansa da masu garkuwa suka nema

Olawumi ya ce radadin kashe matar Adesiyan a gabansa ne ya jawo mutuwar Rauf Adeniji, wanda ya mutu bayan awa uku, cewar rahoton Leadership.

Ya kara da cewa:

“Adesiyan ne ya bada labari, ya ce tsananin tashin hankali da firgicin kisan matar ne ya jawo masa mutuwa bayan wasu sa'o'i."

Olawumi ya ce masu garkuwa sun nemi kudin fansar N250m, amma gwamnatin tarayya ta hana biyan kudin ko kadan.

Ya ce bayan an ceto wadanda aka sace ne aka fahimci cewa Adeniji ya mutu tun makonni da dama da suka gabata.

APC ta rufe ofishinta bayan mutuwar daraktanta

Kun ji cewa mutuwar dakaraktan gudanarwa na APC, Alhaji AbdulRauf Adeniji, ta girgiza jam'iyya mai mulki a Najeriya.

APC ta ɗauki matakin rufe hedkwatarta ta ƙasa da ke Abuja domin nuna alhininta kan kisan gillar da aka yi wa daraktan.

Adeniji ya rasa ransa ne a hannun masu garkuwa da mutane waɗanda suka sace shi duk da an ba su kuɗin fansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel